SHAIKH ZAKZAKY YA GABATAR DA JAWABIN RUFE TARON TUNAWA DA WAKI'AR ZARIYA A ABUJA
Daga Saifullahi M. Kabir

Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne ya gabatar da jawabin rufe taron tunawa da Waki'ar Zariya na karo na shida da aka gabatar yau Asabar 12/12/2021 a Abuja.
Jagoran, wanda ya gabatar da jawabinsa da harshen Turanci kai tsaye ta hanyar nunawa a bidiyo, wanda aka nuna ta Majigi a wajen taron, ya bayyana fatansa na ya kasance a muhallin. "Na so ace ina tare da ku a wajen taron nan don na saurari jawaban mutane kafin na yi nawa, amma dai duk daya ne InshaAllah."
Sannan sai ya taya yan uwa murna kan haduwarsu a wannan rana, inda yake cewa: "Na taya ku murna dangane da haduwarku a yau a wannan muhalli kan muhimmin al'amari wanda ya shafi rayuwar dan adam, wato 'Yancin Bil Adama."
Shaikh Zakzaky bayyana cewa dukkan mutane an kawo su doron kasa ne don su rayu tare da junansu, kuma a rayuwa taren nan akwai bukatar dokoki da hakkoki da za su lura da tafiyar rayuwa da zamantakewarsu, kuma daga mafi muhimmancin hakkoki akwai hakkin duk dan adam din da ya samu kansa a doron kasa a bar shi ya rayu, wani ba zai kashe shi ba face sai in ta hanyar shari'a ne.
Shaikh yace, wannan hakki na rayuwa da sauran hakkoki suna nan rubuce a dokokin kasar Nijeriya, wanda kuma mahukuntan kasar nan sai da suka rantse da Allah a kan za su kare shi.
Yace, amma abin takaici, an wayi gari yanzu a Nijeriya 'yancin barin mutum ya rayu ya zama labari, domin kuwa mahukuntan kasar sun dauka cewa suna da ikon su dauki rayuwar duk wanda suka ga dama a duk lokacin da suka ga dama. Yace a yanzu Kisa ba bisa hakki ba ya zama ruwan dare a kasar nan, a yayin da mutanen da aka dauke su aiki don su kare doka sun zama su da kansu ne suke saba dokar kasar.
Yace abin takaici a yanzu, hukuma kan aika jami'an tsaronta su aiwatar da ta'addanci a kan mutane. Sojoji, yan sanda da yan sandan farin kaya, yanzu ma su kan saka kayan 'yan ta'adda su rufe fuskokinsu kamar yadda yan ta'adda ke yi, su je su aiwatar da aikin ta'adda a kan al'umma.
Yace sakamakon yadda mahukunta suka zama 'yan ta da tarzoma, sun tilastawa al'umma ta zama kamar su.
Shaikh yace da yake muna magana ne akan 'Yanci, ya kamata mu fahimci cewa wannan al'ummar ba za ta taba zama mai bin doka ba matukar mahukunta kasar basu mutunta hakkokin mutane wanda doka ya tanadar musu ba. "Wadanda suke kan mulkin kasar nan suna ganin kamar su ne doka, kamar sun fi karfin doka, suna iya daukar ran duk wanda suka so a kowane lokaci suka so. Ba su damu da kowane irin takura ko shawara da ake basu ba." inji Shaikh Zakzaky.
Ya jaddada cewa mafi muhimmancin hakki, wanda dole kowa ya kiyaye shi, shine 'yancin rayuwa. "Ba ka da yancin ka katse rayuwar wasu, ba ka da damar ka dauki rayuwarsu, ba wani mai damar ya aiwatar da kisan kai, kai hatta zubar da ciki baka da damarsa, saboda idan da ace mamarka ta zubar da cikinka ne da ba za ka rayu ba. Babu wani mai damar ya dauki rayuwar kowa!"
Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa, baya ga hakkin rayuwa, akwai kuma hakkin zamantakewa, duk halittu hatta dabbobi suna da hakki. Haka ma matattu suna da hakki da suka hada da ai musu janaza idan suka rasu, bisa yadda addini da al'adarsu ya tanadar. Amma abin takaici yanzu kuna iya ganin mahukuntan kasar nan suna ganin cewa suna iya su kashe mutane kuma su ƙone gawarwakinsu, ko su dauke su su je su bizne su a wani waje da ba a sani ba.
Da yake magana dangane da Waki'ar Zariya, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa wani yanayi ne da aka shiga, inda sojojin Nijeriya suka kewaye Zariya da dukkan hanyoyin shigarta, suka kashe mutane fiye da dubu, suka dauke gawarwakinsu, suka tafi da su suka bizne a manyan ramuka a boye.
Yace abin da ya fi haushi shine yadda suka kama mutane fiye da 500 suka chaje su da laifin kashe soja guda daya. Ko da yake sun gabatar da su a kotuna, kuma dukkansu kotunan sun wanke su daga zargin da ake musu sun sake su, amma dai ka dubi irin yadda mahukunta suka so su boye baki dayan ta'addancin da suka aiwatar.
Shaikh Zakzaky yace, kisan Kiyashin Zariya shine farkon kashe-kashen da Hukumar nan ta fara aiwatarwa, amma ku dubi yadda kashe kashe ya zama ruwan dare a yanzu. Yanzu ga mutane nan a cikin matsanancin tsoro da fargaba.
Shaikh ya cigaba da cewa: Ba za ku iya kashe mutane kuma ku yi tsammanin ku za ku zauna lafiya ba, kun riga kun kashe zaman lafiya.
Yace, ya kamata mu yi tunanin makomar al'umma. Wasu sun tambaye ni a kan ko akwai wani fata dangane da makomar al'umma? Nace Eh, akwai. Ba muna zaune ne a cikin al'umma da basu da fata (mafita) ba, lallai akwai fata na gari, sai dai mafitan zai taso ne daga mutane, ba daga mahukunta ba. Bamu da wani fata daga mahukuntan nan, domin su basu damu da halin da al'ummarsu ke ciki ba. Amma su mutane, ya kamata su farka, su tashi su nemi kyakkyawar makoma a al'ummarmu. Muna fatan samun kyakkyawar canji ba da jimawa ba. Wannan ne fatanmu.
A karshe, Jagora (H) ya yi godiya ga mahalarta, tare da addu'ar samun taimakon Allah Ta'ala.
MUZAHARAR KUDUS KASHIN FARKO A BIRNIN KANO.
Jiya Jumma'a 07/05/21, wacce ita ce Jumma'ar Kashe ta watan Ramadan na bana. Yan uwa Maza da Mata almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky a fadin Kasar nan sun gudanar da Muzaharar kin amincewa da mamayar Falasdinu da Masallacin Kudus da Yahudawa suka yi tun a shekarar 1967. A wannan Muzaharar da Gangami ana gudanar da su ne a fadin Duniya don nuna alhini da tausayawa da kuma Goyan Bayan Al'ummar Falasdinawa wadanda yan Ahlul Sunna ne Larabawa. Yahudawa suka mamaye masu Kasa suke kashe su da rushe musu gidaje.
Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky na Da'irar Kano sun gudanar da Wannan Muzaharar har Kashi biyu, daya da Safe, daya kuma bayan Sallar Jumma'a duk a Birnin Kano.
Muzaharar Safe an faro tane daga daura da Gidan Aminu Kano wato Mumbayya dake Gwammaja, misalin karfe tara na Safe. Dandazon Yan Uwa Maza da Mata, Yara da Manya ne suka shiga Sahu, suna tafe suna Waken nuna goyan baya ga al'ummar Falasdinu da tsinewa Yahudawa Masu Jajayen Kunnuwa da kuma masu bakaken Kunnuwa irinsu Buhari da El Rufa'i da magoya bayansu.
Muzaharar ta biyo ta Titin Gwammaja, ta shige ta Tagwayen gida, Yan Kosai har zuwa Kofar Mazugal. Daga nan aka shige ta daura da Mayanka aka shige ta kofar Masallacin Yan Izala na Triumph zuwa Fagge har zuwa Shatale-talen Triumph wajen da aka kammala a daura da Wapa.
Masu Muzaharar suna rirrike da Tutoci da Banoni da kuma Hotunan Shiekh Ibrahim Zakzaky. Suna tafe suna fadin Masallacin Kudus na Musulmi ne Kwato shi ya zama Wajibi. Wasu na fadin 'Death to Isreal, Death to America. A lokacin da wasu ke kiran Free Zakzaky, Yanto Kudus dole ne'
Muzaharar ta dauki hankalin Jama'a da yawa, sun kuma yi Allah wadai da ci gaba da Kashe Falasdinawa da Yahudawa suke a cikin Wannan Watan na Ramadan ba tare da Majalisar dinkin Duniya ta taka musu birki ba.
Malam Bashir Sabon Titi ne ya yi jawabin rufe Muzaharar. A cikin Jawabinsa ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su farka daga baccin da suke yi su hada kai don kwato yancinsu daga Azzalumai Mahukunta Yaran Yahudawan Duniya. Sannan ya jawo hankalin Mutane akan kashe Kashen da ake a Kasar nan da cewa duk suna faruwa ne saboda Mutane sun bar koyarwa Manzon Allah da watsi da tsarin da ya zo da shi. Sannan ya kara da su amsa kiran da Sheikh Ibrahim Zakzaky yake na dawo koyar Manzon Allah da tabbatar da tafarkinsa abin da shi ne zai yantar da Mutane daga danniyar Farare da bakaken Yahudawa irin su Buhari, a samu zaman lafiya mai dorewa da yalwar Arziki.
A karshe ya yi kira ga Gwamnatin Buhari da ta gaggauta sako mana Jagora. ya kara da cewa ba za su taba ganin daidai a Gwamnatinsu ba matsawar suna ci gaba da yiwa Shiekh Zakzaky haramtacciyar tsarewa. Sannan ya jawo hankalin yan uwa da su ci gaba da fafatukar ganin Jagora ya samu yancinsa. Ya ce ba gudu ba ja da baya za mu ci gaba da bin dukkan Matakan da suka dace har sai Azzalumai sun sako mana Jagora ba za mu daina ba ko za su karar da mu ne.