News

AN BANKADO MAKIRCIN HADDASA FITINA A KAN TATTAKIN ARBA’EEN NA BANA

TAKARDAR MANEMA LABARAI
AN BANKADO MAKIRCIN HADDASA FITINA A KAN TATTAKIN ARBA’EEN NA BANA
Mun samu masaniyar cewa jami’an tsaro sun shirya makirce-makirce don haddasa hatsaniya a yayin Tattakin Yaumul Arba’een wanda muka saba gudanarwa duk shekara, domin dandana irin wahalar tafiyar da Yazidu dan Mu’awuya ya sanya Zuri’ar Manzon Rahma Muhammad {S.A.W.A} suka yi daga Karbala zuwa Damaskas a shekara ta 680 AD.
Wannan Tattaki ibada ce, wadda masu imani suke gudanarwa domin amsa kiran da Imam Husain {A.S} ya yi a filin Karbala na cewa wa zai taimake shi, wanda kuma akwai ruwayoyi da dama wadanda aka ruwaito daga Manzon Allah cewa ya zama wajibi ga masu imani su amsa wannan kira, ko da kuwa da jan jiki ne a kasa {Rarrafe}. Lallai wannan Tattaki wani alami ne na amsa wancan kiran, kuma Milyoyin masu imani suna gudanar da shi a ko’ina a sassannin duniya.
A Najeriya, makiya wadanda suke adawa da tuna duk wani lamari wanda ya shafi Zuri’ar Manzonmu, Annabi Muhammad {S.A.W.A} a kowane lokaci suna shirya makirce-makirce domin kawowa wannan Tattaki namu tarnaki da ma kokarin hana aiwatar da shi ta hanyar yin amfani da kowane irin salo wanda ya hada har da amfani da karfi. Sanannen abu ne dai cewa, lamari na yin Tattaki domin nuna murna a kan wani al’amari ba bakon abu ba ne, haka nan kuma ba sabon lamari ba ne. Mutane da dama sun gudanara da Tattaki daga wurare masu nisan gaske domin nunawa tare kuma da bayyanar da murnarsu a kan nasarar da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya samu a zaben shekarar da ta gabata {2015}. Wannan Tattaki ke nan a kan lamarin siyasa. Mu kuwa namu Tattakin na nuna damuwa ne, kuma wani bangare ne na koyarwarmu ta addini. Ba mu taba tursasa wani ba a kan cewa sai ya yi wannan Tattaki, haka nan kuma ba mu taba cin zarafin wani ba a yayin wannan Tattaki, don haka ya zama wajibi a bar mu, mu gudanar da koyarwarmu ta addini.
A wannan shekarar, majiyoyi masu tushe sun tabbatar mana da cewa sun kulla makirci na kaddamar da hare-hare a kan masu gudanar da Tattakin a wurare da dama tare kuma da kona gidaje da kuma wuraren sana’o’i na masu Tattakin a yayin da suka bar garuruwansu domin gudanar da Tattakin. Wannan makirci ya kuma hada da yin amfani da zauna-gari-banza a kowace hanya ta masu gudanar da Tattakin, wadanda za su auka wa masu Tattakin, musamman da daddare a yayin da masu Tattakin suka yada zango domin su huta kafin da safe su ci gaba da tafiya. Sun shirya za su kashe duk wanda suka samu tare kuma da kwashe dukkanin matsugunnai na wucin-gadi da masu Tattakin suke yin amfani da su a yayin Tattakin. Haka nan kuma za su lalata ababen hawan da aka bayar domin a yi amfani da shi ta kowace irin hanya a yayin wannan Tattakin.Daga cikin makircin da aka kulla har da cewa za su fadi wa Asibitoci cewa kada su karbi duk wani wanda aka jikkata domin yi masa magani a yayin harin. Haka nan kuma sun dauki sunayen wadansu fitattun ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} wadanda za su yi kokarin kashewa a yayin wannan mummunar aika-aika da suka tsara aiwatarwa.
Akwai kuma batun kashe mutane 'yan kudancin kasar nan mazauna Arewacin Najeriya wadanda suka hada da Musulmi da Kiristoci domin haddasa rikici tsakanin al’umman da ke zaune a Kudanci da kuma Arewacin tarayyar Najeriya. Dukkanin wadannan makirce-makirce ne wadanda ake son a aiwatar da su cikin gajeren lokaci.
Daga cikin makirce-makirce kuwa wadanda suka kira na dogon lokaci sun hada da ci gaba da yin amfani da masu wa’azi wadanda ake biyan su kudi domin gudanar da wa’azi na cusa wa al’umma kiyayyar Harkar Musulunci a Najeriya {IMN}. Za a kuma samar wa da masu wa’azin dukkanin abubuwan da za su taimaka masu wajen cimma wannan bukata cikin sauki.
Kazalika, za a biya wadansu kungiyoyi na jama’a makudan kudade domin su bakanta Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} a ciki da wajen kasar nan.
Wannan lamari kuma sun bayya cewa akwai bukatar kula da taka tsan-tsan a yayin aiwatar da shi saboda yana samar wa Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} tausayawa da kuma samun goyan baya daga mutanen da ba a tsammani daga ciki da wajen Kasar nan, lamarin da suka cimma matsayar hana ci gaba da faruwarsa da kuma samar da akasin hakan ta kowace irin hanya.Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} tana so ta kara tabbatar wa da daukacin al’umma da ‘yan Najeriya ma’abota hankali da sahihin tunani da ma sauran al’umman kasa da kasa cewa wannan Tattaki na Yaumul Arba’een wanda ake gudanarwa a kowace shekara, wanda kuma za a gudanar da shi a cikin ‘yan makwanni masu zuwa, yana nan a matsayinsa na ayyuka na lumana na koyarwar addini wanda ma’abota imani suke gudanarwa tsawon shekaru biyar da suka gabata daga lokacin da aka fara aiwatar da shi.
Taskace yake a kundin tahiri cewa in ban da a shekarar da ta gabata, wadda jami’an tsaro suka fake da Boko-Haram suka tayar da Bom suka kashe mutane 32 a kan hanyar masu Tattaki daga shiyyar Kano, tafiyar ba ta taba samun tangarda ba ballantana kuma ta zama ta hatsaniya ko tayar da husuma ba. Dangane da batu na kazafin tare hanya kuwa, ba mu hana masu motoci da sauran masu amfani da hanya yin amfani da hanyoyi. Haka nan kuma sanannen abu ne wanda ya ke taskace a tarihi cewa mun rasa ‘yan uwanmu da dama a shekarun da suka gabata wadanda masu tukin ganganci suka buge a yayin Tattaki, wanda lallai haka ba zai iya faruwa ba idan da rufe hanya muke yi muna hana sauran al’umma yin amfani da hanyar.
Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} a kowane lokaci tana fuskantar cutarwa daga dukkanin matakan Gwamnati, ta hanyar yin amfani da dukkanin madafun iko da karfi na Jiha, wanda aikata hakan karara take mana ‘yancin mu ne na iya aiwatar da al’amuran addini da kuma ‘yancinmu na iya aiwatar da taro. Wannan yunkuri na jami’an tsaro na kawo tarnaki a kan Tattakin Yaumul Arba’een da ake gudanarwa shekara-shekara ya zama dole a fassara shi ta wannan fuska. Don haka muna ankarar da al’ummar tarayyar Najeriya da ma sauran al’ummar duniya cewa, duk wani abu da ya faru ga ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Najeriya {IMN} a yayin Tattaki, to gwamnatin Najeriya ita ke da alhakin faruwarsa.
Daga karshe, muna kara jaddada bukatarmu ta a gaggauta sako mana Jagoranmu wanda ake tsare da shi a boye, Shaikh Ibraheem Zakzaky da duk sauran wadanda ake tsare da su tun bayan kisan kiyashin da jami’an tsaro Sojojin Najeriya suka yi a garin Zariya a cikin watan Disambar shekarar da ta gabata 2015.
SA HANNU:
Ibrahim Musa
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Nijeriya
28/10/2016

Share on Thumblr
Submit to reddit