MARTANI : GANGAMIN GANIN BAYAN SHI'A A IKKO (LEGAS)

Bayan ta'addancin da Sojojin Nijeriya ’yan ina-da-kisa suka yi ma raunana 'Yan Nijeriya #Zariya _kisan Kiyashi, inda suka kashe mutum sama da 1000+ a Birnin Zariya, Gwamnatin Nijeriya ke daukar dawainiyar tallace-tallace na farfaganda ta kafofin sadarwa da nufin cusa kyama, da haddasa karan tsana ga Harkar Musulunci a Nijeriya a zukatan Jama'a. Wannan yunkuri dai ana yin sa ne don a iya samun damar halasta wannan danyen aiki da Sojojin Nijeriya suka aiwatar bisa umurnin Shugaban kasar Nijeriya, Buhari. Kash! Allah Mai kowa Mai iko, ashe sun makara, 'Yan Nijeriya sun fadaka, sun kai 'GANO ' wadanda ke bukatar a samar da ingantacciyar Hukumar Bincike mai zaman kanta, wadda za ta binciki wannan kisan Kiyashi. Wanda har ya zuwa yau Gwamnatin Nijeriya ta ki ta samar da shi.
Yayin ziyarar aiki da Shugaban Nijeriya Buhari ya kai Kwanan nan a kasashen Saudi-Arabiyya da Qatar; kasashen da suka dauki akidar #wahabiyanci a matsayin addinin da hukuma ta yarda da shi, ya furta a sarari cewa Kasar Nijeriya ba za ta shiga cikin kungiyar hadaka na rashin kan gado wadda ke tattare da rashin gaskiya da yaudara wai da sunan yaki da ta'addanci. Kaico, sai ga Gogan naka bayan ya dawo gida Nijeriya, 'Yar kwikwiyon barandan kasar Qatar - kafar sadarwar Al Jazeera - ta zo takanas ta Kano, ta yi hira da shi don ya bayyana shigar Nijeriya wannan hadaka mara ma'ana da Saudiya ke ma jagoranci.
Ba dadewa sai ga wasu zauna-gari-banza, duk inda ta fadi sha, mijin-iya-baba, sun fara bayyana da #alamomin addinin Kirista da sunayen su irin na Kirista. Aikin da aka ba su na farko, gabatar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar Iran a Abuja, wanda wani "limamin kirista "ya Jagoran ta. An samu tabbacin cewa mafi yawan kiristocin da suka hallara a wurin Sojojin haya ne daga jihar Ribas a yankin Kudu Maso Kudu na Nijeriya.
Yau (08/03/2016) sai ga wani gungun ’yan a-bi-yerima-a-sha-kida, "Nijeriyawa sun hade a kan yaki da ta'addanci "(Nigerians United Against Terrorism) wacce ba a san da zamanta ba, karkashin jagorancin wani wai mai suna Jude Feranmi ta kaddamar da kamfen a birnin Ikko(Legas) da taken " #kickAgainstShiiteExtremimTerrorism" ( #WatsiDaTsatstsauranRa'ayinshi'aDaTaaddanci", bisa yunkurin hana riko da tsattsauran ra'ayin rikau a kasar. Da yake Dandalin kaddamar da wannan kamfen din cibiyar da ta kware ne a wajen yada sharri da bata suna, bai zo da mamaki ba, da ma African independent Television (AIT) ta kware akan haka, kuma ya tabbatar da hasashen cewa an dauki nauyin sa ne.
Tambaya a nan ita ce, ina Jude Faranmi da ‘yan dabarsa suke yayin da #BokoHaram ke kuli-kulin kubura da Nijeriya tsawon shekaru sama 5 ya zuwa yau? A 'yan tsakanin nan ta'addancin Boko Haram ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum sama da 30,000+ ‘yan Nijeriya da ba su ji ba, kuma ba su gani ba, garuruwa da kauyuka bila adadin, an kona su kurmus, sama da matan Nijeriya 1000 aka sace su. Musamman kowa na sane da Shahararren lamarin nan na batan #YanMatanChibok, wanda har yanzu an kasa ceto su. Kar a manta cewa ta'addancin Boko Haram ya yi sanadiyyar kashe dubbai na Jami'an Tsaron Nijeriya, tare da kona barikokin Soja da ofisoshin 'Yan Sanda, har da barnata sansanonin Soja. Ina Jude Feranmi yake yayin da wadannan kashe-kashe, kone-kone da sace-sace ke gudana da gayyar sa "Nigerians United Against Terrorism "? Wannan ba ta'addanci ne da ya kamata yan Nijeriya su hade a yake ta ba?
"Muna yunkuri ne don hana 'Yan Shi'a kar su tabbata a kan tafarkin tsattsauran ra’ayi, a shirye muke, mu tabbatar ba a bar 'yan Shi'a sun dauki tafarkin harkar Soji ba, kamar yadda wasu daga cikin Jagororinsu suka dauka yanzu ba." Wannan zancen Jude Feranmi ke nan da sauran jama'ar sa da aka dauki hayar su.
Tsawon shekaru 37 Harkar Musulunci a Nijeriya ta kwashe tana gudanar da ayyukanta, ba a sajjala kashe ko raunata wani ba, (bil hasali ma 'ya'yan ta ake kashewa, ake raunatawa). Don haka tuhumar ta'addanci ko tsattsauran ra'ayin a kan ta bai da asali balle madafa, wanda yunkuri ne na wadanda suka kashe mutum sama da 1000+ a Zariya, kuma suka tona wagegen rami suka binne su don su batar da shedar aukuwar laifuffukan yaki da suka yi. Wannan zabi na gudanar da ayyukan Harkar Musulunci ba tare da Hatsaniya ba, zabi ne na kashin kai, kamar yadda Musulunci ya karantar, wanda Jagora Mai hangen nesa, Malam Ibrahim Zakzaky ya doru a kai, babu wani karfi da ya tilasta masa. Wannan zabi ne don tsananin kauna da soyayyarsa ga kasarsa da jama'ar da ke cikin ta, kamar yadda Musulunci ya tanadar. Ana iya ganin haka yayin da Sojoji suka kashe masa Almajiransa 33 da Mr Pious Unyawu a matsayin cikon na 34 , wanda akwai 'Ya'yansa 3, amma ya yi kiran da a kwantar da hankali tare da hana yin ko da zanga-zangar lumana ne ranar 25/07/2014, bayan an kammala muzaharar nuna goyon baya ga jama'ar kasar Falasdinu, bisa mamayar da Yahudawan Sahayoniya suka yi ma kasar Falasdinu kuma suke kashe su.
Ya nuna a sarari cewa wadanda suka aiwatar da ta'addancin Zariya ne suka ba ma Jude Feranmi da tawagarsa kwangilar bata sunan Harkar Musulunci a Nijeriya. Saurari zancen su:-"Ko da yake babu wani abin da za mu nuna muku a yau, yayin wannan kaddamarwa kamar yadda ake yi, yayin kaddamar da sabon gini, ko sanfurin kaya ko wani abu da ido ke iya gani.” Wadannan zauna-gari-banza wadanda ko kujerar zama ba su da ita, balle teburin rubutu, bare uwa-uba ofis, a ce za su hada kan 'Yan Nijeriya a kan yaki da Ta'addanci! Tirkashi! Abin da kamar wuya dan sanda ya ga gawar Soja! Tafdi jam!
Jude Feranmi da 'yan koren sa ba su gushe ba suna cewa " #KawarDaTsatstsauranRaayinShi'aDaTaaddanci, wata tafiya ce wadda ta doru a kan fafutukar tabbatar da cewa tsattsauran ra'ayin rikau bai sami gindin zama ba ta yadda zai haifar da gawurtacciyyar ta’addanci ba. ‘Yan rajin gwagwarmaya a fagen sadar da zumunta, Jagororinsu da duk masu fatan alheri, 'Yan Nijeriya duk sun dukufa don kariya da hadewar wannan kasa, bisa wannan fafutukar. "
Tare da girmamawa, na kwashe shekaru sama da 15 a fagen sada zumunta kuma mai fafutuka, ban taba jin wani mai suna "Jude Feranmi" ba. Daukacin jiga-jigan masu fafutuka a fagen sada zumunta, duk sun yi tofin Allah tsine a kan kisan kiyashin da sojoji Nijeriya suka yi a Zariya, sai dai ‘yan kadan wadanda suka sayar da 'Yancinsu ga Matar Shugaban Nijeriya, A’isha Buhari, wanda kwanan nan ta shirya liyafa ga kafafen sada zumunta da masu fafutuka.
Akwai tambayoyi da daman gaske wadanda ya kamata a tambaya, wanda amsoshin su zai dada bayyanar da hakikanin jama'an da ke buya a bayan irin wadannan Sojojin haya. Menene dalilin da ya sa masu daukar nauyin wadannan zauna-gari-banza ke amfani da kiristoci da alami na kirista yayin duk wani gangami? Wannan yana da matukar muhimmanci mu fahimci cewa, mafi yawan kiristocin Nijeriya sun yi Allah wadai da kisan Kiyashin Zariya, kuma sun jajanta ma Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Malam Ibrahim Zakzaky a kafafen sada zumunta daban-daban. Amfani da mutane masu sunayen Kirista da alamomin kirista, wani yunkuri ne na raunanawa tare da yunkurin kawo sabani tsakanin Harkar Musulunci a Nijeriya da Kiristocin Nijeriya. Wannan ba wani abu bane illa kokarin da miyagun da suka aiwatar da kisan Kiyashin Zariya ke son su nuna rashin amincewar da Jama'a ke da shi ga Harkar Musulunci, ba wai ya takaita ga masu tsattsauran ra'ayin wahabiyanci na Arewancin Nijeriya ba ne kawai. Kar a manta cewa akwai yan koren Isra'ila a cikin kiristocin Nijeriya.
Daga karshe, abin lura ne, a tsaya a yi tsokaci ,musamman Jude Feranmi da jama'arsa in da gaske suke yi a kan hada kan al'umman Nijeriya don yakar ta'addanci, to su tattara hankulansu, karfi da karfe a kan ayyukan ta'addancin Boko Haram da 'Yan gudun hijira wadanda ke matukar bukatar taimako. Baya ga Boko Haram, akwai babban barazanar da ke fuskantar Nijeriya a halin yanzu #ISIS & #AlQaeda. Harkar Musulunci a Nijeriya tun asali ba ta doru a kan Hatsaniya ba ne, kuma za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin kwanciyar hankali da lumana, (Insha Allah) a duk tarurrukanta da ayyukanta. Masu mummunar manufa, wadanda burin su ne shekar da jinainan mutane bisa tsattsauran ra'ayin wahabiyanci da barnata dukiyoyi su ke yada Ta'addanci. A lokuta da dama hare haren da Ta'addanci ya sha rutsawa da 'Yan Harkar Musulunci a Nijeriya,wanda ya yi Sanadiyyar salwantar rayukan yan uwa da dukiyoyi da dama . Aikinmu ceton rayuka da kare dukiyoyi ne.