MUZAHARAR TSARE SHEIKH ZAKZAKY KWANA 2000 A BIRNIN KANO.
Yau alhamis da yamma 03/06/21, yan uwa Maza da Mata almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na Da'irar Kano suka fito Muzaharar cika kwana 2000 da Buhari yiwa Sheikh Zakzaky haramtaciyyar Tsarewa a Kurkuku.
An hau sahu da Misalin Karfe Biyar saura kwana a daura da Gidan Mumbayya dake Gwammaja Kano. Sannan aka yi kwana aka mike Titi Gwammaja zuwa Kofar Mazugal. an fito ta Kofar Mazugal aka hau Titin IBB zuwa Mayanka, zuwa Kasuwar Kofar Wambai zuwa daura da Filin Idi daf da Kantin Kwari nan aka Kammala Muzaharar.
Mahalarta Muzaharar suna tafe suna rera 'Free Zakzaky kai Buhari Shaidai.' wasu na fadi 'Kwana dubu yau da tsare Mana Jagora Free Zakzaky dole.'
Wasu Yan Uwan kuma suna rabawa Mutame masu Kallon Muzaharar da masu tafiya Takardar bayyana dalilin fitowar mu da kuma nuna irin Ta'addancin da Buhari ya yiwa Sheikh Zakzaky da sauran almajiransa. Takardar na dauke da yadda Buhari ya bijerewa umarnin babbar Kotu a Abuja na ya saki Sheikh Zakaky ya gida masa gida ya kuma biyashi diyyar Naira Miliyan Hamsi tsarewar da ya yi masa a bisa zalunci. Wanda babu wani umarnin Kotu da Buhari ya girmama, ya ci gaba da tsareshi da kokarin halakashi.
Malam Aliyu Rimin Gado ne ya yi takaitaccen Jawabin rufewa. A cikin Jawabinsa ya kara Jaddada Kiran yan uwa na dole ne Azzalumai su gaggauta sako mana jagora. Ya kuma tsinewa duk wadanda suke Zaluntar Sheikh Zakzaky da masu jin dadi. Ya kuma roki Allah da ya gaggauta Kubutar da Sheikh Zakzaky ya bashi lafiya da mai dakinsa.
Malam Adamu Gobirawa ne ya rufe taron da addu'a. An kammala lafiya.




