TSAKANIN IZALA DA BOKO HARAM.
Duk wanda ya saurari jawabin da Shugaban Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnati Lid Da’awati Wal Jihad, Malam Abubakar Shekau ya yi na baya-bayan nan, zai fahimci ba kawai babu bambanci tsakanin wannan kungiyar da kuma Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunna (IZALA) ba ne, amma abu daya ne a furuci da aiki.
A cikin jawabin nasa, Abu Muhammad Abubakar Shekau, ya jadadda hakikanin akidarsu da fito da ita sarari, inda ya kore dukkan wani shakku, shubuha, ko kuma cece-kuce a kan Malamai da littattafan da madogarar da suka dogara da ita wajen kafirtawa da kuma kashe al’ummar Musulmi da suke yi ba dare ba rana.
Bayan ya lissafo manyan Malamai irin su Shehul Islam Ibn Taimiyya, Allama Zahbi, Shaikh Muhammad Bn Abdlwahab da littafinsu da kuma irin fatawowin da suka bayar a kan halatta jinin wadanda ake tuhuma da aikata shika asgar, sai ya ce ba sa kafirtawa ko kashewa, sai wanda Allah da Manzo da Salafus Salih suka kafirta ko kuma suka ce a kashe ko da kuwa wannan mutumin yana Sallah yana Azumi ko yana jagorantar jama’a Sallar Juma’a.
A cikin jawabin nasa na kusan mintina 40, Abubakar Shekau, ya musanta ikirarin sojoji na cewa sun kashe shi, ko kuma an jikkata shi a hari ta sama da suka kai masa a maboyarsa. Ya tabbatar da cewa yana nan cikin koshin lafiya da walwala. Yana mai cewa ba zai mutu ba har sai ajalin da Allah ya diba masa ya cika.
Masu nazarin al’amura na ganin cewa duk masu kafirta Musulmi da kuma kashe su, ko kuma murna idan wasu azzaluman masu mulki sun kashe wasu raunana, ’yan Boko Haram ne a cikin wata rigar ta daban. Idan har gwamnati tana ganin in ta murkushe ’yan Boko Haram na cikin daji masu dauke da makamai shi ke nan, tamkar ta kashe maciji ne, ba ta sare kansa ba. Wajibi ne a tsige matsalar daga tushenta.
Wasu masana kuma suka hakikance cewa ba wani bambanci tsakanin Wahabiyyawa da ’yan Boko Haram; “In ma akwai bambanci a tsakaninsu, bai wuce na Dan Boko Haram din birni da na Kauye ba. Wahabiyawa ne ke yanke wa mutane hukunci kisa (a mumbari), ’yan Boko Haram kuma su zartar!”
Akwai wasu masanan da ke ra’ayin sanar da tsari a wa’azozin da ake yi a daina barin mutane suna wa’azi haka sakaka ba tare da control ba. Cikin masu wannan ra’ayin har da fitaccen Malamin Jami’ar nan, Dakta Sheriff Almuhajir, inda ya rubuta a turakarsa ta facebook cewa; “A kullum na ga video daga Shekau sai mamaki ya kama ni yadda gwamnati ke barin mutane suna wa’azi sakaka ba ‘control’ a kasar nan, sai an samu ’yan tawaye kuma a ce za a yake su.
“Duk da na sani ba kowa zai gane ba; amma a yanzu haka muna tare da mutane da bambancinsu da shi kawai aiki ne, amma akidar su daya, abin da yake fada shi suke fada, hujjojin da yake dogaro da su, ita ce tasu.
Bambancinsu kawai shi yana kashe Musulmai da sunan kafurci, su kuma suna kafurta su, amma ba su kashe su. Sai dai sun yarda kashe su daidai ne da karantarwa Musulunci. Kuma suna bayyana hakan a kalmominsu da ayyukansu, da kuma kudurce-kudurcensu. Wallahil azeem idan ba a yi ‘controlling’ wa’azi ba, nan gaba ’yan tawaye da za su bayyana sun fi karfin Shekau”, in ji shi.
#FreeZakzaky
#AllahProtcetZakzaky
Saleh Aliyu
25/09/2016