*MUZAHARAR FREE ZAKZAKY A ABUJA: Jami'an Tsaro Sun Kashe Yan Gari*
Daga Yahaya Muhammad Soje
A ci gaba da gudanar da Muzaharar neman a saki Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky da Mai Dakinsa Malama Zeenah Ibraheen yauma Jami'an tsaron yan Sanda sun afka ma muzaharar inda suka bude wuta kan masu Muzaharar bayan kammalawa, lamarin wanda nan take yayi sanadiyyar Mutuwar mutane biyu masu tafiya gidajensu bayan kammala ayyukansu tare da jikkata wani Dan Kabilar Igbo.
Muzaharar wanda aka gudanar a babban kasuwar Otake aka nufi Bagger, bayan kammala Muzaharar ne Jami'an tsaron suka hallara a muhallin suka yi ta luguden wuta, masu muzaharar sun watse inda Jami'an tsaron suka kwashe wadanda suka Harba.
Jami'an tsaron sun ci gaba da bin yan uwa da jama'ar gari suna kamawa, wanda har yanzu bamu da adadin wadanda aka Kama, amma dai sun Kama wasu yan Uwan.
Calling together all brothers and sisters who are interacting with social Networks to a single platform in order to conform with the accepted ideology of the movement in spreading the message of the movement through the internet.