An Kammala Mu'utamar na Kwana biyu da Internet Forum suka shirya a Garin Kazaure Yankin Jigawa. Malam Sunusi Abdulkadir ne ya yi Jawabin rufewa. Sidiya Hauwa Ringim tana Jawabin Godiya. Inda ta godewa Allah da ya ba Mu Ikon Shiryawa da Kammala Lafiya ba tare da an Samu wata Matsala ba.
Sannan ta godewa Malam Sunusi Abdulkadir da Malam Ibrahim Kazaure Wakilin Yan uwa na Kazaure Zone. Da Malaman da suka gabatar da Jawabai musamman Dr Muktar Wanda ya gabatar da Jawabi kai tsage daga Kasar Malasiya. Sannan da sauran Yan uwa da suka Zo daga Yankuna daban daban da har daga Kasar Nijar. Ta yiwa Chairman na Internet Forum na Kasa Ibrahim Daurawa akan Jajircewar da ya yi wajen Shiryawa da gabatar da Mu'utamar din har aka kammala.
A Karshe ta yiwa fatan Allah ya maida kowa Gidansa Lafiya.