YUNKURIN HALAKA YAN INTERNET FORUM BIYU A CIKIN MAKO BIYU.
Yada sakon Harkar Musulunci a kafar Internet yana rusa duk wata Propagandar da Gwamnati take yi na bata sunan Yan Uwa da kokarin hada su fada da al'umma. Shi ne kuma kashin bayan tona asirin duk wani Mummunan Shiri na kauda Harkar Musulunci ta amfani da ta'ddancin akan Yan uwa. Don haka masu wannan aikin suna cikin Hadaruruka daban daban.
Wani abu da ya faru wanda ya fito da haka a fili shi ne. Makon biyu da ya shige, Yan uwa masu Yada sakon Harkar Musulunci a Internet a karkashin Internet Forum na Harkar Musulunci a Najeriya, sun shirya Bitar Sanin Makamar aiki don karawa Juna Ilimi akan Harkar Sadarwa a Intenet, don sanin amfani da Illolin da yake tattare da haka. Sanin Sabbin hanyoyin yada sakon a Internet.
Ranar 7/07/201, Wato Kwana daya kafin fara Bitar. Daya daga cikin yan Uwan da aka saka Lambarsu a Sanarwa Bitar ta karshe, don tuntubar Wajen da sauran bayani ga baki masu shigowa Garin Kazaure. An yi yunkurin Saceshi.
Misalin Karfe Takwas na dare wani Ya kira shi ya ce ya zo Wajen Mu'utamar bai san wajen da ake saukar bakin da suka zo su kwana ba ranar Jumma'a kenan. Dan Uwan ya kwatanta masa. Ko da Mutumin ya zo sai ya sameshi shi kadai, sai ya ce ya rakashi wani kauye a Kusa da Garin Kazaure dan uwan bishi suka hau Mashin suna tafiya har suka shige wajen da ya ce masa za shi. Amma yana cewa su ci gaba da tafiya ba su zo ba. Allah ya taimaka dan uwan ya hango Mota Jeep na biyesu da su tunda suka baro Gari.
Lokacin da dan uwan ya lura akwai Matsala Motar nan na biye da su har suka shige wannan Kauyen sai ya tsaye ya ce shi bai zai shi gaba ba. Kawai sai wannan bakon ya shiga Zaginsa da Ashar da bakaken Maganganu. Ya ce lallai sai ya kashi ba nan su ka yi ba. Koda ya Lura Motar tana rage tafiya kawai sai yarda Mashin din ya shiga Jaji da gudu. Ya je ga wani Kauye a kusa da wajen, ya sanar Mutanen Kauyen. Lokacin da suka yi gaiya suka zo wajen, babu Mutumin babu Motar. A gida kuma ana nemansa sai bayan Karfe dayan dare Ya dawo.
Dan Uwa na Biyu shi ne Aliyu Smith Almusawi. Daya daga cikin Yan uwan da suka gabatar da takarda a wajen Bitar shi ma ya sauka a Kazaure da Dare. Amma a hanya an sace masa Kudinsa da Wasu Mahimman takardu. Hada da ATM Card guda biyu,amma ba wanne labarin ba.
Makon da ya shige an gaiyace wani taro na Marubuta a Abuja. bayan an gama taron yana kan hanyarsa da komawa gida. Ya gamu da wani Mutum ya kira sunansa Faran-faran kamar ya sanshi. ya ce yana cikin Friends dinsa da yake mu'amalla. ya dinga bashi labaru daban daban kamar ya sanshi. Ya yaudareshi zuwa wani Gidan Abinci ya ce a kawo musu abinci. Malam Aliyu ya ce ya koshi. Amma Mutumin ya nace sai ya ci. ganin haka ya dan ci kadan don kada ya bata masa Rai.
Tunda ya ci abincin nan ya kusa daga haiyacinsa. Karshe da kyar ya zo Gida. Ya kama rashin lafiyar da ya kwantar a Asibiti. Binciken Asibiti ya tabbatar masa da cewa guba ya ci a cikin Abinci, sa'ar da ya yi ma baici da yawa ba. Ya samu lafiya bayan jinyar da ya sha da addu'o'in yan uwa, ya samu kansa da Kyar.
SHAWARA GA MASU YADA SAKO A SOCIAL MEDIA.
Kada Mutum ya yarda ya gana da wani wanda bai sanshi ba shi kadai. Komai sabon da ka yi da Mutum indai ba ta zahiri ka sanshi ba.
Duk lokacin da za ku hadu ya zama a cikin Jama'a ne kada kuma ka yarda ku Kebe nesa da Mutane.
Ka da sauki Mutumin da ba kasanshi ba a gidanka ko Ofis dinka. Don za a iya saka maka kayan nadar Labaranka ba ka sani ba.
Kada ka ci wani abincin Mutumin da ba ka sanshi ba. Don kawai kuna haduwa a kafar Sadarwa ta Social Media. Ko a wajen taro ne idan ba kasan Mutanen ba ka yi taka tsan tsan. Wajen karbar abin Sha. Ko Tayin abinci. Hajiya Naja'atu Bala Muhammad ta ce ta wannan hanyar su Jonathan suka bata Guba don su kasheta a wajen wani taro.
Mu daina baiyana sirrukan mu a Socila Network, da sanar da Jama'a duk Motsinmu. Misali 'Ina kan hanyar zuwa Abuja daga Kaduna I need your Prayers.'
Mu yi hankali da suka lambobinmu a Social Netwoks.
Mu tammab Webcam din laptop dinmu mun rufesu, don gudun daukar hotunanmu ba tare da mun sani ba.
ALLAH NE ABIN DOGARANMU.
FREE ZAKZAKY DOLE.