THE MEMBERS OF THE ISLAMIC MOVEMENT IN KANO ON 30-31/01/2018 & 01/02/2018 HAS CONDUCTED 3 DAYS MOURNING SESSION FOR THE PASSING AWAY OF DAUGHATER OF THE HOLY PROPHET MUHAMMAD (S) IN ALIYU RIDHA HUSAINIYYA KANO.
SOME GUEST SPEAKERS WERE INVITED TO DELIVERED A LAECTURE ON THE LIFE OF SAYYIDA FATIMA ZAHRA (S) MODEL FOR ALL MEN.
SHEIKH SAYYID KHIZIR AL MUSAWI IS ONE THE GUEST SPEAKER WHO GAVE A HEARTRENDING LECTURE ON TRIAL SUFFER BY SAYYIDA FATIMA AFTER THE DEMISE OF HER FATHER.
ZAMAN JUYAYIN WAFATIN SAYIDA FATIMA A KANO NA 2.
Jiya ranar Laraba 31/01/2018 da Yamma aka yi zama na Biyu na tunawa da Ranar Wafatin Sayyida Fatima Zahra bint Muhammad (saawa), a Husainiyyar Imam Aliyu Ridha a.s Kofar Waika Kano.
Bako Mai Jawabi Sheikh Sidi Khizir Al Musawi ne ya halarci Zaman. Ya yi Jawabi akan rayuwar Sayyida Fatima a.s da abubuwan da suka sameta bayan Wafatin Mahafinta Manzon Allah.
Ya fara da kawo Matsayin al'ummar Annabi da Daraja Manzon Allah abin da ya sa Annabi Isa a.s daya daga cikin Manzannin Allah masu Girma 'Ulul Azzami' ya yi addu'a Allah ya saka shi a cikin Al'ummar Annabi Muhammada (Saawa). Sannan ya kawo Matsayin Sayyida Fatima cewa Ma'asumiya ce kuma badan Akwai Imam Ali ba da har ta koma ga Allah bata da mijin Aure. Dalili kuwa saboda Ismarta da Matsayinta a Wajen Allah, nan ya kawo Hadisin da yake cewa Babu wanda ya San Allah sai Manzon Allah sai Ali, ba wanda ya san Manzon Allah sai Allah sai Ali, haka kuma babu wanda ya san Ali sai Allah sai Manzon Allah. Ya kara da cewa wannan Sanin kuma tun farkon Halitta ne. Fatima kuma tsoka ce daga Jikin Manzon Allah.
Sannan ya shiga kawo yadda wasu suka cutar da ita ya fara da kawo kokarin da wasu Sahabbi suka yi an dawo daga wani Yaki suka shirya za su kashe Manzon Allah a wani Gwalalo a tsakanin Duwatsu, sun shirya su turawa Annabi wani Dutsi idan ya zo sai shigewa ta Matsatsin. Annabi ya aika da Imam Ali da wasu Mutane suka je suka koresu.Annabi ba baiyana sunayensu akwai Muhajuruna da Ansar guda 8 a cikinsu.
Ya kawo yadda wasu suka je har gidan Sayyida Fatima bayan Wafatin Annabi, suka yi mata duka suka karya Kofar Dakinta suka yi sanadin zubewar cikinta bayan sun karya mata Kashin Hakarkari da kyauren Kofar dakinta.
Ya kawo Yadda lokacin da tana rashin lafiya wasu manyan Sahabbai suka je Gidan Fatima za su duba, Imam Ali ya sanar da ita ta ce ba ta son zuwansu, suka matsa masa Imam Ali a.s ya dawo ya yi mata magana ta kyalesu. suka shigo, ta saka hijabinta ta juya baya bata kallesu ba. Ta tambayesu ko sun taba ji Manzon Allah ya ce Fatima tsokar Jikinsa ce? suka amsa mata sun sha Ji. Ta ce musu sun taba jin Annabi ya ce Ina fushi da Fushin Fatima, Allah na Fushi da Fushina Suka ce sun sha Ji. ta ce musu sun taba ji Annabi ya ce wanda ya cuci Fatima ni ya cuta wanda ya cuceni ya cuci Allah suka ce sun ji, suka ce sun sha ji. Sannan ta ce musu to ku shaida da duk wanda yake dakin nan ya shaida cewa ni Fatima Kun Cuceni, ina Fushi da ku, ina Kakarku a wajen Allah da Annabi. Ku tashi ku fice mini daga Gida.
A cikin Jawabinsa ya kawo batun Salatin Annabi cewa duk Salatin da babu Alayen Annabi wannan Salatin ba karbabbe bane. Ya cewa Allah ba ya karbar Salatin da aka ce 'Wassahibi Ajma'ina' Ya ce Saboda a cikin Sahhabi akwai Yan Wuta, masu Cutar da Manzon Allah, kamar yadda bukhari ya ruwaito.
Ya kawo Yadda Sayyida Fatima ta fassara Soyaiyar Manzon Allah fiye da komai, kamar yadda Ummul Muminina Aisha ta kawo cewa Wata rana Annabi ya yiwa Sayyida Fatima rada a kunnenta sai sa ta saka Kuka sai kuma ya kama daya kunnan ya sake mata Rada sai ta saka Dariya. Nana Aisha ta tambaye menene Mahaifinki ya fada miki ki ka saka Kuka sannan kuma ya sake fada miki Ki ka saka dariya, Sai Sayyida Fatima ta ce Sirrin Mahaifina ne. Amma bayan Annabi ya yi Wafati ta sake tambayarta sai Sayyida Fatima ta ce mata Maganar da ya yi Mata a Kunne da farko ya ce Ya Kusa komawa wajen Ubangijinsa shi ne ta saka Kuka, sai kuma ya sake yi min rada ya ce a Iyalaina ke ce za ki fara bina. Shi ne ta saka dariya.
Sidi Khizir ya ce wannan shi ne Soyaiya, amma an kawo wani labari mai kama da tatsuniya da wasu suke son Kambama Matsayinsu aka, wai Annabi ya tambayi wani cewa Mai ka fi So ya ce Shi kansa da Iyayensa, Dukiyarsa da Annabi, Sai Annabi ya ce ba ka cika masoyi ba, sai ya ce Sai kansa sai kuma Annabi sai Annabi ya ce da saura. Sannan ya ce yanzu na fi Sonka da ni kaina, Sannan Annabi ya ce yanzu ka zama Masoyi na hakika. Sheikh ya ce soyaiyya ba da baki ake yi ba. Ya za ka ce Ka fi son Manzon Allah da Ranka sannan a je fagen Yaki ka gudu ka bar Manzon Allah a tsakiyar Mushirikai, idan da gaske ne kana sonsa fiye da ranka ka tsaya mana ka ba da ranka ka fanshi ran Manzon Allah.
A karshe ya yi kira ga yan uwa da su yiwa Allah godiya da ya fahmtar da su wannan Tafarkin na gidan Manzon Allah, ya ce idan akwai abin da ya fi Shi'a ma a fada mana.Ba abin da Mutum zai baka. Komai ka gani daga Allah ne.
Ya ce wannan bayanan ne ba a so aji, amma batun Zagin Sahabbai karya ne masu fada ma sun san baya ayi. kawai ba a so ne aji abin da ya samu Iyalan Manzon Allah, saboda idan Mutane suka ji za su tambaya menene ya jawo haka? Daga nan kuma za bar wasu da Iyayen gidansu, wannan ne suka karewa ba wai ana Zagin Sahabbai ba.
Ya Kuma karkare da magana akan Jagaoran Harka Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ce duk abin da wadannan Azzaluman suke masa Jarabawace kuma da yarda Allah sai kwatoshi daga hannaun Azzalumai Za kuma a ga yadda al'umma za ta amsa wannan Kiran da yake yi. Ya yi addua'a duk masu Cutar da Zakzaky da mabiyansu Allah ya wulakantasu tun a Duniya ya sa su yi Mummunan Karshe.