Welcome to the official website of Internet Forum of the Islamic Movement in Nigeria, under the spiritual leadership of his eminence, Sayyid Ibraheem Ya'qoub Zakzaky(H).
TAKARDAR MANEMA LABARAI
Ba da wa'adi da kuma barazanar ta da hankali ba dabi'armu ba ce
Yana da muhimmanci mu isar da wannan bayani cewa Harkar Musulunci a Najeriya ba ta taba ba da wa'adi ko kuma barazanar aukar da fitina a kan kowane mutum, wata kungiya ko gwamnati ba a tsawon shekaru 40 da fara wannan tafiya. Kuma wannan ba zai taba canzawa ba. Amma sai ga shi wani rahoton manema labarai a kwanakin nan ya nuna cewa 'an ba da wa'adi'.
Da alama dai Jami'an tsaro ne ke shirin kai jerin wasu hare-hare sai kuma daga baya su jingina alhakin harin ga Harkar Musulunci lokacin da wa'adin da ake cewa an ba da ya cika, don dai su yi amfani da wannan dama wajen cimma abin da suka kasa tsawon lokaci; wato su jingina fafutikar neman a saki Shaikh Zakzaky da ake yi na lumana a matsayin fitina domin su juya tunanin al'umma a kan Harkar Musuluncin sannan kuma su nuna kisan kiyashin da suka yi a watan Disamba a matsayin daidai. Lallai muna sane da wannan fuska biyu na makiyan mu, na nuna kamar suna kokarin neman a saki Jagoranmu ne, amma a zuciyar su suna nufin mugunta ne. Sun boye Shaikh Zakzaky ba tare da sun bar lauyoyinsa da likitocinsa sun gana da shi ba, amma kuma suna cewa wai suna ajiye shi domin 'ba shi kariya' ne.
Za mu so mu sake karyata duk wani barazanar aukar da fitina da sunan mu. Harkar Musulunci ba ta taba ba, kuma ba zata taba zama ita ke da alhakin tayar da tarzoma da wasu can za su yi da sunanmu ba. Za mu ci gaba da bin duk wasu hanyoyi da suka dace, na yanci da kuma wanda kundin tsarin mulkin kasa ya tabbatar domin cimma manufofinmu, ba kuma za a iya yi mana wata barazana Don mu sare ko mika wuya ba. Gangamin mu na lokaci-lokaci, Muzaharori da kuma duk wata fafutika da muka saba yi za mu ci gaba kamar yadda muka saba ba tare da tsoro ko fargaba ba. Kuma za mu ci gaba da neman hakkin mu a kotunan cikin kasa da kuma na kasa da kasa masu adalci kamar yadda muke yi tun watanni tara da suka gabata.
Daga karshe, muna amfani da wannan dama wajen yin kira ga mutane masu sanin ya kamata da su tsananta matsin lamba a kan gwamnatin Najeriya don ta saki Jagoranmu Shaikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba, domin ya je a kula da lafiyarsa.
Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya.
08050786093
29/09/2016
TSAKANIN IZALA DA BOKO HARAM.
Duk wanda ya saurari jawabin da Shugaban Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnati Lid Da’awati Wal Jihad, Malam Abubakar Shekau ya yi na baya-bayan nan, zai fahimci ba kawai babu bambanci tsakanin wannan kungiyar da kuma Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunna (IZALA) ba ne, amma abu daya ne a furuci da aiki.
A cikin jawabin nasa, Abu Muhammad Abubakar Shekau, ya jadadda hakikanin akidarsu da fito da ita sarari, inda ya kore dukkan wani shakku, shubuha, ko kuma cece-kuce a kan Malamai da littattafan da madogarar da suka dogara da ita wajen kafirtawa da kuma kashe al’ummar Musulmi da suke yi ba dare ba rana.
Bayan ya lissafo manyan Malamai irin su Shehul Islam Ibn Taimiyya, Allama Zahbi, Shaikh Muhammad Bn Abdlwahab da littafinsu da kuma irin fatawowin da suka bayar a kan halatta jinin wadanda ake tuhuma da aikata shika asgar, sai ya ce ba sa kafirtawa ko kashewa, sai wanda Allah da Manzo da Salafus Salih suka kafirta ko kuma suka ce a kashe ko da kuwa wannan mutumin yana Sallah yana Azumi ko yana jagorantar jama’a Sallar Juma’a.
A cikin jawabin nasa na kusan mintina 40, Abubakar Shekau, ya musanta ikirarin sojoji na cewa sun kashe shi, ko kuma an jikkata shi a hari ta sama da suka kai masa a maboyarsa. Ya tabbatar da cewa yana nan cikin koshin lafiya da walwala. Yana mai cewa ba zai mutu ba har sai ajalin da Allah ya diba masa ya cika.
Masu nazarin al’amura na ganin cewa duk masu kafirta Musulmi da kuma kashe su, ko kuma murna idan wasu azzaluman masu mulki sun kashe wasu raunana, ’yan Boko Haram ne a cikin wata rigar ta daban. Idan har gwamnati tana ganin in ta murkushe ’yan Boko Haram na cikin daji masu dauke da makamai shi ke nan, tamkar ta kashe maciji ne, ba ta sare kansa ba. Wajibi ne a tsige matsalar daga tushenta.
Wasu masana kuma suka hakikance cewa ba wani bambanci tsakanin Wahabiyyawa da ’yan Boko Haram; “In ma akwai bambanci a tsakaninsu, bai wuce na Dan Boko Haram din birni da na Kauye ba. Wahabiyawa ne ke yanke wa mutane hukunci kisa (a mumbari), ’yan Boko Haram kuma su zartar!”
Akwai wasu masanan da ke ra’ayin sanar da tsari a wa’azozin da ake yi a daina barin mutane suna wa’azi haka sakaka ba tare da control ba. Cikin masu wannan ra’ayin har da fitaccen Malamin Jami’ar nan, Dakta Sheriff Almuhajir, inda ya rubuta a turakarsa ta facebook cewa; “A kullum na ga video daga Shekau sai mamaki ya kama ni yadda gwamnati ke barin mutane suna wa’azi sakaka ba ‘control’ a kasar nan, sai an samu ’yan tawaye kuma a ce za a yake su.
“Duk da na sani ba kowa zai gane ba; amma a yanzu haka muna tare da mutane da bambancinsu da shi kawai aiki ne, amma akidar su daya, abin da yake fada shi suke fada, hujjojin da yake dogaro da su, ita ce tasu.
Bambancinsu kawai shi yana kashe Musulmai da sunan kafurci, su kuma suna kafurta su, amma ba su kashe su. Sai dai sun yarda kashe su daidai ne da karantarwa Musulunci. Kuma suna bayyana hakan a kalmominsu da ayyukansu, da kuma kudurce-kudurcensu. Wallahil azeem idan ba a yi ‘controlling’ wa’azi ba, nan gaba ’yan tawaye da za su bayyana sun fi karfin Shekau”, in ji shi.
#FreeZakzaky
#AllahProtcetZakzaky
Saleh Aliyu
25/09/2016
Calling together all brothers and sisters who are interacting with social Networks to a single platform in order to conform with the accepted ideology of the movement in spreading the message of the movement through the internet.