Welcome to the official website of Internet Forum of the Islamic Movement in Nigeria, under the spiritual leadership of his eminence, Sayyid Ibraheem Ya'qoub Zakzaky(H).
KARE FIKIRAR JAGORA?
Ibrahim Ahmad Daurawa
Duk Mai shiga Whatsapp ko Facebook a yanzu zai sha karo da irin wannan rubutun ko da wannan sunan ko da wani mai kama da shi. Haka za ka ji wasu suna furta haka a wajeje da dama. Suna tada Jijiyar Wuya suna su fa akan kare Fikirar Jagora a shirye suke su yi fada da duk wani dan uwa, wasu ma suna kunduma Ashar da kalamai na alfasha iri iri.
Abin tambaya shi ne wai menene Fikirar Jagora ne. Idan mu san Fikirar Jagora za mu gane wadanda suke akan Fikirar Jagora da wadanda suke fada da Fikirar Jagora da kowace irin kama suka fito. Kamar yadda Imam Ali ya ce ne ka san gaskiya za ka gane wadanda suke tare da ita. Abin lura gaskiya ake sani sannan a san wadanda suke tare da gaskiya. Ba Mutane ake sani ba a ce su wane da wane sune akan gaskiya.
Wannan Ma'aunin ya kamata mu yi amfani da shi wajen tace su wane da wane akan Fikirar Jagora suke ko akasin haka. Don haka sanin Ainashin fikirar Jagora daga Jagora zai taimaka mana cikin sauki mu gane wane akan Fikirar Jagora, wanene kuma yake yunkurin sauya yan uwa daga Yakirar Jagora, amma da sunan yana kare Fikirar Jagora.
Shiekh Ibrahim Zakzaky shi ne Jagoran Harka Musulunci a Najeriya. Kuma komai nasa a fili yake, ba wani abu da yake a boye. Akwai Jawabansa daban daban a Kaset da Audio da Bidiyo kowa zai iya mallaka ya saurara. Sannan abin da ya fi Mahimmanci shi ne aiyuka da Matsayar Sheikh Zakzaky akan kowane abu, wanda yake fadi cewa Harkar Musulunci Karatu ne da aiki da shi. Aiyukansa suna Fassarar Karatunsa kuma a fili suke. Muna gani aiyukansa da yadda yake hulda da Mutane daban da daban masoya da Makiya. Talakawa da Azzalumai. Ba wani abu da ya shige mana duhu, domin yana zaune ne a cikinmu. Don haka duk mai neman gaskiya babu wani abu da zai shige masa duhu a halin yanzu.
Munufar Sheikh Zakzaky kirane ne zuwa ga tabbatar Musulunci a aikace a kawunanmu, kamar yadda Allah ya umarce mu da mu aikata shi. Allah kuma bai dora mana abin da ya fi karfinmu ba. Hanyar Tabbatar da Musulunci shi ne hanyar Gwagwarmaya da fadi tashi har Allah ya dubemu da Rahmarsa ya tabbatar mana da abin da muke hankoro. Abin da ya fi mahimmanci shi ne neman Yarda Allah a wannan Gwagwarmayar. Yarda Allah shi ne burinmu shi ne a'ala. Idan muka samu wannan mun yi Nasarar.
A takaice aikata addini irin yadda Manzon Allah ya aikata shi ne Kiran da Manufar Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky. Idan Mutum yana aikata addini yadda Manzon Allah da Imamai suka aikata a cikin Sauki za a gane. Idan kuma yana aikata wani abu daban shima cikin Sauki za a gane.
Abin tambaya ana iya sauya Munufar Sheikh Zakzaky ta gwagwarmaya akan tafarkin Allah? Amsa ana iyawa saboda an sauya Munufar wasu Annabawan.
Ta wacce hanya ake sauyawa, ta ciki ko ta waje. Amsa ana sauyawa ta cikin Da'awar ba ta waje ba. Ko ta hannun dama ku ta hannun Hagu.
Sauya Da'awa ta hannun Dama shi ne a fifita wasu abubuwa da ba su da Muhimmanci a ba su Muhammanci a watsar da masu Muhimmanci. Kamar a ce ba a bukatar Jihadi yanzu kawai abin da ake bukata shine Azkar a tsarkake Zukuta. Ko a ce ba a bukatar Bincike da Sabunta Ilimi mu rike abin da ake da shi kada mu yi shishigi akan lamarin Allah. Idan aka bi wannan hanyar an sauyawa Addini Matsayi a cikin Al'umma an kuma dakile matsayin da yake da shi wajen motsa al'umma da kawo sauyi. Kamar yadda ya faru a Tarihin Musulunci.
Ana kuma sauya Munufa da fikirar Da'awar mai kira ta hannun Hagun. shi ne a shigo cikin Addini a dinga karfafa wasu Munanan dabi'u ana Yakar duk wani wanda yake da Kyakyawar dabi'a, a hankali sai Mutanen banza su zama su ake ganin Kimarsu, mutane su dinga gudun aikata duk wani abu mai kyau, saboda ana kyamar masu aikata hakan. A hankali duk wani Aiki na Addini mai kyau sai a gujeshi, a sauya shi da Kishiyarsa. Kamar dai yadda ya faru a lokutan Sarakunan Banu Umayya.
Ana amfani da wannan dabarar a sauyawa Addini fasali gabadaya da wani abu wanda Addinin yake Yakarsa. Misali Arnar Rumawa sun kasa kawo Karshen Kiristanci na Hakika sai wani Sarki ya kawo dabara ya ce su shiga Addinin su Sauyashi. A hankali suka sauya Bautar Allah da Bautar Gumakan Rumawa komai suka sauya shi suka ce shi Kiristanci. Masu addinin na Gaskiya suka kashesu, mutane suna ganin su batattu ne. Suka rungumi masu Bautar Gumakan Rumawa da sunan sune masu Addinin Kiristanci na Hakika.Ta wannan hanyar aka kawar da koyarwa Annabi Isa.
Duk wadannan matakan guda biyu Makiya suna amfani da su yanzu wajen kawo karshen wannan da'awar ta Sheikh Zakzaky don sun san cewa ba za su iya gamawa da ita da karfi bindiga ba.
Bana son na tsawaita.Yanzu tunda mun san ana sauya Fikirar Mai Kira.Idan mu lura da kyau mu ma Azzalumai suna son koma suna Yunkurin sauya Fikirar Jagora da wasu Gurbatattun Fikirori. Yanzu menene abin yi. Shin zamu zuba Idanu ne har Yaki ya ce mu har gida.?
Su wanene ya kamata su zama ma su kare fikirar Jagora? Shi akwai wasu ne da aka ware aka baiwa alhakin kare Fikirar Jagora? Idan haka ne wane Mataki ne ake dauka a zama mai kare Fikirar Jagora. Ta wacce hanya za a gane dan uwa yana kare Fikirar Jagora???
Wadannan amsoshin masu sauki ne, duk dan uwa hakkinsa ne ya ga cewa ya kare Fikirar Jagora, don haka dole ya san menene Fikirar Jagora. Ya kuma sani daga Jagora kai tsaye.
Babu wasu Yan uwa da ka nasafta aka ba su alhakin kare Fikirar Jagora, dukkan mu za mu zama masu kishin Fikirar Jagora, hakkin ne akan kowane dan uwa ya kare Fikirar Jagora.
Hanyar da za mu gane Dan uwa yana kare Fikirar Jagora shi ne, mu ga yana dabbaka Halayya irin ta Jagora. Misali yana kira wajen hada kan al'umma ba tarwatsu ba, Tausayawa da Girmama yan uwa da sauran al'umma ba jefo alkaba'i da rashin tarbiya, da sharri a cikin yan uwa ba. Ya zama Ma'abocin Addini abin misalai da sauke duk Hakkukuwan Harka , mu ganshi yana aiki da Ilimi a komai nasa, a takaice ya zama Wakilin Sheikh Zakzky a kowane fanni na rayuwarsa.
Wani abin mamaki sai ka dan uwa yana Gunduma ashar yana zage zage da sunan kare Fikirar Jagora. Idan aiyukan dan uwa suka yi hannun riga da kiran Sheikh Zakzaky ko ya kwana yana cewa shi yana kare Fikirar Jagora ne mun san yana yaudarar kansa ne, karya yake yana wakiltar Shaidani ne amma ba Sheikh Zakzaky ba.
Fikirar Jagora a fili take, kuma aikata addinin Zalla shi ne Fikirar Jagora ba sabanin haka ba. Babu Zagi, shagube, Habaici da cin Mutunci a fikirar Jagora. Kira ne da hikima da kyawawan aiyuka abin da yake rinjayar Zukatan abokan adawa, ba harzuka Mutane ba.
Ibrahim Daurawa.
Duk Mai shiga Whatsapp ko Facebook a yanzu zai sha karo da irin wannan rubutun ko da wannan sunan ko da wani mai kama da shi. Haka za ka ji wasu suna furta haka a wajeje da dama. Suna tada Jijiyar Wuya suna su fa akan kare Fikirar Jagora a shirye suke su yi fada da duk wani dan uwa, wasu ma suna kunduma Ashar da kalamai na alfasha iri iri.
Abin tambaya shi ne wai menene Fikirar Jagora ne. Idan mu san Fikirar Jagora za mu gane wadanda suke akan Fikirar Jagora da wadanda suke fada da Fikirar Jagora da kowace irin kama suka fito. Kamar yadda Imam Ali ya ce ne ka san gaskiya za ka gane wadanda suke tare da ita. Abin lura gaskiya ake sani sannan a san wadanda suke tare da gaskiya. Ba Mutane ake sani ba a ce su wane da wane sune akan gaskiya.
Wannan Ma'aunin ya kamata mu yi amfani da shi wajen tace su wane da wane akan Fikirar Jagora suke ko akasin haka. Don haka sanin Ainashin fikirar Jagora daga Jagora zai taimaka mana cikin sauki mu gane wane akan Fikirar Jagora, wanene kuma yake yunkurin sauya yan uwa daga Yakirar Jagora, amma da sunan yana kare Fikirar Jagora.
Shiekh Ibrahim Zakzaky shi ne Jagoran Harka Musulunci a Najeriya. Kuma komai nasa a fili yake, ba wani abu da yake a boye. Akwai Jawabansa daban daban a Kaset da Audio da Bidiyo kowa zai iya mallaka ya saurara. Sannan abin da ya fi Mahimmanci shi ne aiyuka da Matsayar Sheikh Zakzaky akan kowane abu, wanda yake fadi cewa Harkar Musulunci Karatu ne da aiki da shi. Aiyukansa suna Fassarar Karatunsa kuma a fili suke. Muna gani aiyukansa da yadda yake hulda da Mutane daban da daban masoya da Makiya. Talakawa da Azzalumai. Ba wani abu da ya shige mana duhu, domin yana zaune ne a cikinmu. Don haka duk mai neman gaskiya babu wani abu da zai shige masa duhu a halin yanzu.
Munufar Sheikh Zakzaky kirane ne zuwa ga tabbatar Musulunci a aikace a kawunanmu, kamar yadda Allah ya umarce mu da mu aikata shi. Allah kuma bai dora mana abin da ya fi karfinmu ba. Hanyar Tabbatar da Musulunci shi ne hanyar Gwagwarmaya da fadi tashi har Allah ya dubemu da Rahmarsa ya tabbatar mana da abin da muke hankoro. Abin da ya fi mahimmanci shi ne neman Yarda Allah a wannan Gwagwarmayar. Yarda Allah shi ne burinmu shi ne a'ala. Idan muka samu wannan mun yi Nasarar.
A takaice aikata addini irin yadda Manzon Allah ya aikata shi ne Kiran da Manufar Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky. Idan Mutum yana aikata addini yadda Manzon Allah da Imamai suka aikata a cikin Sauki za a gane. Idan kuma yana aikata wani abu daban shima cikin Sauki za a gane.
Abin tambaya ana iya sauya Munufar Sheikh Zakzaky ta gwagwarmaya akan tafarkin Allah? Amsa ana iyawa saboda an sauya Munufar wasu Annabawan.
Ta wacce hanya ake sauyawa, ta ciki ko ta waje. Amsa ana sauyawa ta cikin Da'awar ba ta waje ba. Ko ta hannun dama ku ta hannun Hagu.
Sauya Da'awa ta hannun Dama shi ne a fifita wasu abubuwa da ba su da Muhimmanci a ba su Muhammanci a watsar da masu Muhimmanci. Kamar a ce ba a bukatar Jihadi yanzu kawai abin da ake bukata shine Azkar a tsarkake Zukuta. Ko a ce ba a bukatar Bincike da Sabunta Ilimi mu rike abin da ake da shi kada mu yi shishigi akan lamarin Allah. Idan aka bi wannan hanyar an sauyawa Addini Matsayi a cikin Al'umma an kuma dakile matsayin da yake da shi wajen motsa al'umma da kawo sauyi. Kamar yadda ya faru a Tarihin Musulunci.
Ana kuma sauya Munufa da fikirar Da'awar mai kira ta hannun Hagun. shi ne a shigo cikin Addini a dinga karfafa wasu Munanan dabi'u ana Yakar duk wani wanda yake da Kyakyawar dabi'a, a hankali sai Mutanen banza su zama su ake ganin Kimarsu, mutane su dinga gudun aikata duk wani abu mai kyau, saboda ana kyamar masu aikata hakan. A hankali duk wani Aiki na Addini mai kyau sai a gujeshi, a sauya shi da Kishiyarsa. Kamar dai yadda ya faru a lokutan Sarakunan Banu Umayya.
Ana amfani da wannan dabarar a sauyawa Addini fasali gabadaya da wani abu wanda Addinin yake Yakarsa. Misali Arnar Rumawa sun kasa kawo Karshen Kiristanci na Hakika sai wani Sarki ya kawo dabara ya ce su shiga Addinin su Sauyashi. A hankali suka sauya Bautar Allah da Bautar Gumakan Rumawa komai suka sauya shi suka ce shi Kiristanci. Masu addinin na Gaskiya suka kashesu, mutane suna ganin su batattu ne. Suka rungumi masu Bautar Gumakan Rumawa da sunan sune masu Addinin Kiristanci na Hakika.Ta wannan hanyar aka kawar da koyarwa Annabi Isa.
Duk wadannan matakan guda biyu Makiya suna amfani da su yanzu wajen kawo karshen wannan da'awar ta Sheikh Zakzaky don sun san cewa ba za su iya gamawa da ita da karfi bindiga ba.
Bana son na tsawaita.Yanzu tunda mun san ana sauya Fikirar Mai Kira.Idan mu lura da kyau mu ma Azzalumai suna son koma suna Yunkurin sauya Fikirar Jagora da wasu Gurbatattun Fikirori. Yanzu menene abin yi. Shin zamu zuba Idanu ne har Yaki ya ce mu har gida.?
Su wanene ya kamata su zama ma su kare fikirar Jagora? Shi akwai wasu ne da aka ware aka baiwa alhakin kare Fikirar Jagora? Idan haka ne wane Mataki ne ake dauka a zama mai kare Fikirar Jagora. Ta wacce hanya za a gane dan uwa yana kare Fikirar Jagora???
Wadannan amsoshin masu sauki ne, duk dan uwa hakkinsa ne ya ga cewa ya kare Fikirar Jagora, don haka dole ya san menene Fikirar Jagora. Ya kuma sani daga Jagora kai tsaye.
Babu wasu Yan uwa da ka nasafta aka ba su alhakin kare Fikirar Jagora, dukkan mu za mu zama masu kishin Fikirar Jagora, hakkin ne akan kowane dan uwa ya kare Fikirar Jagora.
Hanyar da za mu gane Dan uwa yana kare Fikirar Jagora shi ne, mu ga yana dabbaka Halayya irin ta Jagora. Misali yana kira wajen hada kan al'umma ba tarwatsu ba, Tausayawa da Girmama yan uwa da sauran al'umma ba jefo alkaba'i da rashin tarbiya, da sharri a cikin yan uwa ba. Ya zama Ma'abocin Addini abin misalai da sauke duk Hakkukuwan Harka , mu ganshi yana aiki da Ilimi a komai nasa, a takaice ya zama Wakilin Sheikh Zakzky a kowane fanni na rayuwarsa.
Wani abin mamaki sai ka dan uwa yana Gunduma ashar yana zage zage da sunan kare Fikirar Jagora. Idan aiyukan dan uwa suka yi hannun riga da kiran Sheikh Zakzaky ko ya kwana yana cewa shi yana kare Fikirar Jagora ne mun san yana yaudarar kansa ne, karya yake yana wakiltar Shaidani ne amma ba Sheikh Zakzaky ba.
Fikirar Jagora a fili take, kuma aikata addinin Zalla shi ne Fikirar Jagora ba sabanin haka ba. Babu Zagi, shagube, Habaici da cin Mutunci a fikirar Jagora. Kira ne da hikima da kyawawan aiyuka abin da yake rinjayar Zukatan abokan adawa, ba harzuka Mutane ba.
TASIRIN HARIN IRAN AKAN SANSANONIN AMURKA. Part 2
Ibrahim Ahmad Daurawa.
TASIRIN HARIN AKAN SIYASAR AMURKA DA IRAN.
Wannan harin ya kunyata Rundunar Sojan Amurka wacce akewa lakabi da Daular ce mai zaman kanta wacce ba a taba irinta ba a Tarihin Daulolin da suka gabata. Kuma ya wulakanta Shugabannin Amurka masu Matsanancin Girman Kai, masu Siyasar Danniya da Babakere. Sannan ya Sulmiyo da Girman kan Kasar Amurka ta fadi Wanwar. Kima da Matsayin Amurka a matsayin 'Super Power' guda daya Tilo ta fadi. Matsayin Amurka na Yar Sandar Duniya tsumagiyar kan hanya ya zube. Saboda tsoron Danniya da Murdiyar Amurka da ake a Duniya ba a taba samun wata Kasa da ta kai mata hari ba a wannan Karnin, amma sai ga Iran wacce take fama da takunkumi iri iri na shekaru 40, ta yi alkawari zata kai Mata Hari, Amurka ta sha alwashin Idan ta kawo sai buzunta. Kuma ta cika alkawarinta amma Amurka ta kasa cika alkawarinta na baje Wajaje 52 na Iran, ta ma buge da neman Sulhu. Wannan bai taba faruwa a Tarihin Amurka ba, akai Mata hari ta ce a zo a zauna ayi Sulhu. Karshe dai ta buge da batun Takukunmi. Wannan wane irin abin Kunya ne.
Wannan ya saka matsayin Amurka a wajen Yan Kanzaginta ya zube, sannan ya bude Kofar da sauran masu yiwa Amurka tsiwa su ga cewa suma za su iya, su kara bijere Mata. Kasashen Gabas ta tsakiya da suke ganin Amurka kamar Allah ce suka mikawa Mata Wuya, wai zata karesu. Gashi yau Amurka ta Kasa kare kanta, balle kuma ta karesu. Wannan ya jefa Tsoro a zukatansu. Nan da nan Natanyahu Shugaban Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya fito ya ce su babu ruwansu da Rigimar da ake a tsakanin Kasar Iran da Amurka don haka kada a tsoma su a ciki. Dole ya fito ya fadi haka saboda dama da Makaman Garkuwa daga Makamai Masu Linzami na Kasar Amurka suke tutiyar kare kansu daga Makaman kasar Iran, yanzu gashi Amurka ta kasa kare kanta daga harin Iran.Masanan Makamai na Kasar Isra'ila sun fito fili sun ce Mizayal din da Iran ta harbo, Makaman Isra'ila na Kariya ba za su iya karesu ba. Saboda an kera su ne a bisa fasahar Garkuwar makamai masu Linzami na Kasar Amurka wadanda suka gaza kare ko Mizayal daya daga wadanda kasar Iran ta harbo musu.
Wannan ya saka Saudiya suka yi lakwas, haka sauran Kasashen Tekun Fasha cikinsu ya duri ruwa. Saboda Amurka da suke Tinkaho da ita yau ta gaza Kare kanta daga Makaman Kasar Iran.
Wannan Harin da Iran ta kai ya bata matsayi da Girma a Idon Duniya, ya fito da ita daga kangin da Amurka ta jefa ta. Yanzu ta zama cikakkiyar Jagoran Masu fafutuka da Danniyar Amurka a Gabas Ta tsakiya. ya kuma baiwa sauran abokanta Karfin hali da Kwarin Gwiwa na Tunkarar Amurka da Kawayenta gaba Gadi.
Makaman Kasar Iran yanzu za su samu kasuwa a Kasuwar Cinikayyar Makamai. Masanan Kimiyya da Kere-kere na Iran za su yi Kima da tsada a wajen Takwarorinsu na Duniya. Abin da zai kawo budin Tattalin Arziki da mallakar wasu Fasahohin a cikin sauki. Tun bayan Harin da aka kai a Aramco, wani Kamfani a Rasha ya bukaci hadin Gwiwa da Kamfanin da ya Kera Drones din da Yan Houthi suka kai Hari kan Aramco saboda akwai sabuwar Fasaha ta wajen kera Injin Drones din, an Kerashi a bisa Fasahar Turbo Jet Engine, wanda sabuwar Fasaha ce a Kera Jiragai marasa Matuki.
Na karanta wani Bincike da wani Masanin Makamai masu Linzami ya yi Nazari akan Tarkacen Makamai Masu Linzami da Iran ta harbo a Sansanin Amurka. Ya yi bayani na Ilimi da Fasaha, ya kuma Yabawa irin ci gaban da Makeran Makamai masu Linzami na Kasar Iran suka kawo har Zanen banbancin da yake a tsakanin fasahar Kera Makama masu linzami wacce aka sani da wacce aka iya Nazari a Makamai masu Linzami na Kasar Iran. Wanda ya nuna shi ya baiwa Makamai karin Sauri da kuma saukin Sarrafawa idan an harbo su, yadda za su sauka akan wajen da aka saita su.
Wannan wani ci gaba ne kuma abin alfahari cewa Musulmi ma za su iya taka rawa suma iya sauya Fasahar Kere-kere ta Zamani. Yanzu kasar Iran ta zama abin koyi kuma Sabuwar alkiblar Kimiya da fasaha Kamar yadda Kasashen Musulmi suka taka a karnin baya lokacin da ake ruko da Musulunci sau da Kafa.
Wannan zai saka Iran taka rawar gani a Siyasar Duniya da yiwa Amurka katsalanda ga Muradunta na Gabas ta tsakiya. Yan Siyasar da Masu Mulkin Yankin dole su dinga safa da marwa a Birnin Tehran neman Sulhu. Masu yiwa Amurka hamayya a Siyasar Duniya irin su Rasha,China da North Korea dss, za su baiwa Kasar Iran Muhimmanci da goyan baya, wannan zai sauya Akalar Siyasar Duniya ya zama akwai Matsayi na tsakiya, ba kamar yadda Amurka ta shata cewa 'kodai ka zama tare da mu ko kuma kai dan Ta'adda ne.' Yanzu akwai wani Matsayi na wadanda ba sa tare da Amurka kuma ba yan Ta'adda bane, sannan dole a dama da su.
Kasashen Larabawa da suka baiwa Amurka Kasarsu suka Kafa Sansanonin Soja. Dole su fara tunanin abin da zai biyo baya wajen hada kai da Amurka a kai wa Iran Hari. Don sun san cewa Amurka ba zata iya karesu ba idan suka tsokana Kasar Iran. Wannan kuma zai kara jefa su cikin Tashin Hankali, saboda su dai ba za su iya hana Amurka amfani da Sansaninsu na Kasarsu ba, don ba su suke Iko da Kasar ba Amurka ce. Kuma idan haka ta faru Iran zata mayar da martani. Wannan ne ma ya saka Kasar Saudiya ware Makudan Kudade har Dala Miliyan Dubu suka zuba a Lalitar Amurka don su basu Tsaro. Amma sun manta Makaman Amurka da Sojojinsu suna nan aka kaiwa Kamfanunsu hari na Aramco ba su iya hangowa ko kare koda Makami daya daga cikin Sama da Talatin da aka harbo ba.
Amurka kuma dole ta yi taka tsan-tsan akan duk wani Mataki da zata dauka akan kasar Iran, don ta san cewa Iran tana da karfin da zata kare kanta da kuma kawai duk wani sansanin Amurka da Kadarorinta hari a duk inda suke a Gabas ta tsakiya.
Kaifin fasahar Makaman Iran ya baiyana a fili yada suka zabi wajajen da suke so suka kaiwa hari a nisan sama da Kilomita 700. Kamar yadda Rundunar Sojan Iran ta ce ba manufar harin ne su kashe Sojojin Amurka ba, sun yiwa Amurka Gargadi ne cewa Suna da karfin kai mata hari a duk wajen da suke so a Yankin. Sannan ya fito da manufar Yaki a wajen Musulmi, saboda Iran tana da zabi ta kashe duban Sojojin Amurka amma bata yi hakan ba sai yan Kalilan. Wannan ya nuna Kisa bashi ne Muradi a Yakin Musulmi ba, kuma wannan shi ne karo na biyu da Sojan Kasar Iran suka tausayawa Sojan Amurka na farko a lokacin da suka harbo Jirgi mara Matuki na Kasar Amurka wanda ya fi kowane tsada da kayan satar bayanai. Amma sai suka kyale daya Jirgin da yake dauke da Sojoji har sama da Talatin aka yi masa gargadi suka arce. A wannan ma haka ta faru, Sojojin da suka tsallake Rijiya da baya sun tabbatar da haka.
Babban abin da yake damun Amurka shi ne an kaiwa Sansanin Sojanta mafi Girma da tsaro a gabas ta taskiya hari an yi rugu-rugu da shi, bata iya kareshi ba. Kuma ta kasa cika alkawarin da ta yi na mayar da martani. Abin da ya taba Mutuncinta da matsayin Sojanta. Sai dai mu zuba Ido mu gani me Amurka zata ta yi ta dawo da Kimarta a Idon Duniya. Za ta tsaya ne akan Saka Takunkumi ko zata rama
A karshe wannan harin ya baiwa Musulmi Girma da matsayi cewa dogaro da Allah jari ne. Duk wanda ya dogara da Allah ya bi dokokinsa, Allah zai buda masa taskarsa ta Ilimi ya zama Gagabaradau a Duniya.
TASIRIN HARIN IRAN AKAN SANSANONIN AMURKA. Part One.
Ibrahim Daurawa.
Idan Mutum ba sai san Karfin Amurka a fannin Soja da fasahar Kera Makamai da kuma Karfinta a Siyasar Duniya ba. Zai Wahala ya fahimci irin Tasirin da Harin da Kasar Iran ta kawai Amurka. Dole Sai ka san wasu abubuwa a Siyasar Duniya da Harkar Tsaro da kuma Kitumurmurar Siyasar Gabas ta tsakiya, sannan za ka gano babbar Matsalar da harin ya haifarwa da Amurka. Musamman a Yankin Gabas ta tsakiya.
Babu wanda yake musun cewa Kasar Amurka tana da Rundunar Soja Mafi karfi da Rantsatsun Makamai a kowane fanni na Soja. Haka kwarewa da gogaiya a Yakin Zamani, saboda tun bayan Yakin Duniya na biyu Kasar Amurka a Yaki take da Kasashe daban daban a fadin Duniya
Amma idan za a gabza gaba da gaba ne, a tsakanin Amurka da Kasar Iran, Zai wahala ga Amurka ta iya yin galaba akan Kasar Iran. Saboda wasu dalilai wadanda ba a wannan Rubutun nake son kawo su ba. Amma abin lura shi ne Amurka ba taba yin Nasara a dukkan Yakukuwan da ta yi ba tun bayan Yakin Duniya na biyu. Ta kwashe Shekaru sama da 18 a Kasar Afghaninstan ba ta yi nasara ba, ta kashe kudi sama da Dala Tiriliyan Uku don ta mamaye Kasar Iraki, amma a karshe ba ta yi Nasara ba yau Shekara 17 ba iya cimma Muradunta a Iraki ba. Haka Labanon ba ta kwashe da dadi ba. Ga Kasar Yemel da take gani duka dauka ne, amma babu alamar za ta yi Nasara. Wannan ya nuna karfin Soja kawai ba shi ne abin da yake sakawa Kasa ta yi Nasara akan abokiyar gabar ta ba. Akwai wasu abubuwa da suke taimakawa Karfin Soja a kai ga Nasarar.
Amurka ce Kasa mafi girman kai da dagawa a doron Kasa a halin yanzu. Amurka ke damawa yadda ta so, kowa ya sha ko yana so ko baya so. Ta shiga gaban Kasashe a fasaha da Kere-keren Makamai da harkar Sadarwa da Tattalin Arziki. Amurka ce ta nada kanta Yan Sandar Duniya ta kuma zama Tsumagiyar kan hanya fyade Yaro fyade Babba. Ta riga ta zama Kura sai Allah ya isa. Amurka ke iko da wasu Kasashen kai tsaye. Ita ce ke nada Shugabanni da Sarakunan wasu Kasashen Larabawa. Mun ga yadda Wasikar Yan Majalisar Amurka guda biyu kacal suka saka Buhari Karkarwa a gaban wata Miskiniya, cikin yan Awanni ya sako Mutanen da ya rantse ba zai sakesu ba duk da Umarnin Kotunan Kasar nan. Abin da ya rantse da Kur'ani zai yi biyaiya ga dokar Kasa, zai kuma karesu. Haka Yayi watsi da Kiraye kirayen duk wasu Masu Mutunci a ci da wajen Kasar nan. Amma yana ganin Wasika daga Amurka ya rude ya Kideme, ya rikice yana rawar Jiki ya bada Umarni ya ce a sako su. Mutum Daya aka nema amma da ya tsorota biyu ya saki rigis bai sani ba. Saboda ya san duk Ta'addancinsa da Fir'aunancinsa sun damashi sun shanye, sune ma suka yi shi, suka bashi umarni yake kashe Yan Kasarsa.
Bayan Kisan Ta'addanci na Matsorata da Donald Trump ya saka Sojan Amurka suka yiwa Gwarzon Yaki da Ta'addanci da yan Ta'addan Yankin Gabas ta tsakiya Janar Kassim Solaimani. Wanda ya saba duk wata doka Ta kasa da kasa. Kuma Karara aikata laifin Yaki ne. Trump ya zaci Iran za ta yi shiru, ko ta nemi a sansanta. Amma sai ya ji suna shan alwashin daukan fansa. Kan Yan Kasar da Gwamnatin Kasar ya hade waje daya. Don haka gudun abin da zai biyo baya. Trump ya mika Goron Tattaunawa har da tayin janye Takunkumin da suka Kakaba musu da kuma karin tallafin Tattalin Arziki. Amma Iran ta ki amincewa da tayin da ya yi mata.
Trump da wadanda suka bashi Shawarar Kisan Janar Solaimani ba su yi tunanin abin da zai biyo bayan Kisan ba. Kuma sun dauka idan suka shiga Kafafa Yada Labarai na Yahudawa suka yi Karerayin da suka saba yiwa Amurkawa idan suna son su kai su Yakin Satar Man fetur shi kenan komai zai saisaita kamar yadda suka tsara. Amma sai akasin abin da suka tsara ya faru. Iran Kuma ta dage akan sai ta dauki Fansa. Wannan ya saka Trump tura Jakadun Kasashe daban daban har 16 don su shawo kan Iran kada ta dauki fansa da alkawura daban daban.
Me ya sa Trump ya ke kokarin lallamar Iran kada ta dauki fansa, bayan shi yake da Rundunar Soja mafi karfi a Duniya da Makaman Kare dangi?. Saboda Makamai ba su ne suke yin galaba a Yaki ba, Mutane ne masu Azama da Manufa Kyakkyawa. Kawayen Amurka na al'ada sun janye goyan bayan da suke baiwa Amurka Ido rufe a kowane Yaki Amurka ta jajibo, misali Kasar Ingila. Mutanen Amurka sun fara wayewa sun gane Gwamnatocinsu suna kaisu Yaki ana kashesu saboda Muradan Manyan Kamfanonikan Attajiran Yahudawa masu juya Amurka kamar Waina ba don Kare Muradun Kasar Amurka ba. Samun Tirjiya ga Yan Majalisar Amurka saboda bai tuntubesu ba. Kadan ne daga Matsalar cikin Gida da kuma ta kawayensu da Trump ya fuskanta wacce zai zata ba.
Amma babbar matsalar shi ne. Kasar Iran tana da Mutane masu Karfin Imanin da za su Yaki Amurka har Digon Jininsu na karshe, wasu Saboda Allah wasu yan Kalilan saboda Kishin Kasa. kasar Iran kuma ta kafa Kawayenta a koina a Yankin Gabas ta Tsakiya wadanda suke a shirye su kaiwa Muradun Amurka hari da Amurkawa. Misali a Labanon akwai Hisbullah, a Iraki akwai Hashidu Sha'abi ko PMF. A Yeman akwai Yan Houthi, Gaza akwai Hamas da Islam Jihad. Wannan sun yiwa Sansanonin Amurka da Muradunta da Kawayenta Kawanya, kuma kowane an jarraba kauda shi a baya da Karfin Makamai da Makircin Yahudawa an kasa. Babban Abin da Amurka take tsoro shi ne Iran ta samar da wasu Makamai da fasahar Sadarwa ta Yakin Zamani wacce har yanzu Amurka ba fahimcin bakin Zarenta ba. Takukumin da Amurka da Kawayenta suka Kakabawa Kasar Iran ya zama alheri gare su, ta dogaro da Kansu suka Kera Makamansu da Irin Fasahar Masanansu. Wannan Makamai an gwada su a Labanon, Isra'ila ta sha Kashi a Hannun Hisbullah a Shekarar 2006, haka Hamas sun kori Sojan Isra'ila a Lokacin da suka yi alwashin Mamaye Zirin Gaza da Sojansu ta kasa. Kwananan Iran ta harbo Jirgin Amurka mafi tsada da tarkacen Fasahar Leken Asiri da layar Zana. Sannan Harin da Yan Houthi suka kawai Kamfanin Man Fetur na Amurka a Saudiya mai Suna ARAMCO ya firgita Amurka da Kawayenta, har yau an kasa gano ta ina aka kawo harin balle a gane wanda ya kawo shi. Sai kawai cewa ake Iran ce saboda Makamanta ne ko kuma fasahar ta ce.
Wadannan Abubuwan sun jefa tsoro a Zukatan Sojojin Amurka da masu juya akalar Mulkin Amurka wadanda suke baiwa Trump Umarni wadanda yake yawan kira da 'Deep State'. Don haka Trump ya yi barazanar idan Kasar Iran ta kuskura ta kaiwa Amurka hari akan Kadarorinta ko Sojanta ko Fararen hula yan Kasarta ya rantse sai ya baje Kasar Iran, zai kawai Mahimman Wurare har 52 harin da zai mayar da su Toka. Wannan ba Barazana bane, alwashi ne. duk wanda ya san Siyasar Amurka ta danniya da babakere ya san za su aikata. Kuma ba a taba samun wata Kasa ta yi alkawarin kaiwa Amurka hari ta kai mata harin ba. Rabon ma da aka kawai Amurka hari Shekara wajen 70 kenan. Batun ma za a kawai Amurka hari a wannan Karnin babushi. Shi ya sa suke taka wadanda suka ga dama su Murje mu mutsike su shige abinsu, ba ruwansu da Doka ko Ka'ida ta Duniya.
MUHIMMANCI WAJEN DA IRAN TA KAIWA HARI.
Masana a Siyasar gabas ta tsakiya suna da tabbacin Kasar Iran za ta kaiwa Amurka harin Ramuwar Gaiya. Sai dai ba wanda ya zaci za ta iya kaiwa Sansanin Ain Assad Hari. Saboda ba wanda ya zaci Kasar Iran tana da karfin Makaman da koda ta kai harin za su iya kaiwa kusa da Sansanin. Balle kuma karfin halin da zata taba kaiwa Fuska, Hanci da Idanun Amurka a gabas ta tsakiya hari. Harin ya baiwa Masani Harka tsaro da Karfin Soja da Cakwakiyar Siyasar Duniya Mamaki. Don Al Assad shi ne Alami na Dagawa da Jiji da kai na Amurka. Wurin ne cike da Na'urorin leken Asiri ta sama da Kasa, cibiya ce ta Sarrafa Jiragan Leken Asiri da kai farmaki marasa Matuki. Haka kuma wajen cike yake da rantsatsun Na'urorin hango Makamai masu Linzami daga Nesa, wato Earlier Warning System. Nan ne kuma Cibiyar Tattara Rahotannin Asiri wanda Sattelite suke kwasowa a Kasashen Yankin Gabas ta tsakiya. Sannan kuma nan ne cibiyar bada Umarni da tattance bayanan Sirru da aka sato a wajaje daban daban a Yakin gabas ta tsakiya. Wajen yana kewaye da Makaman Kakkabo Jiragan sama da Makamai masu Linzami wanda kamar yadda suke Koda kansu ko Tsuntsu bai isa ya shige ta kan Sansanin ba sai da Izninsu. Balle Wani Makami mai Linzami ko Jirgin Sama mai Layar Zana. Saboda ko ta ina wani abu ya taho ana hangoshi ta Sattelite da Jiragai mara Matuki da suke Sinturi ba dare ba rana a kewayen Sansanin, kafin ya karaso Rantsatsun Radar da suke Kusa da wajen da Watan Dan Adam da yake sararin Samaniya za su hango shi a harbo shi da Makaman Kakkabo Jirgin Sama ko kusa da wajen ba zai karaso ba. Nan cibiyarsu ta Electronic Warefare take.
Amma duk da wadanda nan Makamai da Na'urorin Iran ta kawo harin wajen, ba kuma harin ba zata bane sun shelanta za su kawo hari kuma akan Sojoji ba fararen Hula ba. Sojan Amurka da Makamansu duk suna cikin Shirin ko ta kwana. Amma cikin dare ba zato ba tsammani suka ji Makamai masu linzama suna suka a Sansanin babu wata Na'ura mai hangen makamai daga nesa ko mai hangen makamai daga Kusa, ko Jiragansu na AWASC da suka iya hangosu. Makamai masu Linzami suna tafiya da Jelar wuta a bayansu kamar Tauraruwa mai wutsiya. Amma duk Sattelite din da suke sama da Drone guda hudu da suke shawagi a sama kamar yadda wani Sojan Amurka da suke basu Umarni ya fada cewa sune Idanuwansu a sama ba wanda ya hango komai. Suka shafe tafiyar Kilomita sama da 700 a cikin Dare suna tafiya tun daga Kasar Iran suka keta Kasar Iraki babu wata Na'urara da ta Sansanosu har suka sauka a Sansanonin.
Wani Sojan Kasar Denmark da ya ke a Sansanin a lokacin aka kawo Harin, ya fada a wata Shira da wani gidanta TV ya yi da shi mhttps://www.reddit.com/ai.
Ya ce suna Sansanin a Karkashin Kasa cikin Mabuyar Kankare. suna cikin Tsoro, ba zato ba tsammani sai kawai suka ji Aradu daga Sama ta sauka a Sansanin. Gine-gine na rushewa, wuta na tashi, tartsatsi baraguzai har wajen da suke. Sun sallama Mutuwarsu ta zo. Ya kara da cewa Sai bayan da Mizayal din farko ya sauka sannan Jiniyar Gargadin an kawo hari ta fara Gunji. Aka tambayeshi me ya sa da farko bata yi kara ba, ya ce saboda babu wata na'ura da ta sansano Makaman sun taho, saboda Makaman Rantsatsune masu kai hari wajen da aka aika su.
A karshe ya ce gaskiya duk wani waje mai mahimmanci a Sansanin an koneshi ko ya tarwatse, ya ce Kamar Cibiyar bayar da Umarni da wajen kai farmakin Sigina wato Electronic Warefare center da kuma Manyan Rada rada masu Sansano Makamai duk sun tarwatse, haka wajen Maboyar Jiragan Yaki da filin tashin Jiragai duk an yi musu Luguden Mizayal.. Ya ce a takaice dai Sansanin ya tashi daga aiki gabadayansa. Ya ce shi ya tabbatar Iran bata yi niyar kashe Sojoji ba, don ba a kawai wajen da Sojoji suke kwana harin ba, ya ce da an kai duban Sojojin Kasashe daban daban ne za su hakala. Ya ce wannan ya nuna Sojan kasar Iran suna da cikakkiyar Taswirar Sansanin da dukkan Sansanin Amurka da ke Yankin, ya ce wani abin tsoro shi ne babu Makami kwaya daya da makaman Kakkabo Makamai masu Linzami na Amurka da suka iya tare ko da kwaya daya. ba su ma hango su ba balle su harbosu.
ME NE NE HIKIMAR WAHABIYAWA NA CEWA IRAN KAWAR AMURKA CE?
Idan ana batun hankali, aiki da ilimi da basirar da Allah ya yiwa dan Adam. Idan ka zo kan Wahabiyawa suna ajiyeshi akan Shi'a da Kasar Iran. Suna amfani da Wahamin Shaidan, Karya, Kazafi da Sharri don sakawa Mutum Kamatar Shi'a da Yan Shi'a. Sannan babu ruwansu da Tarihi ko bayani na Zahiri ko Hujjoji na Hankali da Shari'a.Ba a batun Tunani ko Nazarin abubuwan da suke faruwa yau da gobe, balle Adalci. Abin da kawai suke so shi ne ka yi Imani da duk abin da suka fada maka akan Kasar Iran da yan Shi'a, shi ya sa ma suka ce Shari'a Sabanin Hankali ce. Duk abin da suka fada ya halasta idan za a saka Mutum ya kyamaci Shi'a kamar yadda Dan Taimiya ya basu Fatawa.
Babu banbanci a tsakanin Shaikh, Ustazu, Ko Professor ko Dr ko kuma dan Primary ko mai tura Kura ko mai sayar da Pure Water a bakin Titi. Duk Tunaninsu daya ne kan Shi'a. Illa yan Kalilan.
Abu ne mai sauki, kuma ruwan dare ka ji dan Izala Prof ko Shaikh wane, ko Dakta wane yana cewa da Kasar Iran da Amurka dan Jumma'a ne da Dan Jumma'i. Duk abin da yake faruwa Dirama ce suna wasa ne da hankali Mutane kawai amma Masoya Juna ne, a Karkashin Kasa suna dasawa sosai da juna.
Ga Mutum Wayyaye mai Ilimi Zamani ko na Addini abin zai zame masa wani banbarakwai. Ba zai iya fahimtar abin da ake so a nuna masa ba. Amma za su dage haka yake babu batun wani bincike. Duk wanda bai yarda ba Wallahi shima Dan Shi'a ne kawai Takiya yake.
Idan ka ce ya za a yi ace kawaye ne kuma Abokai juna, gashi suna Caccakar Juna kullum Amurka kokari take ta Mamaye Kasar Iran, ga Takunkumin Tattalin Arziki tana ta saka mata duk ta kassara rayuwar Mutanen Kasar ta hana Kamfanununkan Kasar bunkasa yadda ya kamata. Ta hana ayi Kasuwanci da ita ko a zuba hannun Jari a Ksar. Kullum Tattalin Arzikinta yana kasa, sakamakona haka. Tsahon Shekaru Aba'in?
Wani abin Mamaki ma shi ne Wahabiywa ne kan gaba wajen murna da Takurawar da Amurka take yiwa Iran, sune kan gaba wajen posting din Sulmiyowar Darajar Kudin Iran sakamakon Matsin Tattalin Arziki da Amurka ta kakaba mata.Sune ke nuna Yadda Talakawan Kasar suke fama da Matsin Tattalin Arzikin da Amurka ta kakaba musu. Suna na daya wajen Yayata Boren Talakawan Iran Yan Shi'a Saboda Gallazawar Takukunmin da Amurka ta kakabawa kasar na Zalunci, suna murna da farin ciki da hakan, komai kankantarsa ko daga Wajen Jaridun Isra'ila Labarin ya fito.
Idan ka ce me ya sa kullum Amurka ke Matsawa kasar Iran a Harkar diplomassiya da hana ta mallakar Abin da za ta kare kanta a harkar Tsaro. Tana kokarin wareta a duk wata Harkar, Kasuwanci, Kimiyya, Fasaha, hatta Harka Lafiya da Kayan Jin Kai?
Wahabiyawa za su ce maka wannan duk Takiyya suke a Karkashin Kasa akwai Soyaiya da Taimakon Juna, ba sa so ne Musulmi su sani don kada su gano yan uwan Juna ne.
Amma idan ka ce musu Me ya sa Amurka da Kasar Saudiya suke Kawance da Juna ko ace Zaman Ubangida da bawa. Amurka tana Gina Kamfanunnuka da Zuba hannun Jari a Kasar, tana kokari wajen samar da kyakyawan yanayi na Kasuwanci. Tana kafa Makamai na tsaron Kasar tana baiwa kasar Kariya ta fannin Soja, ta kuma sayar musu da Makamai masu tsada, har ta Kafa Sansanonin Soja ta kuma Jibge Dubban Sojajojinta Yan Luwadi da Madigo, Bakaken Mazina maciya Alade a Kasa Mai Tsaki?.
Wahabiyawa Za su yi dariya su ce kai ba ka gane bane wannan duk Siyasa ce. A karkashin Kasa Yaki suke da Juna ba sa kaunar Juna Sam sam.Kowane so yake ya rusa kowane.
Wannan kam duk Mai hankali Tunaninsa zai Kulle. Idan ka ce a kawo maka hujja babu, ba a bukatar wannan idan ka matsa za su ce maka kai dan Shi'a ne ko kuma dan Boka Akida.
Wannan tunanin na Wahabiyawa ya sabawa Hankali da tunani, musamman a wannan Zamanin na aiki da Hankali da Ilimi Nazarin hujjoji da ba'asi akan abubuwan da suke faruwa yau da gobe. Ba yadda za a ce ga wasu Mutane suna fada da junansu duk Duniya ta shaida, daya yana neman halaka daya. Sama da tsahon Shekaru 40, Kullum Kakkarfan yana amfani da duk Karfin da Allah ya bashi wajen ganin ya kawo karshen abokin Adawarsa ta kowacce hanya babu tausayi ba adalci sai Zalunci tsagwaronsa a Kokarinsa na ganin ya kassara abokin Adarwarsa. Amma wani ya zo ya ce wai Soyaiyya suke a boye, suna taimakawa juna. Hankali ya nuna duk Masoyi yana son ganin Masoyinsa ya ci gaba ya samu kwanciyat hankali, ya tallafa masa wajen ci gaban arzikinsa da kare Mutuncinsa. Amma a wajen Wahabiyawa duk wannan ba haka bane idan akan Iran da Yan Shi'a ne..
Dole ka Yarda cewa Amurka da Iran Kawayen Junane, duk abin da suke yi dirama ce babu wani takun saka a tsakaninsu. Kuma dole ne ka yarda da Amurka da Kasar Saudiya Abokan Adawa da juna ne duk abin da suke hulda da taimakon Juna duk Yaudara ce suke yiwa Amurka, a karkashin kasa fada suke da yaki da Juna. Wannan shi ne Tunanin Wahabiyawa tun daga kan Farfesa ko da kuwa ya kai Ameritus har zuwa kan mai sayar da Pure Water a Bakin Titi. Haka ake tattaunawa a Masallatansu da kuma a Teburin Mai Shayi.
Amma a Zahiri abin da Wahabiyawa suke yi wata Hikima ce da Iyayengidansu Yahudawa suka tsara musu, suke bi Ido Rufe. Amma masu amfani da hankali a cikinsu sun gane. Suna gani kuma wannan wata farar Dabara ce da za su ci gaba da Damfarar Mutane su Jefi Tsuntsu biyu da Dutse daya.
HIKIMAR ALAKANTA AMURKA DA IRAN CEWA ABOKAN JUNA NE.
Wannan dabara ce da Wahabiyawa ko na ce wadanda suka Kirkiro Wahabiyanci suka lakabawa Yaransu, don gudun kada a ganosu da wuri, cewa su Yaran Amurkawa ne ko na ce Yahudawa. A lokaci guda kuma a cusawa Mutane Kiyayya da Shi'a da Kasar Iran ta yadda za a nisanta su da fahimtar hakikanin Shi'anci da Kasar Iran, a kawo Rarraba a tsakanin Musulmi don a raunta su Gabadaya yadda za a ji dadin Murkushesu.
Abu na farko shi ne duk wani Musulmi ya san cewa Hulda ta Soyaiya da biyayya ga Kafurai Haramin ne ga Musulmin na kwarai. Amma Hulda ta Kasuwanci ko Kwadago ko Diplomasiiya wacce babu Kaskanci a tsakanin Musulmi da Kafurci ba haramin bane.
Abu na biyu kuma shi ne. Ayar Kur'ani ta nuna karara cewa Yahudu da Nasara ba za su So ka ba har sai ka bi hanyarsu ko Addininsu. Ma'ana idan Kai Musulmin kwarai ne to dole ne a ganka da kai da Yahuda da Nasara kuna Sa-in -sa. Ba kana bin su kamar Rakumi da alaka ba.
Wadannan abubuwan guda biyu suna da matukar Mahimmanci da sauki wajen gano wanene Musulmin Kwari ko wanene Gurbataccen Musulmi , kuma wanene Munafuki. Ba ka bukatar sai ka yi karatu mai yawa na Boko ko na Addini ka gano haka. Saboda Hausawa ma sun ce Abokin Barawo shima Barawo ne. Duk wanda ka ga yana shiri da Fasiki suna dasawa da juna shima Fasiki ne.
Wannan shi ne abin da Wahabiyawa suke gudu shi suke tsoro. Saboda Mutane za su gane su Addinin da suke tunkaho da shi ba na gaskiya bane, Saboda Duniya ta shaide su cewa suna dasawa da Yahudawa, ba ma dasawa ba su Yaran Yahudawan Amurka da Isra'ila ne. Duniya kuma ta Shaida tun bayan Kifar da Gwamtani Sarki Sha na Kasar Iran wanda a lokacinsa Kasar Iran suke dasawa da Isra'ila da Amurka sai abin da suka ce shi Kasar Iran take yi. Amma tun bayan Kifar da shi da dabbaka Juyin juya halin Musulunci. Kasar Iran suke adawa mai Zafi da Isra'ila da kuma Kasar Amurk. Babu wata Kasa a Gabas Ta tsakiya da take Yakar Muradun Amurka da birewa Manufofinta a Yakin irin Kasar Iran. Wannan abin a fili yake ba a boye ake yi ba. Wahabiyawa suna gani idan aka ci gaba da haka Kasuwar Wahabiyanci za ta Mutu da wuri, Musulmi za su dauki Kasar Iran a zama abin koyi kuma Shugabarsu. Don haka suka koma wajen Iyayengidansu don su kawo masu dauki.
Yahudawa Allah ya zargesu da Cakuda Gaskiya da Karya, haka kuma Wahabiyawa gwanaye ne a wajen taddalisi da Sauya Tarihi da yi masa Kwaskwarima ya dace da Akidarsu ta Kafurta Musulmi. Shi ne suka hadu suka fito da wannan Dabarar ta cewa Iran da Amurka da Isra'ila Yan uwan Juna ne, Abokan juna ne. Kai Tagwaye ne ma, dan Juma ne da Dan Jumma'a,. babu wani banbanci. Idan Mutum ya ce to ya suke fada da kokarin kauda juna. Sai ace maka aiya bane gane bane!. Duk abin da ka ga suna yi Dirama ce don su Yaudari Musulmi, amma a karkashin Kasa shiri ne kwakkwara.
Idan Mutum yana bin Siyasar gabas ta tsakiya ya ce amma Yahudawa sun Yaki da Hisbullah, sun Kashe Mutane da yawa a Labanon. Hisbullahi kuma a Yakin da suke yi da Isra'ila a 2006, Hisbullah sun Kashe Sojan Isra'ila har suka kore su daga Kudanci Labanon da suka mamaye tun a Yakin kwana shida a 1967. Sai su yi dariya su ce an rufta da kai duk wasan Kwaikwayone.Idan ka dage da kawo misalai sai su ce an rudeka ka zama dan Shi'a.
Wannan shi ne Dabarar Wahabiyawa, yan Izala. Da wannan suke boye alakarsu da Soyaiyarsu da Amurka da Isra'ila, su lakawa Kasar Iran abin da suke ne suke yi a Zahiri kowa yana gani. Dole ka ajiye hankali da Nazarin da abin da yake faruwa a gabanka, ka kuma yi watsi da Tarihin abubuwan da suka faru a tsakanin Iran da Amurka da Kasar Ingila. Ka rufe Idanunka akan Muradun Amurka na Mamaya da Danniya a Kasashen Musulmi.ka rungumi wannan Tatsuniyar.
Amma wannan Dabarar ba zata rufe gaskiya ba, karya da Kazafi babu yadda za su yi galaba akan Gaskiya. Yanzu a Zamanin Bayanai da Ilimi muke.
THIS SPEECH WAS DELIVERED IN 1992, AT A.B.U ZARIA
By Sheikh Zakzaky
"We must realize that this will not take us out of the woods. Even if all the people were to call for the resignation of Babangida, a worse tyrant will take up the mantle. That is the fact. When Shagari was the president, people wanted him out. The moment he was toppled, Buhari took over. Then people felt that things were much better with Shagari than with Buhari. Now after removal of Buhari, people are again saying Buhari is even better. Now, if Babangida is to step aside, people will agitate why will he not come back?"
"It is like a spoilt car. You keep changing drivers because of your erroneous belief that the problem is with the drivers. As long as the car is not repaired, the journey will never be smooth. The problem is not about drivers."
"For the avoidance of doubts, only a just system will produce just leaders. Thus, our efforts must be geared towards ensuring a just system. A just system will necessarily have to precede just leaders."
IMAM ALIY (KW) LIFE IS WORTHY A ROLE MODEL FOR US.
The grand finale of the annual Imam Aliy (KW) mauluds that was
undertaken by the youth forum of the IMN in Kano, Nigeria was marked
on Sunday 3rd Sha’aban 1438 (30/4/2017) at Markaz Kofar Waika, Kano
with Mal Badamasi Ya’quob, Professor Dahiru Yahya and Mal Sunusi
AbdulKadir Koki as guest speakers.
Mal Bashir Dan Dago, Mal Mustapha Limanci and Mal Uzairu Badamasi were
amongst the few poet that electrify the atmosphere with beautiful
songs of our Noble Prophet (SAWA), Imam Aliy (KW), Sayyida Fatimatul
Zahra (AS), Ahlul Bait (AS) and His Pious servants.
Mal Badamasi and Prof Dahiru in their speeches at the occasion drew
lessons worthy of emulation of the life of Imam Aliy (KW) adoring on
us to emulate his life worthy or emulation. In their speeches they
drew various lessons from the activities and role played by Shaikh
Zakzaky (H) in calling on us to come back to Al-Islam. Mal Badamasi
enjoyed youths to remain steadfast along the path of Allah and engaged
in all activities that gat one closer to Allah (T).
Mal Sunusi AbdulKadir Koki in his speech enjoyed youths to see to
getting on the very footpath Imam Aliy (KW) has stood and follow in
this religion that we have heard, read in this religion and will
emulate. Likewise, Mal Sunusi drew lessons from the life of Imam Aliy
(KW) on his leader in which he has vowed and stood by his leader even
if it will lead to his dead against all oppressors and oppression. If
we do agree Shaikh Zakzaky (H) is our leader would we remain mute and
fold our arms against any form of oppression or oppressors?
In the Maulud competition held in various categories, Mal Badamasi
Ya’aquob, Prof Dahiru Yahya and Dr Nura Azare handed prizes to winners
with the overall champions being Kofar Waika and Gwarzo zone. The
second were Naibawa and Kura zone and third Kura and Tudun Wada zone.
After the prizes distribution Mal Badamasi gave a closing prayer.Muhammad Isa Ahmad.
THE PRICE OF GUIDANCE
---------------------------------------------------
The religious activities of Sayyid Ibrahim Zakzaky at the academic ground of the University paved the the way for the inception of the Islamic mission when he was the vice president of the Muslims Students Society of Nigeria in its international wing. At this stage, the Islamic activities was confined to the University campus and in such a situation, lectures, seminars and symposiums were organised and paper presentation on various current Islamic issues were discussed to educate young students of the Islamic activities about global and national situations. Coupled with this vigorous development among young Muslims students, another group of students under the umbrella of palm wine drinkers association intensified their filthy and unhygienic activities in the campus which affected the entire students that were residents in the University campus.
Under the banner of the Muslims Students Society of Nigeria, the committed Muslims of the Ahmadu Bello University under the guidance of Sayyid Ibrahim Zakzaky protested against the continued use of lublic kitchenwares and utensils by the palm wine drinkers association for the consumption of alcoholic beverages which resulted in a severe tussles and widespread upheavals in the University campus.
In a short while, the palm wine drinkers association secured the full supports of the University authorities and the Nigerian government when strong body of well armed military men with armoured tanker in their convoy were dispatched by the military regime to suppress the protest which they described as religious extremism in the University campus. This armoured tanker however, remained at the University campus to provide enough and sufficient security and safety to the palm wine drinkers association until they were fully protected.
This event was a landmark as well as a turning point in the history of Islamic mission which was in reality, the mainspring of its powerful resistance against the secular regime that supported every act of religious abomination and popular aggression against the masses.
Free Allama Sayyid Ibrahim Zakzaky, his wife and followers now!!!
Calling together all brothers and sisters who are interacting with social Networks to a single platform in order to conform with the accepted ideology of the movement in spreading the message of the movement through the internet.