Kisan Sojoji a Zariya: Kashin Mutane Uku Da Suka Yi Murna, Da Abin da Ya Kamata Su lura!
Daga Ammar M. Rajab
GABATARWA
Tun bayan kisan dubban al’umma da Sojojin Nijeriya ‘yan ina-da-kisa a karkashin jagorancin shugabanta, Tukur Yusuf Burutai suka yiwa ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a watan Disambar 2015 tare da kame jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky bayan sun harbe shi da kashe masa ‘ya’ya Uku, da kashe Yarsa da kuma harbin matarsa tare da kame ta, an samu ra’ayoyi mabambanta dangane da abin da Sojojin Nijeriyar suka yi. Ganin haka yasa nake son mai karatu ya fahimci wasu nau’in mutane Uku (3) da suka yi murna da farin ciki na kisan da Sojojin suka yi ba don komai ba sai don wasu dalilai na su da ba shi a ilimin ‘yan Adamtaka ba shi a ilimin hadisi (koyarwar Manzon Allah) ko ilimin Alkur’ani. Zan takaita rubutun don gudun tsawaitawa.
NA FARKO: nau’in farko da suka yi farin ciki dangane da kisan da aka yiwa ‘yan uwa sune; mutanen da suka kwashe shekara da shekaru suna wa’azi a mimbarorinsu na wa’azi, Masallatansu, rubutu a jaridu daban-daban, buga littattafai cikin harsuna daban-daban, amfani da ‘yan Sara suka da ‘yan iskan gari wajen kaiwa ‘yan uwa hari tare da kashe ‘yan kwarori, domin ganin an kawo karshen abin da suka kira ‘YADUWAR SHI’A A NIJERIYA’. Wannan kashin dama sun dade suna kira da gwamnati da ta taimaka musu ta kawo karshen abin da suka kira ‘Shi’a’ a Nijeriya ta hanyar kashe su, rusa muhallansu da dukkan sauran hali na rashin nuna tausayi. Wanda a zahirance suna nufin Harkar Musulunci da mabiyanta. Don suna ganin abin ya fi karfinsu. Suna yin hakan ne domin ganin yadda kullum suka rike makami guda daya kwallin kwal tamkar rai, wanda suke yiwa take da; ‘SHI’A NA ZAGIN SAHABBAN ANNABI DA MATANSA DA KUMA AUREN MUT’A’ da sauran irin wadannan karairayin, amma sai suka lura yana tasiri ne kawai ga ire-irensu, wadanda ba su damu da su binciki ilimi ba, da masu addini don son ran su. Amma idan suka hadu da masu son ina addinin gaskiya yake, sai ka ga al’amarin ta sauya zani. Ganin haka minbarorinsu, Masallatansu, da duk inda suka samu dama ba abin da suke yi a kullum sai dira ga ‘yan Shi’a da mabiyanta, kai ka ce dama duka Hadisan Manzon Allah da ayoyin Alkur’ani baki daya dama an sauke su akan Shi’a da mabiyanta. Kai ka ce kuma (sunnar Manzon Allah) da suke cewa suna son su tsaida dama sunna ce ta kiran a kashe wanda bai yadda da ra’ayinsa ba. Wuraren wa’azinsu ya zama dama don Shi’a ake wa’azin (shi’a sun ba su aiki). Su kuma Shi’ar ba su damu da su ba, balle idan sun zo wa’azi suka rika yi musu raddi. Su kam duk idan ka je wa’azinsu to abu daya ne dama za a fada, shi ne ‘SHI’A NA ZAGIN SAHABBAN ANNABI DA MATANSA DA KUMA AUREN MUT’A’. Kullum wa’azi guda daya har aka fara gajiya da ji. Ba za ka taba jin sun fada maka inda ka gaza ka gyara ba, domin aikinka a nan shi ne sakamakon ka a lahira.
To, a zahirin gaskiya irin wadannan nau’i na mutane sun yi farin cikin gaske, sun zuba ruwa a kasa, sun yi walima, sun yi addu’a da suka ga an kashe mu, don a tunaninsu yanzu wani yaki ne ake musu domin ganin bayan Shi’a da ‘yan Shi’a. Wannan hali na su yasa ma suka manta da fadin Sayyidina Ali bn Abi Talib (shima dai Sahabi ne) da yake cewa; “mutum imma dan uwanka ne a addini ne, ko abokinka a halitta.” Kiyayya da hassada ta kai su ga rashin nuna tausayi ga abin da suma zai iya faruwa da su daga wadanda suka kashe mu, duba da gwamnatin da ta kashe mu, gwamnati ce da ta ce; “ba ruwanta da addini kowa na iya addinin da ya ga dama.”
KASHI NA BIYU: kashi na biyu na wadanda suka yi farin ciki da murna sune Sojojin da suka yi wannan aika-aika, da wadanda ba su cikin aikin, amma sun yi murna da hakan, ba don komai ba saboda yadda aka dora su a irin wani tunani na cewa; Musulunci abin tsoro ne, wanzuwar Musulunci tamkar rushewar su ne na aiki bisa mutunta mutum. Aka kuma cire musu tausayi da imani tun a wajen da ake yi musu ‘traininig’ na watanni shida (wadanda suka shiga ta ‘recruitment’) ta hanyar shagaltar da su da abubuwa na sabawa Allah, shiyasa zaka ga mafi yawan Sojojin Nijeriya (ba duka ba) suna iya aikata duk abin da aka umurne su ba tare da sun yi tunani ko tambayar dalili ba, tare da mantawa cewa; “a wurin Allah babu wanda ya fi wani sai wanda ya fi jin tsoronsa.” Kuma Allah ba ruwansa da dokar kasarka don ba dokarsa bane, kuma idan ka kashe masa halitta saboda dokar kasar ka, ba ka da hujjar da zaka iya kare kanka a gabansa a ranar; ‘yauma tublar sara’ir.’ Don kisa a dokar Allah ma tana da ka’ida ko da an tabbatar wanda za a kashe ya kashe wani ne. Balle haka nan ka je ka kashe ma Allah halittarsa bisa hujjar ‘AN TARE MA SHUGABAN SOJOJI HANYA NE.’ Ku shirya abin da zaku fadawa Alkalin da ba ya bukatar kwamiti, ‘video clip’ domin yanke hukuncinsa. Saboda shi Allah ya shirya dokokinsa da ka’idojinsa wajen kashe duk wata halitta da ta aikata kisa, ko take da hannu wajen aikata kisa.
KASHI NA UKU: kashi na Uku sune; wadanda dama ba su san me Harkar Musulunci da jagoranta Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) take gudanawar ba, ba su taba jin bayaninta daga mabiyanta ba sai daga makiyanta. A don haka suna yin hukunci ne bisa abin da makiyan Harkar Musulunci suka fada musu. To, wannan kashin suma da farko sun yi murna sosai bisa rashin sani, saboda an dora su ne bisa hululu, kuma wannan kashin ne idan ka same su ka yi musu bayani na abin da ya faru, zaka ga sun sauko daga ra’ayinsu, sun zub da hawaye sun kuma tausaya mana na abin da ya faru. Kuma a nan ne suke gane makidan da gadar zaren da ake shiryawa Musulmi da Musulunci, amma saboda ta’assubanci na wasu mutane kalilan al’umma da yawa ta kasa ganewa.
KAMMALAWA
Zan kammala wannan rubutun nawa da cewa; ga wadanda suka yi farin ciki na abin da ya faru damu, to su kara himma, su yi shewa yadda suke so, su yi walima, su yi duk wani nau’i na farin ciki, amma su sani bayan farin cikin da za su yi, bakin ciki da kuka ne zai biyo bayan farin cikin na su. Saboda abin da suke son ganin an kawo karshen shi, to ba fa zai yiwu ba, kuma za su ga irin bunkasar da zai yi da tambaza har inda ba su zato. Kuma ‘ya’yanku namu ne, mu kuke haifawa. Jinin da aka zubar tamkar taki ne da ake zubawa shuka don ta girma. Dama mu mun sani, in dai addini ne irin na Manzon Allah (saww), to wannan addini ba ya yaduwa da kuma sake fahimtarsa ga wadanda suka jahilce shi, to sai wasu sun sadaukar da rayuwarsu. Ku binciki tarihin al’ummar Yarbawa ku sha labari, mafi yawan al’ummar Yarbawa da kuke ganin su Musulmi, suma sakamakon shekar da jinanan bayin Allah ne wadanda suka kai musu Musulunci, wani Sarkinsu yasa aka yanka su, a karshe sakamakon zubar wannan jinin wadannan bayin Allah, yanzu ta kaima ba zaka iya lissafa Yarbawa Musulmai nawa ne a cikin su ba. Sai dai ka lissafa wadanda ba Musulmai ba a cikin su.
Kuma ku sani dabi’a ta rashin nuna tausayi a matsayinka na Mutum, dabi’a ce da bamu san ina mutum yake samo shi ba. Na san dai ba Manzon Allah ya koyar ba, don ba inda aka taba ruwaitowa Manzon Allah ya ce; “masha Allah, Alhamdulillah da aka kashe wadanda bana so.” Ba kun ce ku sunnar Manzon Allah kuke bi? To, ina kuka samo dabi’ar rashin nuna tausayi? Ba dabi’a ce ta mutum ba, ba kuma dabi’a ce ta Musulmin kirki ba, kai ko Musulmin banza ma ba dabi’arsa ba ce ta nuna rashin tausayi. Amma kowa yana aiki ne domin girbar sakamakon aikinsa a gobe kiyama.
Irin wannan hali na su ya kara tabbatar min da cewa; lallai gwara dabba a halitta da dabba a dabi’a. Kuma irin wadannan zan iya cewa suna cikin wanda Allah ta’ala ya siffanta a Alkur’ani da yake cewa; “‘summa kasat kulubukum, fa hiya kal hijarati au ashaddu kaswa.’ Wadannan masu busassun zukatan su kadai za su rika wannan aikin. Saboda wanda ya so aikin mutane, tamkar ya yi tarayya da su ne a aikin.
Wannan yake tuna min maganganun bayin Allah da suke cewa; “babu wanda zai so iyalan gidan Annabi da masoyan iyalan gidan Annabi fa ce Mumini, babu kuma wanda zai ki su ya kuma yake su, ya yi fada da su fa ce; azzalumi, Fasiki ko kuma Munafuki.”