NAZARI
Shaikh Ibraheem Zakzaky zai ba da bahasi a gaban Kwamitin binciken da fadar Shugaban kasa ta kafa a kan Sojoji, yayin da masu lura da lamurra ke tir da sauraron sa a asirce
Kwamitin binciken keta hakkin bil'adama da fadar Shugaban kasa ta kafa a kan Sojojin Nigeria ya amince Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ba da bahasi a asirce, amma a Abuja. Yayin da aka dawo zaman Kwamitin a harabar kotun Tarayya Kaduna ranar 18 ga watan Oktoba 2017, koken da Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne aka saurara wanda kulen da aka fuskanta shi ne ko za a bar Shehin Malamin ya bayyana gaban Kwamitin ya ba da nasa bahasin ko ko a'a.
Lauya mai tsaya wa Harkar Musulunci a Nijeriya wanda ya jagoranci wasu Lauyoyi biyu a zaman kwamitin, ya sanar wa Kwamitin cewa sun gabatar da bukatar a ba da umurni na kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) don ya ba da bahasi. Har ila yau sun bukaci Kwamitin ya ba da umurni na a saurari koken da Harkar Musulunci a Nijeriya ta gabatar a Abuja. Mista kyon ya nuna cewa dalilin rokon sa na farko ya zama dole ne saboda ta saba ma ka'idar adalci a ce an saurari koken ba tare da an ji daga Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya ba.
Bukatar da ke neman a ba da umurnin sauraron koken zuwa Abuja ta zama tilas domin Lauyoyin Harkar Musulunci a Nijeriya ba su da masaniya cewa, Kwamitin zai zauna a Kaduna sai a kurarren lokaci, wanda tattara shaidun da za a gabatar zai yi wuya a wannan kurarren lokaci.
Amma shi Lauya mai wakiltar Sojojin Nijeriya, Farfesa Yemi Akinseye George SAN, ya nuna rashin amincewa a kan rashin cancantar sauraron koken da Harkar Musulunci a Nijeriya bisa doka, cewa an haramta Harkar a jihar Kaduna. Don haka ba za a saurari koken ba a Kaduna ko wani wuri a fadin Nijeriya, sai dai a canza kanun koken ya nuna cewa yana wakiltar 'yan Harkar Musulunci a daidaikun su, amma ba a matsayin wasu jama'a ba. Da yake mai da martani, Mista Kyon cewa ya yi Harkar Musulunci a Nijeriya bai takaita ga jihar Kaduna ba, amma motsi ne da ya watsu a ko'ina cikin Nijeriya, don haka za a saurari koken yadda yake.
Bayan sauraron hujjojin kowane bangare, Kwamitin ya jawo hankalin lauyan da ke tsaya wa Sojojin Nijeriya, Farfesa Akiseye SAN ga rahoton Hukumar binciken da jihar Kaduna ta kafa wanda ya nazarci matsalar Sojojin da 'yan Shi'a ya gabatar, wanda a ciki aka bayyana cewa Harkar Musulunci a Nijeriya "Jama'a ce da ake samu a duk fadin jihohin kasar Nijeriya." A bisa wannan ne Kwamitin ya amince da sauraron koken yadda aka gabatar da shi. An ayyana sauraron koken a Abuja daga ranar 30 ga Oktoba 2017 zuwa 3 ga Nuwamba.
A kan zancen da ake yi na Kwamitin ya ba da umurnin a kawo Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya don ya ba da nasa bahasin, Farfesa Akiseye George ya sanar da Kwamitin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba ya hannun rundunar Sojan Nijeriya. Amma Mista Kyon ya gaya wa Kwamiti cewa Malam Ibraheem Zakzaky (H) na hannun hukumar tsaron kasa DSS, don haka yana da gayar muhimmanci Kwamitin ya ba da umurnin a kawo Shaikh Zakzaky (H), don "rashin sauraron Shaikh Zakzaky (H) tsantsan rashin adalci ne, idan ba a kawo shi ba," kamar yadda ya ce.
Yayin da Shugaban Kwamitin ke yanke hukunci, ya yi la'akari da bukatar Lauyan da ke tsaya wa Harkar Musulunci a Nijeriya, inda ya umurci dukkanin masu ruwa da tsaki su tabbatar an kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gaban wannan Kwamitin bincike tare da tabbatar da cewa, an tsara yadda zai bada na shi bahasin a wurin da ake tsare da shi ko kuma wani wuri na daban da ya dace tare da daukan kwararan matakai, domin abin da Kwamiti ya kira "Matakan tsaron da za su taso wanda zai shafi wannan." Kwamitin ya kuma ba da umurnin cewa, Lauyoyin masu koken da na Sojojin Nijeriya za su kasance a wurin da su Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) za su ba da shaida, amma a asirce.
Manazarta shirin halartar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun yi inkarin wannan matsayi da Kwamitin ya dauka tare da bayyana shakkun za a yi adalci a wannan yanayi na zaman sirri. Kodayake wasu na ganin, an sami babban ci gaba, ganin cewa Shaikh Zakzaky (H) zai bayyana ya ba da nasa bahasin abin da ya faru. Wasu kuma na ganin cewa sauraron bahasin sa a asirce alama ce da ke nuna cewa ba za a yi adalci ba, alhali Sojojin Nijeriya sun aiwatar da hare-harensu su ne a sarari. Dadin dadawa wasu na ganin Kwamitin ya fadi ba nauyi, domin ya kasa cimma muradin kafa shi na sauraron koke a bainar jama'a.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko sauran shaidun da Harkar Musulunci a Nigeria ke da niyyar gabatarwa don tabbatar da hare-haren da Sojojin Nigeria suka aiwatar na kisan kiyashin Zariya daga 12 zuwa 14 ga watan Disamba 2015 su ma za su kasance ne a asirce. Harkar Musulunci a Nijeriya dai dama ta nuna shakku tunda farko na ingancin Kwamitin a matsayin mai cikkakken 'yanci.
A wata sabuwa kuma, Shugaban Kwamitin ya furta cewa akwai wani koken na daban a kan Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Wannan koken na biyu, wanda wani Muhammad Ali ya gabatar ne a rana ta biyu na zaman Kwamitin, baya ga wanda aka bada a rana ta farko. Ba a san abin da koken ya kunsa ba, tunda ba a ba ma Lauyoyin Harka ba tukun. Amma Shugaban Kwamitin ya ce duk koken da ya shafi Harkar Musulunci a Nijeriya za a saurare su a Abuja, tsakanin 30 ga Oktoba zuwa 3 ga Nuwamba 2017.
Muhammad Ali dai shi ne Sojan haya da hukumar Sojojin Nijeriya ta ba shi kwangilar tsarawa da aiwatar da duk wani makirci da suka aiwatar a kan Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) lokacin zaman Hukumar bincike da jihar Kaduna (JCI) ta kafa a can baya, shekarar 2016. An gan shi a sarari Sojojin Nijeriya na karfafa shi ya yi sauri ya gabatar da kokensa yayin da Kwamitin ke zaman sa a wannan ranar. Da kamar wuya a ce za su iya karyata mummunan ta'addancin da suka aikata a kan bil'adama a sarari, wanda hatta hukumar binciken da jihar Kaduna ta kafa ta tabbatar da wadannan laifuffuka.
Kamar kullum kwamitin fafutukar ganin an saki Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na nan tafe da karin haske, a duk lokacin da ya samu.
© #FreeZakzaky Campaign Committee, Oktoba 2017