TASIRIN HARIN IRAN AKAN SANSANONIN AMURKA. Part 2
Ibrahim Ahmad Daurawa.
TASIRIN HARIN AKAN SIYASAR AMURKA DA IRAN.
Wannan harin ya kunyata Rundunar Sojan Amurka wacce akewa lakabi da Daular ce mai zaman kanta wacce ba a taba irinta ba a Tarihin Daulolin da suka gabata. Kuma ya wulakanta Shugabannin Amurka masu Matsanancin Girman Kai, masu Siyasar Danniya da Babakere. Sannan ya Sulmiyo da Girman kan Kasar Amurka ta fadi Wanwar. Kima da Matsayin Amurka a matsayin 'Super Power' guda daya Tilo ta fadi. Matsayin Amurka na Yar Sandar Duniya tsumagiyar kan hanya ya zube. Saboda tsoron Danniya da Murdiyar Amurka da ake a Duniya ba a taba samun wata Kasa da ta kai mata hari ba a wannan Karnin, amma sai ga Iran wacce take fama da takunkumi iri iri na shekaru 40, ta yi alkawari zata kai Mata Hari, Amurka ta sha alwashin Idan ta kawo sai buzunta. Kuma ta cika alkawarinta amma Amurka ta kasa cika alkawarinta na baje Wajaje 52 na Iran, ta ma buge da neman Sulhu. Wannan bai taba faruwa a Tarihin Amurka ba, akai Mata hari ta ce a zo a zauna ayi Sulhu. Karshe dai ta buge da batun Takukunmi. Wannan wane irin abin Kunya ne.
Wannan ya saka matsayin Amurka a wajen Yan Kanzaginta ya zube, sannan ya bude Kofar da sauran masu yiwa Amurka tsiwa su ga cewa suma za su iya, su kara bijere Mata. Kasashen Gabas ta tsakiya da suke ganin Amurka kamar Allah ce suka mikawa Mata Wuya, wai zata karesu. Gashi yau Amurka ta Kasa kare kanta, balle kuma ta karesu. Wannan ya jefa Tsoro a zukatansu. Nan da nan Natanyahu Shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya fito ya ce su babu ruwansu da Rigimar da ake a tsakanin Kasar Iran da Amurka don haka kada a tsoma su a ciki. Dole ya fito ya fadi haka saboda dama da Makaman Garkuwa daga Makamai Masu Linzami na Kasar Amurka suke tutiyar kare kansu daga Makaman kasar Iran, yanzu gashi Amurka ta kasa kare kanta daga harin Iran.Masanan Makamai na Kasar Isra'ila sun fito fili sun ce Mizayal din da Iran ta harbo, Makaman Isra'ila na Kariya ba za su iya karesu ba. Saboda an kera su ne a bisa fasahar Garkuwar makamai masu Linzami na Kasar Amurka wadanda suka gaza kare ko Mizayal daya daga wadanda kasar Iran ta harbo musu.
Wannan ya saka Saudiya suka yi lakwas, haka sauran Kasashen Tekun Fasha cikinsu ya duri ruwa. Saboda Amurka da suke Tinkaho da ita yau ta gaza Kare kanta daga Makaman Kasar Iran.
Wannan Harin da Iran ta kai ya bata matsayi da Girma a Idon Duniya, ya fito da ita daga kangin da Amurka ta jefa ta. Yanzu ta zama cikakkiyar Jagoran Masu fafutuka da Danniyar Amurka a Gabas Ta tsakiya. ya kuma baiwa sauran abokanta Karfin hali da Kwarin Gwiwa na Tunkarar Amurka da Kawayenta gaba Gadi.
Makaman Kasar Iran yanzu za su samu kasuwa a Kasuwar Cinikayyar Makamai. Masanan Kimiyya da Kere-kere na Iran za su yi Kima da tsada a wajen Takwarorinsu na Duniya. Abin da zai kawo budin Tattalin Arziki da mallakar wasu Fasahohin a cikin sauki. Tun bayan Harin da aka kai a Aramco, wani Kamfani a Rasha ya bukaci hadin Gwiwa da Kamfanin da ya Kera Drones din da Yan Houthi suka kai Hari kan Aramco saboda akwai sabuwar Fasaha ta wajen kera Injin Drones din, an Kerashi a bisa Fasahar Turbo Jet Engine, wanda sabuwar Fasaha ce a Kera Jiragai marasa Matuki.
Na karanta wani Bincike da wani Masanin Makamai masu Linzami ya yi Nazari akan Tarkacen Makamai Masu Linzami da Iran ta harbo a Sansanin Amurka. Ya yi bayani na Ilimi da Fasaha, ya kuma Yabawa irin ci gaban da Makeran Makamai masu Linzami na Kasar Iran suka kawo har Zanen banbancin da yake a tsakanin fasahar Kera Makama masu linzami wacce aka sani da wacce aka iya Nazari a Makamai masu Linzami na Kasar Iran. Wanda ya nuna shi ya baiwa Makamai karin Sauri da kuma saukin Sarrafawa idan an harbo su, yadda za su sauka akan wajen da aka saita su.
Wannan wani ci gaba ne kuma abin alfahari cewa Musulmi ma za su iya taka rawa suma iya sauya Fasahar Kere-kere ta Zamani. Yanzu kasar Iran ta zama abin koyi kuma Sabuwar alkiblar Kimiya da fasaha Kamar yadda Kasashen Musulmi suka taka a karnin baya lokacin da ake ruko da Musulunci sau da Kafa.
Wannan zai saka Iran taka rawar gani a Siyasar Duniya da yiwa Amurka katsalanda ga Muradunta na Gabas ta tsakiya. Yan Siyasar da Masu Mulkin Yankin dole su dinga safa da marwa a Birnin Tehran neman Sulhu. Masu yiwa Amurka hamayya a Siyasar Duniya irin su Rasha,China da North Korea dss, za su baiwa Kasar Iran Muhimmanci da goyan baya, wannan zai sauya Akalar Siyasar Duniya ya zama akwai Matsayi na tsakiya, ba kamar yadda Amurka ta shata cewa 'kodai ka zama tare da mu ko kuma kai dan Ta'adda ne.' Yanzu akwai wani Matsayi na wadanda ba sa tare da Amurka kuma ba yan Ta'adda bane, sannan dole a dama da su.
Kasashen Larabawa da suka baiwa Amurka Kasarsu suka Kafa Sansanonin Soja. Dole su fara tunanin abin da zai biyo baya wajen hada kai da Amurka a kai wa Iran Hari. Don sun san cewa Amurka ba zata iya karesu ba idan suka tsokana Kasar Iran. Wannan kuma zai kara jefa su cikin Tashin Hankali, saboda su dai ba za su iya hana Amurka amfani da Sansaninsu na Kasarsu ba, don ba su suke Iko da Kasar ba Amurka ce. Kuma idan haka ta faru Iran zata mayar da martani. Wannan ne ma ya saka Kasar Saudiya ware Makudan Kudade har Dala Miliyan Dubu suka zuba a Lalitar Amurka don su basu Tsaro. Amma sun manta Makaman Amurka da Sojojinsu suna nan aka kaiwa Kamfanunsu hari na Aramco ba su iya hangowa ko kare koda Makami daya daga cikin Sama da Talatin da aka harbo ba.
Amurka kuma dole ta yi taka tsan-tsan akan duk wani Mataki da zata dauka akan kasar Iran, don ta san cewa Iran tana da karfin da zata kare kanta da kuma kawai duk wani sansanin Amurka da Kadarorinta hari a duk inda suke a Gabas ta tsakiya.
Kaifin fasahar Makaman Iran ya baiyana a fili yada suka zabi wajajen da suke so suka kaiwa hari a nisan sama da Kilomita 700. Kamar yadda Rundunar Sojan Iran ta ce ba manufar harin ne su kashe Sojojin Amurka ba, sun yiwa Amurka Gargadi ne cewa Suna da karfin kai mata hari a duk wajen da suke so a Yankin. Sannan ya fito da manufar Yaki a wajen Musulmi, saboda Iran tana da zabi ta kashe duban Sojojin Amurka amma bata yi hakan ba sai yan Kalilan. Wannan ya nuna Kisa bashi ne Muradi a Yakin Musulmi ba, kuma wannan shi ne karo na biyu da Sojan Kasar Iran suka tausayawa Sojan Amurka na farko a lokacin da suka harbo Jirgi mara Matuki na Kasar Amurka wanda ya fi kowane tsada da kayan satar bayanai. Amma sai suka kyale daya Jirgin da yake dauke da Sojoji har sama da Talatin aka yi masa gargadi suka arce. A wannan ma haka ta faru, Sojojin da suka tsallake Rijiya da baya sun tabbatar da haka.
Babban abin da yake damun Amurka shi ne an kaiwa Sansanin Sojanta mafi Girma da tsaro a gabas ta taskiya hari an yi rugu-rugu da shi, bata iya kareshi ba. Kuma ta kasa cika alkawarin da ta yi na mayar da martani. Abin da ya taba Mutuncinta da matsayin Sojanta. Sai dai mu zuba Ido mu gani me Amurka zata ta yi ta dawo da Kimarta a Idon Duniya. Za ta tsaya ne akan Saka Takunkumi ko zata rama
A karshe wannan harin ya baiwa Musulmi Girma da matsayi cewa dogaro da Allah jari ne. Duk wanda ya dogara da Allah ya bi dokokinsa, Allah zai buda masa taskarsa ta Ilimi ya zama Gagabaradau a Duniya.