Welcome to the official website of Internet Forum of the Islamic Movement in Nigeria, under the spiritual leadership of his eminence, Sayyid Ibraheem Ya'qoub Zakzaky(H).
KUNDIN TATTAKI 2015, YAN TABLIK.
Daya daga cikin Tawaga mai Muhimmanci lokacin Tattaki sune Masu isar da sakon Tattaki ga masu Kallon Tattaki da kuma Garuruwa da kauyukan kan Hanya. Wadanda ake Kira yan Tablik.
Yan Tablik sun hada Mata da Maza, suna amfani da harshen Hausa, Fulatanci, Turanci da ma Igbo. Suna tafe suna yiwa Mutane bayin abin da ya sa muka fito da hakikanin abin da ya faru a Karbala ga Iyalan Manzon Allah. Wannan ya na saka Mutane da yawa sanin abin da aka yiwa Imam Husain a,s a Karbala abin da ya saka wasu Kuka don tausayawa.
Suna bin bakin Titi suna yiwa duk wani Gungun Yan kallo Bayani. Wasu kuma suna shiga cikin Kauyuka da Rugajen Fulani. Suna yiwa Fulanin bayani da harshen Fulatanci don su fahimce su Sosai. Wannan ya sa Garuruwan da Rugajen kusa da ke bakin hanya suna da masaniyar akan abin da ya sa muke Tattaki don haka Wa'azin da Yan Izala suke bin Garuruwan bakin hanya sun yiwa Mutane Karya kafin a fara Tattakin don su farmana ko su hanamu Masauki, ba shi da tasiri a wajen Jama'ar da suke yiwa Karya.
Wani Mai Tablik da Fulantaci ya fada mani wata Rana ya shiga wata Ruga sai da ya shiga cikin Ruwa da Kayoyi ya isa Rugar ya fara bayani, sai wata Tshohuwar Bafulatana ta karbe bayanin da yake yiwa Jikokinta ta shiga bashi labarin Waki'ar Ashura ya ce wani abin ma bai sani sai a rannan. A karshe ta cewa Jikonta Yan Mata ku bishi idan kuna son zuwa ayi da ku akan gaskiya suke. Ta yi alkawarin badi shekara mai zuwa da ita za ayi da Jikokinta.
Yan Tablik ba su hutawa kamar yadda yan Internet Forum suke Kutsawa koina haka suma suke kutsawa. Sune suke yiwa Yan Kallo bayanin masu wasan Kwaikwayo wadanda suke tafiya cikin Sahun tattaki cewa wannan shi ne irin yadda aka saka Jikokin Manzon Allah a Sarka ana duka. Abin da yake tayar da hankalin Yan Kallo wasu suke Kuka da hawaye.
Yan tablik suna taimkawa gaya wajen isar da sakon Imam Husain a.s ga Mutane daban daban. Wannan yana taimakawa wajen fahimtar Shi'aci da rage gaba da Kiyaiyar da wasu Jahilai suke yiwa Shi'a. Suna kuma rusa Karerayin da aka yiwa yan Shi'a.
NAZARI
Shaikh Ibraheem Zakzaky zai ba da bahasi a gaban Kwamitin binciken da fadar Shugaban kasa ta kafa a kan Sojoji, yayin da masu lura da lamurra ke tir da sauraron sa a asirce
Kwamitin binciken keta hakkin bil'adama da fadar Shugaban kasa ta kafa a kan Sojojin Nigeria ya amince Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ba da bahasi a asirce, amma a Abuja. Yayin da aka dawo zaman Kwamitin a harabar kotun Tarayya Kaduna ranar 18 ga watan Oktoba 2017, koken da Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne aka saurara wanda kulen da aka fuskanta shi ne ko za a bar Shehin Malamin ya bayyana gaban Kwamitin ya ba da nasa bahasin ko ko a'a.
Lauya mai tsaya wa Harkar Musulunci a Nijeriya wanda ya jagoranci wasu Lauyoyi biyu a zaman kwamitin, ya sanar wa Kwamitin cewa sun gabatar da bukatar a ba da umurni na kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) don ya ba da bahasi. Har ila yau sun bukaci Kwamitin ya ba da umurni na a saurari koken da Harkar Musulunci a Nijeriya ta gabatar a Abuja. Mista kyon ya nuna cewa dalilin rokon sa na farko ya zama dole ne saboda ta saba ma ka'idar adalci a ce an saurari koken ba tare da an ji daga Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya ba.
Bukatar da ke neman a ba da umurnin sauraron koken zuwa Abuja ta zama tilas domin Lauyoyin Harkar Musulunci a Nijeriya ba su da masaniya cewa, Kwamitin zai zauna a Kaduna sai a kurarren lokaci, wanda tattara shaidun da za a gabatar zai yi wuya a wannan kurarren lokaci.
Amma shi Lauya mai wakiltar Sojojin Nijeriya, Farfesa Yemi Akinseye George SAN, ya nuna rashin amincewa a kan rashin cancantar sauraron koken da Harkar Musulunci a Nijeriya bisa doka, cewa an haramta Harkar a jihar Kaduna. Don haka ba za a saurari koken ba a Kaduna ko wani wuri a fadin Nijeriya, sai dai a canza kanun koken ya nuna cewa yana wakiltar 'yan Harkar Musulunci a daidaikun su, amma ba a matsayin wasu jama'a ba. Da yake mai da martani, Mista Kyon cewa ya yi Harkar Musulunci a Nijeriya bai takaita ga jihar Kaduna ba, amma motsi ne da ya watsu a ko'ina cikin Nijeriya, don haka za a saurari koken yadda yake.
Bayan sauraron hujjojin kowane bangare, Kwamitin ya jawo hankalin lauyan da ke tsaya wa Sojojin Nijeriya, Farfesa Akiseye SAN ga rahoton Hukumar binciken da jihar Kaduna ta kafa wanda ya nazarci matsalar Sojojin da 'yan Shi'a ya gabatar, wanda a ciki aka bayyana cewa Harkar Musulunci a Nijeriya "Jama'a ce da ake samu a duk fadin jihohin kasar Nijeriya." A bisa wannan ne Kwamitin ya amince da sauraron koken yadda aka gabatar da shi. An ayyana sauraron koken a Abuja daga ranar 30 ga Oktoba 2017 zuwa 3 ga Nuwamba.
A kan zancen da ake yi na Kwamitin ya ba da umurnin a kawo Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya don ya ba da nasa bahasin, Farfesa Akiseye George ya sanar da Kwamitin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba ya hannun rundunar Sojan Nijeriya. Amma Mista Kyon ya gaya wa Kwamiti cewa Malam Ibraheem Zakzaky (H) na hannun hukumar tsaron kasa DSS, don haka yana da gayar muhimmanci Kwamitin ya ba da umurnin a kawo Shaikh Zakzaky (H), don "rashin sauraron Shaikh Zakzaky (H) tsantsan rashin adalci ne, idan ba a kawo shi ba," kamar yadda ya ce.
Yayin da Shugaban Kwamitin ke yanke hukunci, ya yi la'akari da bukatar Lauyan da ke tsaya wa Harkar Musulunci a Nijeriya, inda ya umurci dukkanin masu ruwa da tsaki su tabbatar an kawo Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gaban wannan Kwamitin bincike tare da tabbatar da cewa, an tsara yadda zai bada na shi bahasin a wurin da ake tsare da shi ko kuma wani wuri na daban da ya dace tare da daukan kwararan matakai, domin abin da Kwamiti ya kira "Matakan tsaron da za su taso wanda zai shafi wannan." Kwamitin ya kuma ba da umurnin cewa, Lauyoyin masu koken da na Sojojin Nijeriya za su kasance a wurin da su Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) za su ba da shaida, amma a asirce.
Manazarta shirin halartar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun yi inkarin wannan matsayi da Kwamitin ya dauka tare da bayyana shakkun za a yi adalci a wannan yanayi na zaman sirri. Kodayake wasu na ganin, an sami babban ci gaba, ganin cewa Shaikh Zakzaky (H) zai bayyana ya ba da nasa bahasin abin da ya faru. Wasu kuma na ganin cewa sauraron bahasin sa a asirce alama ce da ke nuna cewa ba za a yi adalci ba, alhali Sojojin Nijeriya sun aiwatar da hare-harensu su ne a sarari. Dadin dadawa wasu na ganin Kwamitin ya fadi ba nauyi, domin ya kasa cimma muradin kafa shi na sauraron koke a bainar jama'a.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko sauran shaidun da Harkar Musulunci a Nigeria ke da niyyar gabatarwa don tabbatar da hare-haren da Sojojin Nigeria suka aiwatar na kisan kiyashin Zariya daga 12 zuwa 14 ga watan Disamba 2015 su ma za su kasance ne a asirce. Harkar Musulunci a Nijeriya dai dama ta nuna shakku tunda farko na ingancin Kwamitin a matsayin mai cikkakken 'yanci.
A wata sabuwa kuma, Shugaban Kwamitin ya furta cewa akwai wani koken na daban a kan Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Wannan koken na biyu, wanda wani Muhammad Ali ya gabatar ne a rana ta biyu na zaman Kwamitin, baya ga wanda aka bada a rana ta farko. Ba a san abin da koken ya kunsa ba, tunda ba a ba ma Lauyoyin Harka ba tukun. Amma Shugaban Kwamitin ya ce duk koken da ya shafi Harkar Musulunci a Nijeriya za a saurare su a Abuja, tsakanin 30 ga Oktoba zuwa 3 ga Nuwamba 2017.
Muhammad Ali dai shi ne Sojan haya da hukumar Sojojin Nijeriya ta ba shi kwangilar tsarawa da aiwatar da duk wani makirci da suka aiwatar a kan Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) lokacin zaman Hukumar bincike da jihar Kaduna (JCI) ta kafa a can baya, shekarar 2016. An gan shi a sarari Sojojin Nijeriya na karfafa shi ya yi sauri ya gabatar da kokensa yayin da Kwamitin ke zaman sa a wannan ranar. Da kamar wuya a ce za su iya karyata mummunan ta'addancin da suka aikata a kan bil'adama a sarari, wanda hatta hukumar binciken da jihar Kaduna ta kafa ta tabbatar da wadannan laifuffuka.
Kamar kullum kwamitin fafutukar ganin an saki Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na nan tafe da karin haske, a duk lokacin da ya samu.
© #FreeZakzaky Campaign Committee, Oktoba 2017
TAKARDAR MANEMA LABARAI
Ba mu yarda da yunkurin kwace mana filin Husainiyya Bakiyyatullah Zariya ba
A ranar 20/07/17 ne aka ga wasu sojojin rundunar sojin Nijeriya suna ba da kariya ga wasu leburori da gwamnati ta yi hayar su don katange filinmu, inda Cibiyar Musulunci ta Husainiyya Bakiyattullah take, kafin rusa ta da sojoji suka yi yayin da suka kawo harinsu na kisan kiyashi a Disamban 2015.
Hukumar kula da ci gaban birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) da jami’anta sun nuna rashin masaniyarsu dangane da wannan gini da ake yi a filinmu yayin da aka tuntube su. Wannan shi ya kara tabbatar da zargin da ake yi cewa, wannan aiki ne na gwamnatin Tarayya karkashin kulawar sojoji kai tsaye, wadanda suke da boyayyar bukata na kwace filin tun da dadewa.
Muna so mu jawo hankulan jama’a da kuma al’ummar kasa da kasa zuwa ga cewa, wannan fili da aka gina Husainiyya Bakiyyatullah a kansa, an mallake shi ne daga wadanda suka mallaki filin tun asali. Muna da dukkan takardun da suka dace kan haka. Kuma duk da cewa, an rurrusa ta ba tare da hujja ta shari’a ba daga hadin gambizar sojoji da gwamnatin jihar Kaduna karkashin Elrufa’i, filin dai namu ne. Don haka gwamnatin Tarayya ba ta da wata hujja na yin gini a filin da ba nata ba. A hakikanin gaskiya wannan shi ne share-wuri-zauna mafi muni.
Kuma yana da kyau a lura cewa, rusa Husainiyya yana cikin wuraren da yanzu haka an shigar da kara a kansa a gaban kotun Tarayya da ke Kaduna. Har ila yau kuma, wannan wuri, wuri ne da aka aikata laifi a kansa, inda gwamnati ta kashe daruruwan fararen hula ‘yan kasa. Don haka kuskure ne babba gwamnati da rana tsaka ta ce za ta lalata shaidar ta’annutin da aka yi a wurin.
A sarari yake cewa, wannan yunkuri na baya-bayan nan na kwace mana fili wani ci gaba ne na danne mana hakkinmu na ’yan Adam. Mun yi amanna cewa, wannan yunkuri na katange filinmu wani yunkuri ne na kara boye irin ta’addancin da sojoji suka yi a kisan kiyashin Disamban 2015.
Haka nan kuma lokacin da aka zaba don yin wannan ginin ya ba masu nazarin al’amuran yau da kullum mamaki, saboda an yi shi ne a lokacin da aka labarto cewa gwamnatin Tarayya na neman wasu hanyoyin lalama don warware matsaloli da rashin tabbas din da ci gaba da tsare Jagoranmu Shaikh Zakzaky yake jawowa a duk fadin duniya. Da alama kurayen da ke cikin gwamnatin nan suna yin wani sabon yunkuri don wargaza neman sulhun da ita gwamnatin ke yi kan kisan kiyashin Zariya da sojojinta suka yi. To, muna so mu tunatar da wadannan kurayen cewa, kamar yadda kudurin doka na Rome da suka kafa kotun manyan laifuka na ICC suka nuna, rusa wuraren ibadu kamar Husaniyya Bakiyyatullah ta Zariya yana daga cikin manyan laifukan yaki.
Muna so a sani a sarari cewa, mu ba za a tunzura mu ba ta kowace hanya. Za mu ci gaba da neman hakkokinmu da tsarin mulki ma ya tabbatar mana da su ta hanyar shari’a da kuma muzaharori na lumana, kamar yadda aka san mu da shi tun shekaru da dama da suka shude. Don haka muna kara jaddada bukatarmu na a saki Shugabanmu, Shaikh Zakzaky da matarsa da sauran ’yan uwa da suke tsare da gaggawa, kuma nan take.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA IMN
Skype: Ibrahim.musa42
22/07/17
RA'AYI RIGA: KOWA DA WACCE YAKE SO
Ni abin da yake bani mamaki da masu cewa Zabe ba ra'ayin Harka bane, cewa da suke yi Policy din Harka yana sauyawa amma Principle ba ya sauyawa. Masha Allah. Abin tambaya wanene yake da Hurumin da zai sauya Policy din. Kowane Dan uwan idan ya sha Fura ta ratsashi sai ya bugi Kirji ya ce Policy canzau? Ko kuwa Jagoranmu ne yake da Hakkin nuna mana cewa yanzu lokaci ya yi da za Mu sauya Policy. Masu cewa an je Court. Zuwa Court da Iznin su Malam aka je kuma tun kafin nan an je Kotu da dadewa. Kuma duk Matakan Free ZAKZAKY da ake dauka yanzu a baya an yi su ba wani Sabo. Ba kuma Wanda ya ci karo da Principles ko Policy din Harka shi ya sa ma ba wani Dan uwa da yake magana akan wani Mataki.
Wani abu da yake bani mamaki shi ne sai ace Ra'ayin Dan uwane ba na Harka ba. Sai kuma ace maka Policy zai sauya ko yana sauyawa da Lokaci. Idan ba rami me ya kawo batun Rami. An ce da Dila ga Hanya can ka bi ba Rami.
Tunda ra'ayin Yan Harka ne sai a daina batun Policy zai sauya ko ya sauya, don ba da yawun Harka ake yi ba, bai kuma shafi Principles ko Policy ba.
Don kuna Tuka da Warwara ne. Idan sha'anin Yan Uwa ne a daidaiku shi kenan kowa yana da ra'ayi, masu ra'ayin Zabe da tsayawa Takara duk su je su yi abin su. Amma su daina cewa Policy din Harka ya Sauya ko zai sauya. Wannan ne yake kawo rudani. Don suna cewa ne Wannan ra'ayin nasu shi ne Policy din Harka. Ba Cinya ba Kafar baya kenan. Idan Policy ya sauya za Mu ji ko gani daga su Sayyid Ibrahim Zakzaky ne. Kamar yadda Mu ka ga Ayatullahi Sidi Ali Khamna'i ya yi kiran Iraniyawa su fito Kwansu da Kwarkwata su jefa Kuri'an Gobe. Su fito su baiwa Makiya kunya.
Sai kuma masu cewa sha'anin Zabe Siyasa ce ba Addini ba. Sheikh ZAKZAKY Malamin addini ne ba na Siyasa ba. Don haka ba zai taba cewa Mu fito Mu yi Zabe ba, ya bar mana Zabi ne.
Tofah. Abin mamaki Wanda yake bin Sheikh Zakzaky ya fito yana Wannan Maganar. Domin abin da Sheikh yake kira Addinine. Ya kuma nuna mana cewa Siyasa da Mu'amalla da Ibada duk Addinin ne. Makiya ne suka raba mana addini daban Siyasa daban. Tarihin Musulunci ya nuna Banu Umayya ne suka fara raba addini da Siyasa.
Ni a fahimtata da Da'awar Sheikh Ibrahim Zakzaky shine Addini Mu Siyasarmu, Siyasarmu addininmu Yaushene ya zama akwai wani Sha'anin na rayuwar da Jagoranmu ba ruwansa Wannan kowa yana da Yanci ya yi abin da yake so. Yanzu wacce fassara za a baiwa Kiran da Ayatullahi Sidi Ali Khamna'i ya yiwa Iraniya? Irinsa kuma Imam Khomeini ya sha yi musu duk Kakar Zabe har ya bar Duniya. Ko su ba su fahimta bane?
A karshe ba ina Cewa ne kada ayi zabe ba. Abin da nake cewa shi ne. Masu amfani da wasu Kalmomi suna rikita Mutane su daina su fito kai tsaye kawai su ce za su zabe. Zabinsu ne ba mai hana su. Yan Kasa ne kamar kowa. Masu cewa abin da suka fahimta a baya daga Jawabin Jagoranmu Shekara da Shekaru ba su ji sabaninsa, ba ko ganin wani abu da ya yi karo da Matsayinsa. Wanda yake Sananne ga kowa Masoya da Makiya akan SIYASAR Najeriya da Yan SIYASAR da kuma Tsarin da ya Samar da su ya ba su Hurumi. A kyalesu da ra'ayinsu ba laifi suka yiwa kowa ba. Su ma Yan Kasa ne suna Hakkin su Zaba ko kada su Zaba.
Aji tausayin Yan uwa a daina amfani da wasu Kalmomi da suke rikitarwa. Don bai kamata akan ra'ayin da ba na Harkar ba a Samu rashin Jituwa a tsakaninmu.
Ibrahim Daurawa.
#Freezakzaky
#GodprotectZakzaky
DA A CE ZA MUYI KOYI DA IMAM ALIY (KW) AZZALUMAI ZASU JI ZA SU CIGABA
DA TSARE JAGORA?Markaz na ‘Yan uwa da ke Kano a yau Lahadi 3 ga Sha’aban 1438
(30/4/2017) ta sha kwalliya khatamar Maulidan Imam Aliy (KW) da aka
fara a wannan watan na Rajab da ya karada halkoki da zones da matasan
harka Islamiyya a Nigeria suka shirya a Da’irar Kano. A wannan
khatamar Frofesa Dahiru Yahya da Mal Badamasi Ya’aqub (kani ga Shaikh
Ibraheem Zakzaky (H) da Mal Sunusi AbdulKadir Koki suka kasance manya
baki masu jawabi.
Mal Bashir Dan Dago na daya daga cikin Shairai da suka kawata khatamar
da dadadan wakoki tare da su Mal Mustapha Limanci, Mal Uzairu Badamasi
da wasu daga cikin Shairai na harka Islamiyya mahalarta suna ta kuma
amsa baitoci tare da liki.
Mal Badamasi da Frofesa Dahiru Yahya sun gabatar da jawabai wanda a
cikin shi suna nunarsar da mahalarta irin tafarki da koyi da za a
gani daga rayuwar Imam Aliy (KW) suna masu nuni da wadanda sukayi koyi
da riko da shi wanda har yazo ga bayanin wanene Shaikh Zakzaky (H) a
wannan nahiyar mu. Jagora kuma Mujaddadi a wannan karnin da ke
nunarsar da al’umma a koma gare shi.
Mal Badamasi yayi kira ga matasa lallai su ga sunyi riko kyam da
tafarkin Allah (T) suna masu aiwatar da aiyuka da zai kusanta su ga
Shi. Sannan su kasance masu aiwatar da dukkanin aiyuka da ikhlasi da
nemar Yardan Sa tare da neman sabati a wannan tafarki.
Mal Sunusi a jawabin nasa ya karfafi ‘Yan uwa tare da ambaton yayin da
muke raya maulidan Imam Aliy (KW) zai fi kyau da tasiri a gare mu, mun
zama masu koyi da ababai da yanayin rayuwa na Imam Aliy (KW) ba kawai
mu zama masu ambato ba. Mal Sunusi ya tambayi mahalarta shin muna koyi
da Imam Aliy(KW) kuwa? Shin Imam Aliy (KW) zai ga azzalumai sun Kama
Jagora (SAWA) bada wani dalili kwakwara ba ya bari a killice shi daga
al’ummah?
Mal Badamasi Ya’aquob, Frofesa Dahiru Yahya da Dr Nura Azare a karshen
Khatamar maulidin sun mika wasu kyaututtuka a gasannin da aka gabatar
sassa daban daban a inda a karshe Halkan kofar Waika da Zone na Gwarzo
suka kasance zakaru, Zone na Naibawa da zone na Kura suka zamo na
biyu, yayin da Halkan Kurna da zone na Tudun Wada suka zamo na uku.
Bayan mika kyaututtuka, Mal Badamasi ya rufe khatamar da add
SABON MAKIRCI: TASHIN BOM DA SUNAN BOKO HARAM.
Idan Mutane suna bibiyar abubuwan da suka faru Mako biyu da ya shige zuwa wannan Makon za su ji kafafan yada Labarai sun ta kawo maganar tashin Boma-Bomai da suna Boko Haram a Maiduguri da wasu Gurare. Bom din yana tashi ne a wajeje daban daban kuma Mutane da yawa sun halaka wasu kuma sun ji Mummunan rauni, an yi asarar dukiya ta dubban Nairori.
Abin da zai fara zuwa tunanin Mutane ma su hankali shi ne ba an ce an gama da Boko Haram ba, yanzu an samu zaman lafiya har Mutane suna bacci da Minshari da saleba, batun Boko Haram ya zama Tarihi ba. Daga cikin abin da Masoya Buhari suke yiwa Mutane Gori shi ne. su ce 'Da tashin Bom gara tashin Dala' ma'ana duk Tsadar kayan masarufi da tsadar rayuwa da Gwamnatin Buhari ta kawo gara haka da Tashin Boma-boma da ake yi lokacin Jonathan. Yanzu Mutane sun samu kwanciyar hankali da zaman Lafiya don haka ko Kwanon Shinkafa zai kai Naira dubu daya ba Matsala bane. Masoya Buhari suna cewa Komai Allah ne ya kawoshi. Amma Buhari ne ya kawo zaman Lafiya da hana tashin Bom. Suna dorawa Allah laifin Komai da ya lalace, amma suna baiwa Buhari ladan kawo Zaman Lafiya.
Abin Lura a wannan sabowar Diramar shi ne Bara kamar haka an kawo harin Bom a Kasuwar yan Waya ta Farm Center a Kano, ana gaf da fara Tattaki. Sheikh Zakzaky a lokacin ya yi tsokaci cewa wannan Makirci ne mu ake shiryawa Makirci don a Kawo mana hari a ce Boko Haram ne. Hakan kuwa ya faru.
Bana ma idan kun tuna kwanaki an sake Tayar da Kurwar Shekau mai rayuka da yawa, a lokacin da ake Shirin fara Zaman Juyayin Ashura da yan uwa suka yi rubuce rubuce da Muzaharori cewa wannan Makirci ne ana so ne a kaiwa Sheikh Zakzaky hari da sunan Boko Haram. Dole wannan Shirin ya rushe sai aka dakko Yan Daba da Yan Sanda cikin Shigar Yan Daba suka dinga bin Yan Uwa suna sara da rana a tsaka.
Wannan ma dai irin na bara ne. An ce an kawo karshen Boko haram da tashin Boma-bomai har Amurka Buhari da Yaransa Buratai suka je aka ba su lambar Yabon kawo karshen Boko Haram. Kwatsam kuma sai ga Boko Haram sun dawo da wata Siga ta tada Boma-Bomai a cikin al'umma har da Sansanin yan gudun Hijira har ma da Sojoji a wadanda aka kashe da sunan Boko Haram.
Wannan ba wani abu bane face shirin shirya kwakwalen al'umma su amince cewa Boko haram da saka Bom a cikin al'umma ya dawo danye. Saboda a fake da wannan a saka mana Boma-bomai a Sahu da sansanin Tattaki da mu ke shirin yi.
Wannan 'Psychological Warfare' ne. Wato yaki da tunani ne, ana shirya tunanin al'umma ne don a samu saukin haifar da wani abu da ake son cimma, yadda mutane za su karbi duk abin da ya zo a matsayin kaddara ce daga Allah, kamar yadda ya faru da wasu Mutane a cikin wannan a'ummar.
Yana da kyau masu shirya wannan Diramar su fahimci cewa mu ba wawaye bane. Kamar yadda Shiekh Zakzaky ya fada bara ranar Yauma Arba'in cewa ba za a yaudare mu da wata aba wai BOKO HARAM ba. Ku je ku yaudari wasu amma ba mu Mabiya Imam Ali a.s. Wallahi duk abin da ya samemu mun san wadanda suka shirya shi.
Yanzu shawara ta rage taku kodai ku fito cikin Khaki ku farmana kamar yadda ku ka yi mana bara a Zariya, ko kuma ku saka Binjima ku dauki Adda da Gariyo kamar yadda ku ka yi mana a Muzaharar Ashura ko kuma ku fake da FILM din Boko Haram ku saka mana Bom ko ku daure Fuskokinku ku daga Tutar ISIS ku kawo mana hari da sunan mun ki Tuba kamar yadda ku shirya Fim dinku na 'SHEKAU YA DAWO' Duk daya ne a wajen mu mun san kone kum kuma kun san mun san kune.Mu da ku Kar-ta-san-Kar ne. A cikin biyu daya zai samemu kodai SHAHADA ko Kuma NASARA.Ku Kuma duk Matakin da ku ka dauka asara za ku yi, karshe kuma ku yi nadama.
Amma ba mu ba kaskanci har abada. HAIHATA MINNA ZILLAH
BUHARI YA BADA UMARIN BINCIKIN CIN ZAFARIN MATA A SANSANIN YAN GUDUN HIJIRA. KO YAUSHE ZA A BINCIKI WANDA SOJOJI SUKA YIWA MATA A ZARIYA.
BBC ta kawo rahotan cewa Buhari ya ba da Umarnin bincike da ladaftar da wadanda suke da hannu a cin Zarafi Yan Mata da Mayan Mata a sansanin Yan Gudun Hijira na Borno, sakamakon fitar da Rahotan Amnesty International da suka yi akan yadda wasu Jami'an Gwamnati da suke yi masu lura da raba abinci da kayan Masarufi a Sansanonin.
Shehu Garba Kakakin fadar Shugaban Kasa a kafafan yada Labarai ya fito yana cewa Ran Shugaban kasa ya baci sosai da ya ji wannan rahotan cin Zarafin kuma sun yi murna da wannan Rahota. Ya kuma yabawa wadanda suka yi wanna Binciken.
Amma abin da har yau ba mu ji ba shi ne matsayin Shugaban Kasa akan rahotan da Su Amnesty International suka yi akan Cin Zarafi da keta Hakkin Dan Adam da aikata lafukan Yaki da Sojojin Najeriya suka yi akan Yan Uwa Mata a ranakun 12 zuwa 14 December a Shekarar 2015. Bayan Amnesty, Islamic Human Right Watch da wasu Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi irin wannan Rahoto ya ma fi wanda aka yi yanzu akan Sansanin Yan gudun Hijira na Bornu irin yadda Sojoji suka keta hakkin Mata Yara da Manya har da Jarirai sannan suka kone wasu da ransu, Suke Binne wasu a rami daya ba Sallah Mata da Maza Yara da manya a hade cikin Tsakar dare a boye. Sannan kuma suka kame wasu suka tafi da su Barakokin Sojoji daban daban na kasar wanda yau babu Duriyarsu.
Bayan wadannan Rahotannin hatta kungiyar Jeka na yi ka ta JCI da Gwamnan Kaduna ya kafa sun bada Rahoton a hukunta wadana suka yi wannan Ta'asar a Zariya amma har yanzu Shiru ba wanda aka kama ko aka gaiyata don amsa tambayoyi akan Keta haddin dan Adam da suka yi.
Shin yan Kasa suna da Darajoji Mataki Mataki ne da wasu suna da Daraja ta daya wasu kuma yan Bora ne. kowa zai iya kashesu da konesu da rusa dukiyarsu ya zauna lafiya, amma wasu idan aka taba su zaka dandana Kudarka?
Za mu so mu ji Matsayin Shehu Sani dana Ubangidansa akan Wannan cin Zarafi da Aikata Laifukan Yaki a Zariya.
Mu dai abin da muka sani shi ne Rayukan Yan Najeriya na wani bai fi na wani Daraja ba, idan kuma an yi wata Sabuwar doka muna Son jin wane lokacin ne aka yi haka. Idan ba haka kuwa Shugaban Kasa shi ne ya bada Umarnin wannan Kisan don haka ma ya yi Biris da Kiyare Kiyaren da kungiyoyi da Kasashe suke na a hukunta wadanda suka yi wannan Aika-aikar.
Raddi ga Gwamna El-Rufai
Daga Free Zakzaky Campaign Committee
Biyo bayan karya doka da yin karan tsaye ga dokar kasa da ta bai wa kowane dan kasa daman yin addinin da ya zaba, da kuma yin cudanya da sauran jama’a da kuma haramta tsangwamar sa da Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya yi, inda ya haramta bin fahimtar addini irin na Shi’a da sunan cewa wai ya haramta Islamic Movement in Nigeria, wato IMN, an samu 'yan kanzagi, mayunwata, makaryata, masu yada fitina da suke yada kirkirarrun karairayi a kan ita IMN domin neman bata mata suna da tabbatar da maganar Gwamnan.
Wadannan karairayi dai an yi su ne da niyyar tabbatar da dalilan da shi Gwamna El-Rufai ya bayar a matsayin hujjojinsa na haramta yin Shi’a da sunan wai ya haramta IMN.
Da farko dai, gwamna el-rufai, yace wai ya aiwatar da wannan haramci ne biyo bayan shawarwari da wata hukumar binciken arangamar da sojojin Nigeria suka kai wa ita harka Islamiyya wato Judicial Commission of Inquiry JCI, a watan disamba na 2015 inda sojojin suka kashe sama da mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky dubu daya, wanda daga bisani bayan sun karyata kisan, suka dawo suka amince da cewa sun kashe mutane dari uku da arba’in da bakwai ne kawai, kuma sun bizne su a boye cikin dare a kusa da makabartar da ke unguwan Mando a garin Kaduna ba bisa ka’ida ba, domin boye kisan gillan da suka yi.
Wasu ma daga cikin wadanda suka bizne, sun bizne su ne da rai bayan raunukan da suka samu na harbin da aka yi musu. Har ya zuwa yanzu dai ba su fadi yadda suka yi da sauran wadanda suka kashen ba.
Gwamnan ya ce ya bi shawarwari ne da hukumar binciken na JCI ta fitar, wanda daga ciki akwai cewa wai kungiyar IMN ba ta da rijista, saboda haka ta haramta.
To amsa a nan shi ne cewa ita IMN ba kungiya ba ce bare ta yi rijista. Harka ce ta addini, inda jama’a ke neman dabbaka addinin Musulunci kamar yadda Musulunci ya tanada. Duk abin da ake yi kama daga salla, azumi, zakka, hajji, Mauludi, zaman ashura da tattaki duka addini ne. Shi IMN alami ne na masu yin wannan addini.
Kasantuwar cewa ba kungiya ba ce ya sa ba ta da duk wasu mukamai da kungiya ke bukata kamar su Shugaban kungiya, Sakatare, Ma’aji, Kakaki, da dai sauransu. Haka kuma ba ta da wani tambarin kungiya ko tsari na rijistar shiga kungiya. A takaice dai ba kungiya ba ce. Kuma ma ai babu wata doka da ta ce don za ka aikata addini, sai an yi maka rijista.
Bilhasali ma akwai bangarori na Harka Islamiyya da ke da rijista da gwamnati domin akwai bukatar haka. Akwai Mu’assasatul Shuhada da ke kula da iyalai da yaran shahidai. Akwai Mizani Publication da ke buga jaridar Al-mizan da Pointer Express. Akwai Islamic Medical Association ISMA, da ke ba da taimakon farko ga mabukata. Akwai Zahra Foundation da ke kula da masu rauni, kuma akwai Fudiyya Islamic schools da ke kula da makarantun Harka Islamiyya da sauransu. Duka kuma wadannan bangarori na da takardun biyan haraji da ake yi kowace shekara. Ashe kenan ka ga ba a yi wa IMN rijista ba ne saboda ba kungiya ba ce kuma ba ta bukatar rijista.
Sai kuma zargin da Gwamna El-Rufai ya ce wai IMN na tare hanyoyi, mallake makarantu da kuma kwace masallatai. Ya kuma ce IMN na tauye wa sauran mutane hakkin amfana da wadannan hanyoyi.
Duk wanda ya san 'yan Harka Islamiyya ya san karya ne a ce suna kwace masallaci, domin kuwa suna salla ne tare da sauran Musulmi a kowane masallaci. Sabanin akidar wahabiyanci irin na Izala da ba sa bin kowa salla sai dan Izala, kuma ba sa salla a kowane masallaci, sai na 'yan Izala. IMN ta dauka cewa duk wanda ya ce La’ilaha illallah musulmi ne kuma ana bin sa sallah. Babu wani masallaci guda da wani zai iya fitowa ya ce 'yan Harka Islamiyya sun kwace a kasar nan gabaki daya, haka ma makaranta.
Maganar tare hanya, a nan sai a tambaye shi ko da akwai wani Gwamna ko Shugaban kasa da ya taba cin zabe, ko ya fadi da bai tare wa jama’a hanya ba?
Shi tare hanya kowa ne yake yi, ba 'yan Shia kawai ba. Musulmi na tare hanyoyi kowace ranar Juma’a, kiristoci ma na tare hanyoyi kowace ranar Lahadi ko lokutan wasu manasibobinsu, Sarakuna na tare hanyoyi wurin hawan kowane salla, mutanen gari na tare hanyoyi wurin buki daban-daban da suke yi da sauran su.
Me ya sa sai 'yan Shia ne kawai aka ga nasu ba a ga na saura ba? Da adalci zai yi, ai sai ya haramta dukkanin kungiyyoyin siyasa da masallatai da coci-coci da masarautu da ma sauran jama’a saboda tare hanya. Amma sai ya zabi 'yan Shi’a kawai domin cimma manufarsa da na Wahabiyawa 'yan uwansa.
Ya kuma kawo zargin cewa wai IMN na gudanar da gwamnati, wai tana da Gwamna a kowace jiha da kuma runduna.
Sai dai bai kawo hujjarsa na fadin haka ba. Su dai 'yan Harka Islamiyya 'yan Nigeria ne. Kuma wannan ne ma ya sa ake ce musu Islamic Movement in Nigeria domin 'yan Nigeria ne ke wannan Harkar. Suna dauke da katin shaidar zama 'yan kasa da fasfo na Nigeria ba na wata kasa ba. Ba su kuma ayyana wani yanki na kasa suka ce wai nasu kasar ba ne. Sa’ilin nan kuma suna amfani da kudin kasar ne. Kuma a duk lokacin da aka zalunce su suna zuwa gaban kotun kasar ne don neman hakki kamar dai yadda suka yi a wannan zaluncin da aka yi musu na wannan kisan gillan da sojoji suka yi a Zaria.
Yanzu hankali bai ba da cewa duk inda jama’a masu fahmta guda suka taru dole ne a ce suna da wakili ba? Harka ce ta jama’a da ake da su a kowane sashe na kasa, saboda haka dole ne suna da wakilci da tsarinsu na gudanar da addini. Ka ga kenan wakilin da suke da shi ko a unguwa ko a Karamar hukuma ko a jiha bai zama wani Gwamna ko Shugaba ba. Haka kuma babu wata kungiya ko wasu taron jama’a da ba su da irin wannan wakilci a jihohhi ko garuruwa. Me ya sa sai na IMN ne kawai Gwamnan ya hango?
Zargin cewa ana da runduna wani sharri ne na neman razana jama’a da neman a kyamaci Harka Islamiyya. Idan IMN tana da harisawa da ke kula da tarurrukanta da tabbatar da cewa komai ya tafi cikin tsari, haka ma kungiyoyi da dama suna da wadannan masu ba da taimakon. Kungiyar Izala na da 'yan agaji kuma suna fareti, kuma suna ma daukar katako mai siffan bindiga wurin faretinsu wanda harisawan IMN ba sa dauka, sa’ilin nan kuma su ma suna rawar daji.
Akwai bangaren 'yan Fitiyanu a karkashin 'yan Darika, akwai 'yan Jama’atu. Haka kuma a kiristoci akwai 'yan Boys brigade, akwai 'yan Girls guide, kuma dukkansu kowanne na fareti da ma rawan daji. Amma da yake gwamnati na da mugun nufi a kan 'yan Shia, sai harisawan Harka Islamiyya kawai ne idanunsu suka iya hangowa don cimma wani muradi nasa.
Akwai kuma zargin cewa IMN wai ba ta girmama hukuma, kuma wai ta addabi al’umma, tana ta da hankalinsu. Wannan ita ma karya ce karara aka kirkira, domin kuwa a lokuta da dama gwamnatoci da suka gabata sun gayyaci yan uwa zuwa warin zama a gidan gwamnati, inda wakilan harka suka halarta.
Ko a bayan harin da sojoji suka kawo wa Harka Islamiyya, Majalisar kasa ta gayyaci Harka kuma wakilanta sun je. Nigerian Bar Association NBA ta gayyaci Harka ta je. Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa, NHC, ta gayyaci Harka kuma ta je. Kai har wasu bangarorin gwamnati ma sun sha bai wa Harka Islamiyya lambar yabo, kamar misali gwamnatin jihar Kaduna da ta bai wa Harka Islamiyya lambar yabo ta hanyar ayyana Shaikh Ibraheem Zakzaky a matsayin Jakadan zaman lafiya, wato Ambassador of peace a zamanin Gwamna Jafaru Isa, da kuma hukumar da ke kula da samar da jini na kasa, wato National Blood Transfussion Services NBTS da ta baiwa Harka takardar yabo na zama jama’an da suka fi kowa ba da gudummawar jini a kasa.
A lokaci guda kuma shi Gwamna El-rufai da yake wannan zargi, ba zai iya ambatar wani lokaci guda daya da ya gayyaci Harka Islamiyya ta ki zuwa ba. Saboda haka wannan wani shaci- fadi ne.
Zan rufe wannan bayani da cewa zargin kin zuwa gaban hukumar binciken da Gwamna El-rufai ya kafa na JCI a matsayin hujjan yi wa hukuma karan tsaye rusasshe ne saboda wadannan bayanai da ya ce hukumar ce ta gano, sune zargin da ya ambata a kan Harka Islamiyya tun lokacin da zai kafa hukumar.
Sa’ilin nan kuma yanzu kowa hankalinsa alkalinsa, shin haramta IMN ne kawai hukumar JCI ta ba da shawarar a yi? Ina maganar hukumta sojojin da suka yi kisan gilla a Zariya da hukumar ta ba da shawarar a yi? Ya ba a kama su an hukumta su ba? Wannan ya ishi amsar dalilin da yasa ba mu hallara gaban hukumar JCI ba. Allah ya sa mu dace
YAN TATTAKIN BUHARI DA YAN TATTAKIN IMAM HUSAIN a.s
Hotuna biyu na farko Hotunan Mutanen da suka yi tattaki ne daga waje daban daban don taya Buhari Murnar cin Zabe na farko ya tako a kasa tun daga Lagos har zuwa Abuja a Kasa Tattaki mafi tsaho da aka taba yi a kasar ko don saboda menene kenan.
Wannan Mutum lokacin Tattakinsa, Mutane sun dinga tururuwar tarbarsa suna yi masa kyauta suna rakashi. Suna daukar Hoto da shi don samun tabarraki. Haka daya Matar duk Macece kuma ita kadai ba wanda ya bata shawarar ko za a iya yi mata fyade ko fashi ko duka biyun koma saceta. Duk garin da suka je suna zama Kanun Labarai a wannan garin yan garin kuma suna alfahari da tsayarwa da suka yi a garinsu. BBC har lokaci suka warewa Mutumin da ya taso daga Lagos zuwa Abuja, haka da ya kammala sun yi shira da shi ta musamman.
Buhari ya ji dadin wannan Tattaki da aka yi masa ya kuma fito da magoya bayansa ya karramasu da kyautuka da yin hotuna.
Babu wani Mutun ko wani Jami'in tsaro da ya yi musu barazana da rayukansu ko barazanar kamu ko Kisa ko kai musu hari, sai ma kambamasu da aka yi da karramawa.
Wani abin Mamaki kuma shi ne hotuna biyu na masu Tattaki ne saboda Juyayin abin da Makiya Manzon Allah suka yiwa zuriyar Manzon Allah don jajantawa Manzon Allah da dandana irin bakar Azabar da suka sha. Kamar yadda sauran ragowar Iyalan Imam Husain da su Sayyada Zainab a.s Kanwarsa da kuma Sahabin Manzon Allah Jabir an Ansari suka fara yin wannan Tattakin. Wadannan Mutanen sun fito ba su yiwa kowa laifin komai ba, ba su zagi wani ba ba su saci kayan kowa ba. Aka samu wasu suka shiga cikinsu suka tayar da Bom ya kashe Mutane da yawa nan take wasu kuma bayan nan suka yi Shahada.
Babban abin mamakin shi ne yadda bana Muhammad Buhari da Jami'an tsaronsa wadanda hakkinsu sune su baiwa Wadannan masu Tattakin Kariya da taimako kamar yadda ake a wasu Kasashe har su kammala lafiya, sai ga shi kamar yadda Malam Yakubu Yahaya ya fallasa shirin Abkawa masu Tattakin, wadanda tsarin Mulki ya baiwa alhakin karewa da Mutunta rayuka, Dukiya da Mutuncin yan Kasa sun yi shirin abkawa masu yin Tattakin don koyi da Sahabban Manzon Allah da Jajantawa Manzon Allah da Iyalinsa akan Kisar kare dangi da Yazidu ya yiwa zuriyar Manzon Allah.
Abin tambaya wai shin yin tattakin Laifi ne Buhari aka yi masa har ya fito ya yi tarba da karramawa wadanda suka yi masa? Amma kuma yanzu yake daukan matakan hana yin Tattaki saboda Manzon Allah. Yana da kyau Gwamnati ta fito ta baiyanawa Mutane cewa yin tattaki ya saba da Tsarin Mulkin Kasar nan, Ko kuma wane irin tattaki ne ya Halasta ga yan Kasa su yi. Ko na wani Mutum ne ya halasta amma na Iyalan Manzon Allah ya haramta? domin ba Buhari kawai ne aka yiwa Tattaki ba Gwamna Nasuru El Rufa'i ya yi Tattaki a Zariya, sannan Tsohon Gwamnan Kaduna ya yi Muzahara bakin cikin faduwarsa Zabe. Kwanakin baya a Kano Gwamna Umar Ganduje ya yi Tattaki lokacin da ya zo ya duba wani Titi da ya yi a Maiduguri Road ya yi irinsa kuma a unguwar Dakata zuwa Zangwon Dakata.
Shin tattaki da sunan Addini ne yake Haram kuma hukuncinsa shi ne aka kashe duk wadanda suke yi kisan Kiyashi har sai an karar da Miliyan 17 sauran Miliyan Uku a garkamesu a Kurkuku a kone Gidajensu da Masa'antunsu da Makarantunsa da cibiyoyinsu. Amma kowa yana da Ikon ya yi Tattaki akan duk wani Kato har a bashi Kyauta, duk lokacin da Mutum ya bushi Iska yana iya yin Tattaki akan komai idai ba akan Addini bane? Wannan wacce Irin Dokace, kuma yaushe aka yita a Kasar nan?
Abin Mamaki masu cewa sun haramta Tattaki saboda tuna Azabar da aka yiwa Iyalan Manzon Allah Musulmi ne kuma duk cikarsu ba wanda bai yi amfani da Manzon Allah ba kafin ya samu darewa akan Kujarar da yake kai. Wadannan Mutane da suke cin albarkar Manzon Allah da 'Ya'yansa sune suke cewa ba za ayi ambaton gidan Manzon Allah ba. Amma su ana iya yin ambatunsu har su sakawa Mutum da Kyautuka. Abin da ya fi komai Muni shi ne a cikin Kasar da mafiya Yawanta Musulmi ne masu tunkaho da Manzon Allah, amma sun kasa cewa wannan abin da wasu tsiraru suke yi cin Mutuncine ga Manzon Allah da Iyalansa da Musulunci gabakidaya sun gum da bakinsu, wasu ma sun Zako lokacin ya yi akar da masu cewa LABBAIKA YA HUSAIN!!!!
TA’ADDANCIN SOJOJIN NIJERIYA A ZARIYA:
Allah kadai ya San adadin da aka raunata.
Daga Ammar Muhammad Rajab
Da safiyar ranar wata Asabar, 27 ga watan Agustan, 2016, cibiyar dake fafutikar ganin an saki jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da wani taro domin tantance adadin wadanda aka raunta a lokacin kashe-kashen da Sojoji suka yi a Zariya tare da tallafa musu da kuma wadanda aka kashe musu mazaje, ‘ya’ya da iyalai. Taron ya gudana ne a muhallin makarantar Fudiyya dake Zariya. Kuma ya samu halartar mabiya harkar daga sassa daban-daban na kasarnan.
Malam Abdurrahman Yola, shi ne jagoran cibiyar dake fafutikar ganin an saki jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana makasudin wannan taron, inda ya bayyana cewa; an shirya taron ne domin tantance adadin wadanda aka raunata a lokacin da Sojojin suka aukawa ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky a ranekun 12 zuwa 14 ga watan Disamban, 2015. Sannan ya tabbatar da cewa; daga cikin mahalarta taron harda mata da kananan Yara wadanda yake suna daga cikin iyalan mutane dubu da har yanzu ba a gansu ba, wanda ya zama wasu an kashe su, wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba. Sannan ya ce; “wa su ba su ga mazajensu ba, wasu kuma mazajensu an kashe su, wasu kuma suna wadansu muhallai wadanda yake ma bamu san a ina suke ba. A don haka yasa muka taru a wannan muhalli domin mu jajanta musu akan yau kimanin kusan wata tara ke nan aka raba su da mazajensu, ba su san inda suke ba. Wasu da aka raba su da mazajensu, an bizne su ne ba tare da yardar iyalansu ba, wanda har yanzu suna fatan ganin kan cewa an dawo musu da gawarwakin mazajensu, ‘ya’yansu da ‘yan uwansu domin su yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.” Inji shi.
Dangane da yadda suke tallafawa iyalai da matan da wannan abu ya shafa kuwa, ya tabbatar da cewa; tun farkon lokacin da jami’an tsaron Nijeriya suka fara aukawa Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky aka samar da wata gidauniya ta musamman wacce take kula da wannan fannin, ya ce’ “kuma daidai gwargwado tana bakin kokarinta wajen ganin ta inganta bangaren dukkan rayuwarsu da ya shafi karatunsu da na ‘ya’yansu.” Sannan ya tabbatar da cewa; wannan gidauniya an kafa ta ne sama da shekara goma sha. Sannan ya nusasshe da hanyar da suke bi wajen tallafawa wadanda abin ya sha, ya ce; hanyar da suke bi wajen tallafawa iyalan wadanda aka rasa akan wannan hanyar shi ne; tallafin da ake samu daga bangaren su ’yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky. Ya ce; “wannan kula kuma ya hada; ‘ya’ya, Iyalai, Mata da Iyayen wanda duk wanda aka kashe ya bari.”
Dangane da wadanda suka ji raunuka kuwa, ya tabbatar da cewa; “muna da daruruwa ne, wadanda suka kwanta a asibiti, aka yi musu jinya akalla sun kusan dari, akwai wadanda ya zama an sallame su, wannna ma yasa ya zamo muka kira wannan taron da sunan taron tantance wadanda aka raunata, sanin adadin wadanda suka samu raunuka da kuma tsananin raunin na su, don sanin wadanda suke bukatar kulawa na musamman domin kaisu inda ya kamata su samu lafiya. Wannan na daga cikin dalilan wanann taron.” Har wala yau ya kara da cewa; sanin raunukan kowanne ne zai sa su san agaji da tallafin da ya kamata su bashi. Ya ce; a taron akwai Likitoci da za su duba marasa lafiyar da nazartar raunukansu domin su sa su shawarwari. Dangane da lafiyar Malam Zakzaky kuwa, ya tabbatar da cewa; a halin yanzu Malam Zakzaky na bukatar ganin likitansa, saboda yadda ya rasa idonsa daya kuma dayanma a halin yanzu ya fara rasa shi shima. Ya ce; “tunda har likitocin da jami’an leken asiri na farin kaya na DSS suka kawo domin duba lafiyar Malam sun tabbatar da cewa; sun yi iya na su ba za su iya ba, ya kamata a basu Malam Zakzaky domin su kaishi inda za a duba lafiyarsa.”
Shi ko Malam Abdulkareem Usamatu, shi ne jagoran likitocin Harkar, wanda yake kula da wadanda aka jikkata shima ya tabbatar da cewa; wadanda suke da su a rubuce akalla suna da sama da mutum tamanin da takwas (88) da suka ji raunuka, ya ce; wadannan adadin har yanzu suna karbar kulawa a asibitoci daban-daban na kasarnan. Sannan ya nusasshe da cewa; wannan adadin banda wadanda suka warke zuwa yanzu. Sai dai ya ce; wasu da yawa sun warke wadanda suka ji raunuka, sai dai mutane 88 din nan ne suka kai ga tantancewa wanda suke asibiti a halin yanzu. Sannan ya yi nuni da cewa; “wasu ma saboda raunukansu baza su iya zuwa taron ba. Sannan wasu ma har ya zuwa yau ba a iya cire harsasan dake jikinsu ba. A halin yanzu wadanda suke kwance mutum 88 ne, wasu an musu aiki, wasu kuma har yanzu ba a kai ga cire musu harsasan jikinsu ba.” Inji Dakta Usamatu.
A karshe ya tabbatar da cewa; wadanda suka nakasa suma ana yi musu tanadi na musamman wajen rage musu radadi. Sannan Iyalai mata da aka kashe musu mazaje, cibiyar dake kula da wannan bangare na Harkar Musulunci, duka tana kula da iliminsu, kula da su, da abin da ya shafi haihuwa da dukkan al’amuran rayuwarsu daidai gwargwado ana yi musu. Sannan ya nusasshe da cewa; ya zuwa yanzu tun bayan kashe-kashen da aka yi, wadanda aka kashewa mazaje, sun haifi akalla jarirai sama da 100. Kuma wannan gidauniya ita take daukar dawainiyyarsu, a gefe guda kuma ‘yan uwa ke daukar dawainiyyar wannan gidauniya.
A lokacin taron, Shaikh Abdulhamid Bello ne ya gabatar da jawabin rufewa, a inda ya karfafa Shahidai masu rai, da Iyalan Shahidai akan su tsaya kyam akan tafarkin Allah. Ya jajantawa Iyalan cikin kuka na rashin cancantarsa ya tsaya a gabansu yana musu bayani. Inda ya bayyana cewa; sun samu wata babban daraja ta musamman. Sannan ya bayyana Shahidai a matsayin wadanda suka tsaya kyam har suka cimma nasara. Har wala yau Shehin Malamin ya ce; duk wanda Allah ya yi masa ni'imar shiriya, ya godewa Allah. Saboda ni'imar shiriya Allah ta'ala ke bayarwa ga wanda ya so. Sannan idan Allah ya baka wannan ni'ima, to akwai gwaji daga Allah, wannan gwajin ne zai sa ka san cewa; kana kan hanyarnan ta shiriya. Ya ba da misali da Annabawa da sauran bayin Allah na yadda Allah ta’ala ke jarabtarsu. Sannan ya nusasshe da mahalarta taron akan cewa; mu da muka rage, akwai Jan aiki a gabanmu na dakewa da tsayawa kyam akan wannan tafarki. Ya ba da misali da Suratul Hud, Wanda Manzon Allah ya ce; Surar sai da ta saka shi furfura saboda yadda Allah ta'ala ya nusasshe shi akan ya tsaya kyam.
A wani bangare na jawabinsa, ya nusasshe da cewa; dukkan wata jarabawa matakin cinyeta shi ne hakuri. Ya kawo ayoyin Allah ta'ala domin tabbatar da bayaninsa. Sannan ya ce; dukkan masu hakuri da wannan gwaji din, bushararsu tun daga duniya za su fara ganin sakamako, hakazalika za su ga sakamako mai kyau a lahira. Sannan ya karfafi 'yan uwa akan kyautata tsakaninmu da Allah, dagewa da ibada. Sannan kuma da inganta 'yan uwantaka a tsakanin 'yan uwa da kyautata kowa zato. Ya jaddada cewa; matakin nasara shi ne; soyayyar 'yan uwantaka ta inganta a tsakanin 'yan uwa, kuma saboda Allah. "Mu kaunaci junanmu saboda Allah, sai Allah ya taimakemu, mu kiyaye hakkin 'yan uwantaka tsakaninmu. Mafi karancin soyayya ga 'yan uwa, shi ne; ka sowa dan uwanka abin da kake sowa kanka. Idan ma zaka iya ka so danuwanka fiye da kanka." Inji Malamin. Sannan ya karfafi ‘yan uwa akan muhimmancin kyautata alaka tsakaninsu da sauran al’umma domin guduwa tare a kuma tsira tare. Ya ce; Manzon Allah Rahama ne ga dukkan talikai, mu yiwa al’umma da’awa da kyawawan dabi’u.
MADALLA DA WANNAN RUBUTUN!
Mai wannan rubutu wanda ya ambaci kan sa da Abdulsalam Kusfa ya yi wannan rubutun ne tun a watan December, 2015. Amma ranar 19 ga wannan watan na October, 2016 ya sake wallafa shi a shafinsa na facebook. Ganin muhimmancin rubutun ya sa ni ma na kofo shi a yadda yake.
Wannan rubutu nawa zan yi shi ne domin jajantawa da nuna rashin amincewa na da ta’addancin da sojojin Nijeriya su ka yi ma yan shi’a wannan garin na mu na Zariya, duk da muna da sabanin fahimta da yan shi’a amma dai su musulmai ne yan uwanmu, sannan abinda a kayi musu ko wanda ba musulmi ba akai ma ya kamata al’umma ta fito ta nuna jujayinta da kuma rashin nuna goyon bayan hakan. Domin akwai abinda ake kira ihsaniyya a larabce shine kiyaye muruwan dan Adam da kuma darajan ransa, don haka ne ma aka tanadi hukuma domin ta kare rayuka da mutuncin al’ummun da ke karkashinta, amma abun mamaki sai gashi mun wayi gari a cikin zariya, jami’an tsaron da aka ce an tanade su domin kare rayukan al’umma sun dauki yini biyu car a bainar jama’a ba abinda suke in banda kashe talakawan da basu da makamai a hannunsu, bayan sun gama kashe dubbabnnin rayuwakan wadannan bayin Allah, wanda ya hada da mata da yara kanana duk wannan bai musu ba suka kama jagoransu bayan sun kashe yayan shi guda uku shima sun harbe shi da bindiga sannan sun harbi uwar gidansa itama da bindiga duk da haka bai musu ba sun tafi dashi wai suna son su gurfanar dashi a kotu. Wannan abune wanda ya sabawa dukkanin dokoki na duniya, sannan dadin da-dawa wani abin bakin ciki da takaici zababben gwamna a jihar Kaduna wanda mu talakawa na jihar Kaduna muka zabe shi a matsayin gwamnanmu sakamakon muna masa tsammanin tausayi da imani da kuma kishin kasa a tare dashi wannan mutum mai suna Mallam Nasir El-Rufa’e sai gashi ya fito a kafafen yada labarai duniya tana jinshi yana goyon bayan wannan ta’asa da sojojin Nijeriya sukayi a Zariya sai kuma gashi shi ma ya dira a kan gine-ginensu yana rusawa. Ya rusa gurin da suke kira Hussainiyya, sannan ya rusa gidan Al-Zakzaky duk da sojoji sun jejjefa bama bamai a gidan Al-Zakzakyn sun rurrusa wani bangaren amma El-Rufa’e bai kyale ba sai da ya karisa rusa ragowan ginin gidan wannan bai mai ba ya kara tafiya can gininsu wanda yake kan hanyar Soba nan ma ya rusa kai Nasiru El-Rufa’e hatta kabari bai kyale ba sai da yasa aka tottone da masallacin su da yake gurin shima Nasiru El-Rufa’e yasa an rusa shi kai hatta kabarin yayan Al-Zakzaky da suke gurin wanda aka kashe bara sai da El-Rufa’e yasa aka tone, kai har makarantansu da take dan magaji itama yasa an rusata, El-Rufa’e bai tsaya nan ba ya tafi har kabarin mahaifiyar El-Zakzaky wanda aka gina mata hubbare yasa aka rusa, wani Karin abin mamaki Nasiru El-Rufa’e bai tsaya nan ba har kabarin kakan El-Zakzaky wanda yake a garin likoro dake kan hanyar Kano sai da yasa akaje aka rusa shi, duk day ace gine-ginen ba akan ka’ida aka yishi ba kuma basu da takardu, amma wannan dalilin nashi ya sabama ka’idar hankali wani Karin abin mamaki da bakin ciki da takaici shine wai duk wannan kashe-kashen rayukan na wuni biyu da sojoji sukayi da kuma wannan rushe-rushen da akayi wai dalili saboda yan shi’a sun tare ma shugaban sojoji hanya sun hana shi wucewa. Lallai wannan jahilcine da kuma zubar da mutuncin kasarmu ta Nijeriya. Babu wata doka ko shugaban mahaukata ne ya rubuta dokar da tace hukuncin al’ummar da ta tare shugabannin sojoji shine kashe ta, ballantana a kashe daruruwa har ma da yara kanana wanda basu balaga ba da mata da kuma rusa musu wuraren ibadunsu da cibiyoyin su, kuma gaskiyar Magana shine ba wata al’umma da za ta iya tare shugaban sojoji tace mai ba zai wuce ba hankali ba zai dau wannan ba, dole sai da wani dalili domin na kalli video da rundunar sojoji suka sake na saurare shi kuma da idon basira, wannan hotone wanda inka tsaya ka kalle shi ne da iya kyayar idonka ba tare da kasa kwakwalwa ka zurfafa tunani ba to za ka ji haushin ‘yan shi’a, amma inka tsaya ka saurari magan-ganun mutanen da suke Magana da yawun yan shi’a, mutanen kala biyu ne akwai wadanda suke baya suna kabbara sannan akwai wadanda suka zo suna Magana dasu jagororin sojojin, kamar yanda ake cewa su wadannan suna dukan kirjin manyan sojojin suna tare su ba haka bane, idan ka kalli abin da kyau zaka ga suna Magana da sojojin Magana irin na hankali ba maganan fada bane, zaka fahimci kafin su wadannan manyan sojojin suzo akwai abinda ya faru awurin kuma mu mutanen zariya shaida ne wannan gurin sojoji sun taba zuwa suka bude musu wuta a bara sannan idan ka kalli hoton bidiyon da idon basira zaka fahimci anyi Editin din shine akwai abubuwan da aka daddatse a ciki, sannan alamane yake nufi kafin su buda ma kansu hanya din akwai abinda sukayi wanda basa son duniya ta gani. Babban abinda nake so na fitar anan dukkanin hasashe na masu ilimi da bincike ba wawaye ba daga cikin mutane, sun tabbatar da cewa kafin yan shi’a su tare hanya akwai abinda sojoji sukayi musu dalili kuwa shine asali wannan taron na sun ba taron da suke kashe hanya bane, domin taro ne wanda sukeyin shi a cikin hussainiyyar su, sannan mafi yawa in suna tarurruka sojoji na kai wa da kawowa a wannan hanya meyasa a baya basu taba tare soja su kace ba zai wuce ba, sannan kamar yanda naji shi El-Rufa’e yana cewa sunayin tattaki suna kashe hanya wannan ma laifi ne daya saba dokokin kasa, Mallam Nasir El-Rufa’e kai ma tattakin nan yana daga cikin tsare-tsaren ka na manufar siyasa, in tattaki laifi ne to kaima ya kamata akamaka a kakkashe iyalinka da mabiyanka tunda hakan agunka shine hukuncin mai tattaki ya tare hanya domin kuwa a Zariya rana tsaka duk mutanen zariya sun sani kayi tattaki da kafar ka da kai da mabiyanka nima ina daga cikin wadanda mukayi tattaki tare da kai tunda daga filin folo wanda yake kusa da hussainiyya din har cikin garin Zariya da kafafunmu kuma kaima da kafarka kuma duk mutanen garin zariya sun san wannan. Maganan gaskiya anan duk da zakaji magan-ganu daban-daban daga bakin mutane da sabanin ra’ayi akwai wadanda suke karkata akan yan shi’a suke da laifi sukai kaza sukai kaza ko basu bin doka oda ko yan tada zaune tsaye ne, abinda nake so nace anan shine a ajiye batun maganan akida gefe da duk wani son rai ni ba dan shi’a bane kuma inada sabani da akidar shi’a amma maganan gaskiya itace, jagoran yan shi’a Sheikh Zakzaky wallahi mutum ne wanda yake kokari wajen tabbatar da hadin kai a tsakanin musulmi, saboda shine Malamin da yake kiran dukkanin Musulmai suna zuwa suna zama a Hussainiyyar su domin tabbatar da hadinkai, sannan shine malamin da almajiransa suke bin dukkanin malamai na kowane bangare suna kai musu ziyara kai bai tsaya nanba har coci yana tura dalibansa suje su kaima kiristoci ziyara don tabbatar da zaman lafiya a kasa, kai muda ba yan shi’a bama har zagin su mukeyi muna cewa suda kiristoci dayane, saboda ma’amalan da sukeyi da kiristoci, anan Zariya ansha a farma kristoci a sassare su da adduna a ji musu rauni amma Zakzaky shi yakesa almajiransa suna debosu suna kawo su gidansa ana basu abinci ana musu magani, kai akwai lokacin da aka farma kristoci a Zariya suna ta guduwa barikin soja, Zakzaky shine yasa almajiransa suna dafa abinci suna kaima kiristoci gun gudun hijirar su dake barikin soja.
ABIN DA YA SA AKA YI MANA DIRAR MIKIYA.
Babban abin da ya sa Azzalumai suke afka mana ta kowane Janibi Abubuwa guda biyu ne.
Na farko shi ne Shirin Kashe Zakzaky da rusa harka wanda bai yi nasara ba a bara. Sun gama tsarinsu tsaf sun dauka wannan kisan Kiyashin da suka yi sun gama da harka kenan har abada, sai wanki hula ya kai su dare.
Maimakon Harka ta Mutu sai wannan ya zama shi ne sanadin da ta yi tashin gwauron Zabi, duk duniya aka santa da Manufofinta. Maimakon a Kashe Zakzaky sai suka maida shi abin da ake cewa 'Immortal' Wato Shaharran da ba za a manta da shi ba a tarihi. Duk kokarin da suka yi na su Muzanta Harka da Sheikh Zakzaky sai ya zama suna jawo masa farin Jini da tausayawa a fadin Duniya a tsakanin Mutane masu banbancin Addini da fahimta da ra'ayi. Sai ya zama abin yana damunsu. Sun kawo dalilai sun dawo da kansu sun karyata kansu. Sun lura Mutane masu hankali suna yi musu darayi suna daukansu wasu Wawaye marasa hankali da sanin Mutuncin kansu. Ba su da wata Hujja ta ci gaba da rike shi tunda sun ce ba laifi ya yi ba suke tsare da shi.
Abi na biyu da yake damunsu shine Muzaharar Free Zakzaky tana damunsu mutuka, amma ba su da hujjar hanawa kuma Muzaharar tana nuna ba Dimokaradiyya suke ba, kuma ba su san kimar tsarin Mulkin da suke Tutiyar karewa ba. Muzaharar tana kara tallata Harka kuma tana Muzanta su. Tana nuna suna keta Dokar Kasarsu. Amma babu yadda za su yi su hana, idan sun fito fili sun ce sun hana muzaharar Free Zakzaky za a ce kun yi Zalunci domin Tsarin Mulki ya ba su dama kuma ba su keta doka ba. A baya sun ta kokari kawo hautsini a Muzahara don su fake da wannan su hana yi. Amma ba su yi nasara ba, sun fara daukar Hayar Mutane suna biyansu suka ga ba za su iya ba su Kudin ba. Su kuma Mutane dama gaiyato aka yi don a biya don haka suka kama gabansu.
A hankali Muzaharar tun anayi a Birane da Kauyuka har ta fara zuwa Abuja. Sannan tun ana yi a Gari gari kowa ya yi tasa aka fara taruwa na yin ta kasa. Can kuma ba su ankara ba sai ga Muzahara a Abuja. Wannan ya firgita su sun tsorata sosai da lamarin Zakzaky. Don haka suka sake gaiyato 'Consultant' daban daban sun yi musu sabon shirin mai suna 'Ka yaki Makiyin har cikin gidansu kada ka bari ya zo gareka' wato ( Fight Your Enemy at his Home and Never let him come to your Home'
*JAMI'AN TSARO NE SUKA KAWO MANA HARI A KANO*
_Saifullahi Shehu Dandume_
Hujjoji na zahiri da badini sun tabbata Kamar yadda hotuna da shaidun gani da ido suka tabbatar.
Akan idon mu motar yan sanda babba ta kawo wasu mutane cikin farin kaya ta sauke a gidan mai na Azman dake France Road suka sakko suka saje da mutanen gari.
Duk da an aje motocin yan sanda a Kofar massallacin na Fagge ba Kamar yadda aka sabayi ba idan zamu tashi muzahara, an tashi muzahara cikin Izza, sun dauka cewa zamu je gadar sama ta Kofar Nasarawa ne Sai sukaje suka kashe titin suka raba positions, amma Sai ya zama an yanke anbi ta kantin kwari, sai sukai Maza suka mamaye wajen gidan Sarki a tunanin su nan za'a sauke muzahara din, nan ma suka Sami labarin anbi titin abbatuwa.
Da akazo Junction na Kofar wanbai saiga motar yan sanda uku a guje, suna sakkowa suka ce ma haris dinda ke bada hannu wajen yabar wajen yace aiki yake, nan take suka fara masa zagi mummuna na rashin tarbiyya irin wanda dole a tunzura wanda ake mawa, kawai wani dan uwa yazo yace mashi tashi a wajen, sun tafi Amma suka biyo su suka cigaba da wannan zagin Amma 'Yan uwan ko waiwayensu basui ba.
Adaidai lokacin da goshin muzaharar yazo Junction na abbatuwa Sai ya tsaya cak ashe sunzo sun saka gate sun rufe inda za'a biyo wato ta kofar Mazugal zuwa filin dalar gyada, sai yan uwa suka yanke shawarar a koma ta wajen gidan boss anyi kwana kenan nanma suka zo suka tsare.
Sai Mal Sunusi AbdulKadir Koki dake jagorantar muzaharar ya bada sanarwan an sallami kowa an tashi don gudun abinda zaije ya dawo har ya zama ya shafi sauran al'ummar gari.
Ganin da yawan yan uwa sun koma Sai harisawa tsiraru da aka bari, akan idona tun farko yan sanda suke cewa mutanen wajen su tashi kar abin ya shafe su, su ka janye su kuma suka fito da yan sanda su masu farin kaya don yin abinda sukai niyya.
Da farko sun so sui amfani da yan dabar kasuwar abbatuwa Sai sarkin fawa din Bai yarda ba, sai su yan sanda din sukai magana dashi kawai Sai gashi yana watsa ma yaran nasa kudi yana cewa ku shiga ku far masu, su Kam yanda kasan anyi masu allura, haka sukai ta saran yan uwa da jifa, duwatsu na sauka Kamar zubar kankara ga yan sanda suna masu rakiya ta Baya.
Lokacin da Allah yaba yan uwa nasara suka maida su, sai kawai yan sanda suka fara harba ma yan uwa tiyagas.
Daga Baya suka rufarma yan uwa da suka rage suna Sara da duka su kuma masu kaki suna dauka su saka a Mota, wannan Bai ishesu ba suka dakko motocinsu suka zuba wadannan zauna gari banza din da yan sanda masu farin kaya suka shigo cikin gari suna ta dukan yan uwa da Sara.
Abinda ya faru bakin asibitin murtala da kasuwar rimi ya kazanta, sun daki sisters sun cire masu hijabi harda dan kwalin kansu? a gaban jami'an tsaron da suke cewa suna bada kariya a gidan radio.
Wani dan uwa yana tafiya kawai wani ya caka mashi wuka ta baya, ya fadi yana Kiran Labbaika ya Hussain Sai kawai yan sanda suka zo suka taka kafarshi suka dauke shi suka jefashi cikin Mota sukai gaba.
Haka muka taho Muna ta dora yan uwa mata da Maza Kan abin hawa da saita masu hanya musamman wadanda ba yan gari ba. Wasu muka kaisu tasha da sauran su.
Sai gashi kwamishinan yan sanda yana cewa, su sun shiga tsakani ne sun ba yan uwa kariya
Tambaya anan itace
Su waye a cikin farin kaya kuka Diba a motar ku Kuna kaisu suna raunata yan uwanmu?
Da kuka ce kun kwace mu a hannun mutanen gari suna cutar damu mutum nawa kuka kama a cikin su?
Da wane tuhuma kuke tuhumar yan uwa da kuka kama don tseratar dasu daga mahara da kuka kaisu kotu yau?
Shin maharan sun dauki motar yan sanda ne da kayan yan sanda sukai amfani dasu wajen kai mana hari Kamar yadda shaidun gani da ido da hotuna suka nuna?
Ya Allah kana ganin duk abinda ya faru, kai mana hukunci tsakanin mu da azzalumai domin Kaine mafi hukunci masu hukunci.
Allah ka Kara mana Juriya da dakewa ka cire mana tsaron Azzalumai, ka kubutar mana Jagoranmu da yan uwanmu daga hannun Azzalumai.
Labbaika ya Hussain
Labbaika ya AL Zakzaky.
Sallar Jana'izar da Binni Shahid Jafar Ali dazu da Rana. Malam Abdulhamid Bello ne ya yi masa Sallah, da nan aka dauki gawar zuwa Makarabar Bacirawa. Yan Sanda suna biye da Gawar suna Kokarin samun dama su kwaceta da haka aka samu suna biye da Yan Uwa da Bindigogi da Motoci har Makabartar. Bayan an binneshi Malam Abdulhamid Bello ya yi takaitaccen Jawabi akan abin ya sameshi da wadanda suka sanadin abkuwa abin, cewa Gwamnati ta tsara ta turosu. Ko sun fito a Khaki ko sun yi Shigar Yan Iskan Gari dai sune. Ko su waye dai aiko aka yi kuma Gwamnati ce.
Malam Sunusi Abdulkadir ma kafin Malam Abdulhamid Bello ya yi nasa Jawabi ya nuna cewa Wannan alamomin kan hanya ne ya nuna mana cewa akan hanyar Imam Husain Muke. Sannan abin Farin cikin ne. Wannan Shahid jiya an Haifa Masa Jariri.
MUN KUSA ZAMA FALASDINAWA. A KASARSU TA GADO.
Yau aka yi Jana'izar Shahid Jafar Ali, wanda a sakamakon Dukan tsiya da sara da Jami'an Tsaro cikin farin kaya suka yi ma sa da rakiyar wasu Yan daba da suka dauka Hayarsu suka biya. Bayan kammala Muzaharar Ashura da aka yi lafiya ne yan sanda cikin Khaki suka fara aukawa yan uwa da suke kokarin komawa gida. Sannan suka baiwa sauran Yan sandan da suke cikin farin Kaya dauke da Takobi da gariyo da barandami da Wuka umarnin suka farwa duk wanda suka samu. Mata da Yara da duk wacce suka gani da Cikakken Hijabi irin wanda Allah ya bada Umarni Matan Musulmi Muminai suka saka. Wannan ya jawo an sari Mutane da yawa da raunata su. Jafar Ali yana cikin wadanda suka samu Raunika mafi Muni.
Yau bayan yi masa Sallah Jana'iza an kama hanyar Makabarta sai Gungun wasu Motoci Yan Sanda wasu a cikin Fararan Kaya wasu a khaki dauke da Muggan Bindigogi suka dinga Bin Motar Gawar suna Kokari tsayar da ita. Abin kamar wasa sai da dabara aka iya kaucewa Sharrinsu. Sun karo wasu Motocin dauke da Yan sanda har guda Uku zuwa Makabarta. Kafin a Kammala sun cika bakin Layin Gidan Man Fetur na Azman da Yan Sanda sun rarraba su waje waje. Don haka da aka Kammala Binneshi sai da aka baiwa Yan Uwa Shawarar sun sauya hanya don alamu sun Nuna suna son su yi kamu ne. dole aka yiwa Yan Uwa Mata Rakiya saboda Sharrin Masu sace Muminai Mata.
Abin tambaya yaushe muka zama a Kasar Falasdinu don a nan ne Idan Yahudawa sun kashe falasdinawa idan sun Jana'iza suke binsu har Makabarta su sake Kashe wasu. Ko sun hana su binnewa ko su hanasu Zaman Makoki.
Yaushe kuma Jana'iza ta zama laifi a kasar nan da har za a biyoka da Kwambar din Jami'an tsaro ana yi maka barazana ga rayuwarka. Wanda ba don Allah ya kiyaye an kauce musu ba da ba mamaki harbi za su sake yi akan Yan uwa.
Yana da kyau masu hankali a Kasar nan su takawa Gwamnati Buhari Birki don Mu ba bakin haure bane, kuma Iyayenmu ba haurowa suka yi daga wata Kasa ba. Muna da yancin Mu yi addini da kuma zaba. Kuma Addinin Gidan Manzon Allah muka zaba za mu yi komai Kisa komai dauri.
TAKARDAR MANEMA LABARAI
SOJOJI SUN SACE YAN HARKA ISLAMIYYA
A KATSINA
Mun samu labarin sojoji sun sace yan uwa
musulmi guda biyu akan hanyarsu ta
dawowa gida daga zaman makokin ashura a garin katsina,
Satar ta fara ne ranar litinin 03-
October-2016, da sunusi haruna a dutsin-
ma, garin katsina. Wasu sojoji ne suka
wurgashi motarsu da yanayi irin na masu
kidnapping, suka kwace bakar tutar Ya Hussain dake hannun sa, tun daga lokacin
ba'a kara jin duriyar sa ba.
Sannan rana ta biyu (talata) wasu soji a
katsina metropolis suka sace yar uwa
budurwa, Aisha attah, bayan zuwanta
zaman makokin imam Hussain, da yamma, tuni aka bayyana cewa sun
dauketa zuwa kano, kuma inda aka kaita
a kano bamu sani ba.
A lokacin da nike wannan rubutun babu
wani laifi da hukuma ta bayyana ta kama
yan uwan dashi, don haka muna sanar da al'umma cewa watan muharram a
kalandar musulunci lokaci ne na tuna
kisan da akaiwa jikan manzo
Muhammad, Imam Hussain a shekarar 61
ah (680 ad).
Haka kawai aka kama wadan nan yan uwa lokacin da suke dawowa daga
zaman makoki.
Bamaso mu aminta da sojojin Nigeria,
kamar yadda al'amarin Nigeria ya koma
addinanci, amman abinda ya faru
kwanannan a katsina shine ya bayyana kasar, yau she ne zaman makokin ashura
ya zama ta'addanci a Nigeria?
Rahoto mai kamar wannan a jos, plateau,
da potiskum, garin yobe, ya nuna cewa
ana turo wasu sojoji guraren zaman
makokin, kuma babu rahoton wani abu na faruwa, tambaya mai muhimmanci
mai bukatar amsa itace miyasa hukuma
take tsoratarwa da soji?
A don haka harkar musulunci a Nigeria
tana kira ga hukumomin dake da alhakin
kama manbobinta dasu sakesu ba tare da wani sharadi ba, tunda basu aikata wani
laifi ba, sannan a karshe muna kira ga
hukumomi dasu daina cutar da yan harka
da sojojin su.
SA HANNU
IBRAHIM MUSA Shugaban yada labarai na Harkar
musulunci
08050786093
05/10/16.
Calling together all brothers and sisters who are interacting with social Networks to a single platform in order to conform with the accepted ideology of the movement in spreading the message of the movement through the internet.