KARE FIKIRAR JAGORA?
Ibrahim Ahmad Daurawa
Duk Mai shiga Whatsapp ko Facebook a yanzu zai sha karo da irin wannan rubutun ko da wannan sunan ko da wani mai kama da shi. Haka za ka ji wasu suna furta haka a wajeje da dama. Suna tada Jijiyar Wuya suna su fa akan kare Fikirar Jagora a shirye suke su yi fada da duk wani dan uwa, wasu ma suna kunduma Ashar da kalamai na alfasha iri iri.
Abin tambaya shi ne wai menene Fikirar Jagora ne. Idan mu san Fikirar Jagora za mu gane wadanda suke akan Fikirar Jagora da wadanda suke fada da Fikirar Jagora da kowace irin kama suka fito. Kamar yadda Imam Ali ya ce ne ka san gaskiya za ka gane wadanda suke tare da ita. Abin lura gaskiya ake sani sannan a san wadanda suke tare da gaskiya. Ba Mutane ake sani ba a ce su wane da wane sune akan gaskiya.
Wannan Ma'aunin ya kamata mu yi amfani da shi wajen tace su wane da wane akan Fikirar Jagora suke ko akasin haka. Don haka sanin Ainashin fikirar Jagora daga Jagora zai taimaka mana cikin sauki mu gane wane akan Fikirar Jagora, wanene kuma yake yunkurin sauya yan uwa daga Yakirar Jagora, amma da sunan yana kare Fikirar Jagora.
Shiekh Ibrahim Zakzaky shi ne Jagoran Harka Musulunci a Najeriya. Kuma komai nasa a fili yake, ba wani abu da yake a boye. Akwai Jawabansa daban daban a Kaset da Audio da Bidiyo kowa zai iya mallaka ya saurara. Sannan abin da ya fi Mahimmanci shi ne aiyuka da Matsayar Sheikh Zakzaky akan kowane abu, wanda yake fadi cewa Harkar Musulunci Karatu ne da aiki da shi. Aiyukansa suna Fassarar Karatunsa kuma a fili suke. Muna gani aiyukansa da yadda yake hulda da Mutane daban da daban masoya da Makiya. Talakawa da Azzalumai. Ba wani abu da ya shige mana duhu, domin yana zaune ne a cikinmu. Don haka duk mai neman gaskiya babu wani abu da zai shige masa duhu a halin yanzu.
Munufar Sheikh Zakzaky kirane ne zuwa ga tabbatar Musulunci a aikace a kawunanmu, kamar yadda Allah ya umarce mu da mu aikata shi. Allah kuma bai dora mana abin da ya fi karfinmu ba. Hanyar Tabbatar da Musulunci shi ne hanyar Gwagwarmaya da fadi tashi har Allah ya dubemu da Rahmarsa ya tabbatar mana da abin da muke hankoro. Abin da ya fi mahimmanci shi ne neman Yarda Allah a wannan Gwagwarmayar. Yarda Allah shi ne burinmu shi ne a'ala. Idan muka samu wannan mun yi Nasarar.
A takaice aikata addini irin yadda Manzon Allah ya aikata shi ne Kiran da Manufar Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky. Idan Mutum yana aikata addini yadda Manzon Allah da Imamai suka aikata a cikin Sauki za a gane. Idan kuma yana aikata wani abu daban shima cikin Sauki za a gane.
Abin tambaya ana iya sauya Munufar Sheikh Zakzaky ta gwagwarmaya akan tafarkin Allah? Amsa ana iyawa saboda an sauya Munufar wasu Annabawan.
Ta wacce hanya ake sauyawa, ta ciki ko ta waje. Amsa ana sauyawa ta cikin Da'awar ba ta waje ba. Ko ta hannun dama ku ta hannun Hagu.
Sauya Da'awa ta hannun Dama shi ne a fifita wasu abubuwa da ba su da Muhimmanci a ba su Muhammanci a watsar da masu Muhimmanci. Kamar a ce ba a bukatar Jihadi yanzu kawai abin da ake bukata shine Azkar a tsarkake Zukuta. Ko a ce ba a bukatar Bincike da Sabunta Ilimi mu rike abin da ake da shi kada mu yi shishigi akan lamarin Allah. Idan aka bi wannan hanyar an sauyawa Addini Matsayi a cikin Al'umma an kuma dakile matsayin da yake da shi wajen motsa al'umma da kawo sauyi. Kamar yadda ya faru a Tarihin Musulunci.
Ana kuma sauya Munufa da fikirar Da'awar mai kira ta hannun Hagun. shi ne a shigo cikin Addini a dinga karfafa wasu Munanan dabi'u ana Yakar duk wani wanda yake da Kyakyawar dabi'a, a hankali sai Mutanen banza su zama su ake ganin Kimarsu, mutane su dinga gudun aikata duk wani abu mai kyau, saboda ana kyamar masu aikata hakan. A hankali duk wani Aiki na Addini mai kyau sai a gujeshi, a sauya shi da Kishiyarsa. Kamar dai yadda ya faru a lokutan Sarakunan Banu Umayya.
Ana amfani da wannan dabarar a sauyawa Addini fasali gabadaya da wani abu wanda Addinin yake Yakarsa. Misali Arnar Rumawa sun kasa kawo Karshen Kiristanci na Hakika sai wani Sarki ya kawo dabara ya ce su shiga Addinin su Sauyashi. A hankali suka sauya Bautar Allah da Bautar Gumakan Rumawa komai suka sauya shi suka ce shi Kiristanci. Masu addinin na Gaskiya suka kashesu, mutane suna ganin su batattu ne. Suka rungumi masu Bautar Gumakan Rumawa da sunan sune masu Addinin Kiristanci na Hakika.Ta wannan hanyar aka kawar da koyarwa Annabi Isa.
Duk wadannan matakan guda biyu Makiya suna amfani da su yanzu wajen kawo karshen wannan da'awar ta Sheikh Zakzaky don sun san cewa ba za su iya gamawa da ita da karfi bindiga ba.
Bana son na tsawaita.Yanzu tunda mun san ana sauya Fikirar Mai Kira.Idan mu lura da kyau mu ma Azzalumai suna son koma suna Yunkurin sauya Fikirar Jagora da wasu Gurbatattun Fikirori. Yanzu menene abin yi. Shin zamu zuba Idanu ne har Yaki ya ce mu har gida.?
Su wanene ya kamata su zama ma su kare fikirar Jagora? Shi akwai wasu ne da aka ware aka baiwa alhakin kare Fikirar Jagora? Idan haka ne wane Mataki ne ake dauka a zama mai kare Fikirar Jagora. Ta wacce hanya za a gane dan uwa yana kare Fikirar Jagora???
Wadannan amsoshin masu sauki ne, duk dan uwa hakkinsa ne ya ga cewa ya kare Fikirar Jagora, don haka dole ya san menene Fikirar Jagora. Ya kuma sani daga Jagora kai tsaye.
Babu wasu Yan uwa da ka nasafta aka ba su alhakin kare Fikirar Jagora, dukkan mu za mu zama masu kishin Fikirar Jagora, hakkin ne akan kowane dan uwa ya kare Fikirar Jagora.
Hanyar da za mu gane Dan uwa yana kare Fikirar Jagora shi ne, mu ga yana dabbaka Halayya irin ta Jagora. Misali yana kira wajen hada kan al'umma ba tarwatsu ba, Tausayawa da Girmama yan uwa da sauran al'umma ba jefo alkaba'i da rashin tarbiya, da sharri a cikin yan uwa ba. Ya zama Ma'abocin Addini abin misalai da sauke duk Hakkukuwan Harka , mu ganshi yana aiki da Ilimi a komai nasa, a takaice ya zama Wakilin Sheikh Zakzky a kowane fanni na rayuwarsa.
Wani abin mamaki sai ka dan uwa yana Gunduma ashar yana zage zage da sunan kare Fikirar Jagora. Idan aiyukan dan uwa suka yi hannun riga da kiran Sheikh Zakzaky ko ya kwana yana cewa shi yana kare Fikirar Jagora ne mun san yana yaudarar kansa ne, karya yake yana wakiltar Shaidani ne amma ba Sheikh Zakzaky ba.
Fikirar Jagora a fili take, kuma aikata addinin Zalla shi ne Fikirar Jagora ba sabanin haka ba. Babu Zagi, shagube, Habaici da cin Mutunci a fikirar Jagora. Kira ne da hikima da kyawawan aiyuka abin da yake rinjayar Zukatan abokan adawa, ba harzuka Mutane ba.
Ibrahim Daurawa.